Ministan Tsaro, Janar C.G Musa Ya Tuno Yadda Ya Tsallake Makirci a Gidan Soja
- Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher G. Musa mai ritaya, ya ce ya fuskanci makirce-makirce a tsawon aikinsa na soja
- Ya bayyana cewa wasu sun yi tunanin sun datse masa hanyar samun manyan mukamai, amma sai Ubangiji ya sauya al’amura
- Tsohon sojan ya ƙarfafi matasa da ma’aikata su jajirce, su dage da gaskiya duk da ƙalubale domin komai zai wuce matukar suka yi tsayin daka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Ministan Tsaron Najeriya Janar Christopher Musa mai ritaya, ya ba da labarin yadda ya sha fuskantar matsin lamba da makirce-makirce a lokacin da yake aiki a rundunar sojin Najeriya.
Ya bayyana cewa ya fara samun masu kulla masa sharri tun daga karamin mataki har ya har zuwa lokacin da ya rike mukamin Babban Hafsan Tsaro (CDS).

Kara karanta wannan
Gudun shan jifa: 'Dan APC ya bukaci gwamna ya ba su hular kwano kafin su iya tallata Tinubu

Source: Twitter
Daily Nigerian ta wallafa cewa Janar Musa ya ce a wasu lokuta, adawar da ya fuskanta a cikin gidan soja ta yi yawa matuƙa.
Ministan tsaro ya tsallake makirce a gidan soja
Daily Post ta wallafa cewa a cewarsa, mutane sun yi haɗaka domin toshe masa hanyar samun ci gaba, suna ganin ba zai kai kololuwar shugabanci ba.
Janar Christopher Musa mai ritaya ya bayyana cewa akwai lokutan da makiyansa suka dauka sun yi galaba a kansa, amma Allah Ya fi su.
Ya bayyana hakan ne a wani taron addini da aka gudanar a ƙarshen mako, inda ya yi waiwaye a kan doguwar tafiyarsa a aikin soja, kalubalen da ya fuskanta da kuma darussan da ya koya daga rayuwarsa.

Source: Facebook
A cewarsa:
“Akwai lokuta da mutane suka yi makirci a kaina, suka yi tunanin sun riga sun yi nasara. Sun ɗauka cewa nawa ya ƙare.”
Sai dai ya ce duk da irin wadannan ƙalubale, ikon Allah ne ya sa ya tsira daga sharrin makiya, har ya kai ga rike manyan mukamai kafin ritayarsa daga aiki, sannan daga bisani aka nada shi Ministan Tsaro.
Ya ce:
“Abin da suka nufa da sharri, Allah ya juyar da shi zuwa alheri."
Sabon Ministan tsaro ya zaburar da matasa
Ministan ya bayyana cewa irin wadannan abubuwa sun koya masa hakuri, juriya da dogaro ga Allah maimakon dogaro da mutane, musamman a tsarin da ke cike da gasa da rikici wajen neman cigaba.
Ya kara da cewa makirce-makirce ba a farkon aikinsa kadai suka tsaya ba, sun biyo shi zuwa manyan mukaman da ya rike, ciki har da lokacin da yake Babban Hafsan Tsaro, kafin ya yi ritaya daga aikin soja.
Musa ya yi kira ga ‘yan Najeriya, musamman matasan sojoji da ma’aikatan gwamnati, da kada su yanke kauna idan suka fuskanci koma baya ko adawa.
Ya ce dagewa, gaskiya da tsayawa kan ka’ida su ne mabuɗan samun nasara a rayuwa a duk halin da mutum ya tsinci kansa.
A kalaman Ministan:
“Idan abubuwa ba su tafi yadda kake so ba, kada ka dauka komai ya kare. Watakila ana mayar da kai ne wata hanya. Idan ka tsaya kan gaskiya kuma ka dage, lokacinka zai zo."

Kara karanta wannan
'Fararen hula na cikin hatsari,' Jigon APC ya fadi kuskuren harin Amurka a Sokoto
Tinubu ya nada sabon Ministan tsaro
A wani labarin, mun wallafa cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya zaɓi Janar Christopher Gwabin Musa tare da nada shi matsayin sabon Ministan tsaro na Najeriya bayan ya bar mukamin Hafsun soja.
A cikin wata wasiƙa da Shugaba Tinubu ya aikawa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya sanar da cewa Janar Christopher Musa ne zai maye gurbin Alhaji Mohammed Badaru Abubakar.
Janar Christopher Gwabin Musa, wanda ya cika shekaru 58 a ranar 25 ga Disamba, ƙwararren hafsan soja ne da ya yi fice a harkar tsaro da ya riƙe mukamin Babban Hafsan Tsaro daga 2023 zuwa Oktoba 2025.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
