Tsautsayi: Ma'aikatan NTA 6 da Dan Jarida Sun Gamu da Ajalinsu a Titin Gombe zuwa Yola

Tsautsayi: Ma'aikatan NTA 6 da Dan Jarida Sun Gamu da Ajalinsu a Titin Gombe zuwa Yola

  • Hatsarin mota ya rutsa da yan jarida a kan titin Gombe zuwa Yola yau Litinin, 29 ga watan Disamba, 2025, kuma mutum bakwai sun mutu
  • Rahoto ya nuna cewa yan jarida shida da suka mutu ma'aikata ne a tashar talabijin ta NTA, da ke hanyar dawowa daga wurin daurin aure
  • Duk da babu wata sanarwa a hukumance daga FRSC, tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Pantami ya tabbatar da aukuwar lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Gombe, Nigeria - Wasu 'yan jarida shida da ke aiki a tashar watsa labarai ta gwamnatin Najeriya (NTA) da wani mutum daya sun rasa rayukansu a hanyar dawowa daga daurin aure.

Rahoto ya nuna cewa mutanen su bakwai, wadanda dukansu mambobi ne na Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen jihar Gombe sun mutu a wani mummunan hatsarin mota a titin Gombe–Yola.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba na shirin barin NNPP, Wike ya aika sakon gargadi ga masu shiga APC

Jihar Gombe.
Taswirar jihar Gombe da ke Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Leadership ta rahoto cewa hatsarin ya faru ne a yammacin ranar Litinin a kan titin Gombe–Yola, yayin da ’yan jaridar ke kan hanyarsu ta dawowa daga wani bikin aure.

Yan jarida 7 sun mutu a hatsarin mota

Bayanai sun nuna cewa waɗanda abin ya shafa na cikin tawagar kungiyar NUJ da ta yi tafiya domin tayaabokin aikinsu, ma’aikacin Nigerian Television Authority (NTA), murnar aurensa.

Daga cikin mutane bakwai da suka rasu, shida ma’aikatan NTA Gombe ne. An bayyana sunayensu da mukamansu, cewar Daily Post.

Sunaye da mukaman yan jaridar da suka mutu a hatsarin sun hada da Manu Haruna Kwami (Manajan Gudanarwa), Zarah Umar (Manajar Labarai), da Malam Isa (Edita),

Sauran su ne Musa Tabra (Tsohon Manajan Labarai da ya yi ritaya), Aminu (Direba), Adams (StarTimes), da kuma Judith I. O. Subeb.

Waɗanda suka samu munanan raunuka sun haɗa da Emmanuel Akila, Steven Doddo, Nina, da Jonathan Bara, kuma a halin yanzu suna karɓar magani a wasu cibiyoyin lafiya a jihar Gombe.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Ƴan bindiga sun kashe bayin Allah, sun sace wasu mutane a Gombe

Jami'an FRSC.
Jami'an Hukumar Kiyaye Hadurra ta Najeriya (FRSC) a bakin aiki Hoto: FRSC
Source: Twitter

Duk wani kokari da aka yi domin samun bayani daga Hukumar Kare Haɗurra ta Ƙasa (FRSC), reshen Jihar Gombe, bai yi nasara ba.

Pantami ya yi jajen hatsarin yan jarida

Yayin da aka kira wayar Babban Kwamandan FRSC ta jihar Gombe, Samson Kaura, baidaga ba har zuwa lokacin kammala wannan rahoto.

Tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Pantami ya tabbatar da faruwar wannan hatsarin a wani gajeren sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

"Inna lil Laahi wa inna ilaiHi Raaji'un! 'yan jarida dhida, mambobin kungiyar NUJ kuma ma'aikatan tashar NTA ta jihar Gombe, sun rasu a hatsarin mota. Allah Ya yi rahama, Ya kiyaye na gaba."

Tsohon dan Majalisa ya yi hatsari a Ribas

A wani labarin, kun ji cewa tsohon dan Majalisar wakilai, Hon. Ogbonna Nwuke, ya tsallake rijiya da baya a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da shi a jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Daga tafiya daurin aure, mutane 7 'yan gari daya sun mutu a jihar Gombe

Lamarin ya faru ne a kan titin Eastern By-pass, kusa da Hypercity a cikin birnin Fatakwal yayin da Hon. Nwuke ke tuƙa motar da kansa.

Hon. Nwuke ya fito ya godewa Allah bisa yadda ya cece shi daga hatsarin, wanda ya auku ranar Litinin, 22 ga watan Disamba, 2025 a Fatakwal.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262