NNPP Ta Dakatar da Shugaban Dattawan Jam'iyya ana Batun Sauya Sheƙar Gwamna

NNPP Ta Dakatar da Shugaban Dattawan Jam'iyya ana Batun Sauya Sheƙar Gwamna

  • Jam’iyyar NNPP ta sanar da dakatar da Shugaban dattawan jam’iyyar a ƙaramar hukumar Ungogo, Alhaji Sammani Muhammad Zango
  • Hon. Sunusi Surajo Kwankwaso, jigo a tafiyar Kwankwasiyya, ne ya bayyana matakin dakatarwar saboda zargin rashin biyayya
  • Wannan lamari na zuwa ne yayin da ake ci gaba da rade-radin Abba Kabir Yusuf zai sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – NNPP ta bayyana dakatar da Shugaban dattawan jam’iyyar a ƙaramar hukumar Ungogo, Sammani Muhammad Zango, daga kujerarsa.

Jigo a Kwankwasiyya, Hon. Sunusi Surajo Kwankwaso ne ya sanar da daukar matakin, bayan an zarge shi da kin bin umarni daga sama.

NNPP ta dakatar da Shugaban kungiyar dattawanta a Ungogo
Jagoran NNPP na Najeriya, Rabi'u Musa Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Wannan umarni na kunshe a cikin wani bidiyo da Sunusi Surajo Kwankwaso ya yi, wanda Kano News Online ta wallafa a shafinta na Facebook, inda ya yi karin haske kan dalilan dakatarwar.

Kara karanta wannan

Shiga APC: Ciyaman ya rabu da 'yunkurin' Abba a Kano, ya tafi gidan Kwankwaso

Jam'iyyar NNPP ta dakatar da Shugaban dattawa

Hon. Sunusi Surajo Kwankwaso ya sanar da dakatar da Sammani Muhammad Zango bisa zargin take umarnin da aka ba shi daga shugabannin jam’iyya.

Rahotanni sun bayyana cewa akwai umarni daga sama da aka bai wa Shugaban dattawan kan ya dakata da batun kiran taron goyon bayan sauya sheka zuwa jam’iyyar APC, amma ya ki bin wannan umarni.

Ana zargin Zango da fatali da umarnin jam'iyya game da sauya shekar Abba
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, Gwamna Abba Kabir Yusuf Hoto; Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Twitter

A sanarwar dakatar da shi da Sanusi Kwankwaso ya karanta, ya ce:

“Sakamakon kin bin umarni da Shugaban dattawan ƙaramar hukumar Ungogo, Alhaji Sammani Muhammad Zango, mun samu umarnin dakatar da shi daga shugaban kungiyar har illa ma sha Allahu.”
“Muna sanar da shi cewa yau an bayar da umarnin dakatar da shi daga matsayinsa na Shugaba, kuma hakan zai ci gaba har izuwa wani ƙarin lokaci, sakamakon kin bin umarni.”
“Muna sanar da ‘yan ƙaramar hukumar Ungogo cewa daga yanzu ba shi ne Shugaban kungiyar a ƙaramar hukumar Ungogo ba.”

Kara karanta wannan

Yadda Abba ya lashi takobin shiga APC ko zai wargaje da Kwankwaso

Martanin jama’a kan dakatar da jigon NNPP

Yayin da rikicin NNPP ke kara daukar zafi, jama’a sun fara bayyana ra’ayoyinsu game da dakatar da Shugaban dattawan jam’iyyar a ƙaramar hukumar Ungogo.

Ibrahim Maikore ya ce:

“To amma ai doka ta ba ka damar yin haka, ko dai ka fi gwamna ne za ka tabbatar?”

Salisu Ahmad ya wallafa cewa:

“Kayyasa an fara kenan, Subhanallah.”

Shi ma Saminu Musa Musa ya ce:

“Anya kuwa NNPP ba za ta gamu da irin wani hari mai girma ba, irinsa na Donald Trump?”

An kori Shugaban NNPP a Kano

A wani labarin, mun wallafa cewa NNPP a mazabar Gargari da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano ta sanar da tsige tare da korar Shugaban jam’iyyar na jihar, Hashimu Sulaiman Dungurawa.

Hukuncin korar Dungurawa daga jam’iyyar ya zo ne makonni biyu kacal bayan sake zaɓensa a matsayin Shugaban NNPP na jihar Kano, inda jagororin suka zarge shi da jawo rabuwar kai a jam'iyya.

An gudanar da taron korar Dr. Hashimu Suleiman Dungurawa ne a ƙarƙashin jagorancin Shugaban mazabar Gargari, Shuaibu Hassan, tare da sakatarensa, Yahaya Saidu Dungurawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng