Tushen Wutar Lantarkin Najeriya Ya Samu Matsala, An Fadi Jihohin da abin Ya Shafa
- Babban tushen samar da wutar lantarki na kasa ya durkushe a yau Litinin, inda samar da wuta ya ragu daga megawatt 2,052 zuwa 139
- Kamfanonin rarraba wuta guda takwas ciki har da na Kano da Kaduna ba su sami ko digo na wuta ba sakamakon wannan matsalar
- Wannan matsalar ta faru ne kwana daya bayan gwamnatin tarayya ta yi ikirarin mayar da cikakken ikon samar da wutar lantarki a kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - An samu gagarumar matsalar wutar lantarki a faɗin Najeriya a ranar Litinin biyo bayan durƙushewar babban tushen wutar lantarki na ƙasa.
Bayanan da aka samu daga hukumar kula da rarraba wutar lantarki mai zaman kanta (NISO) sun nuna cewa samar da wutar ya ragu sosai cikin sa'a ɗaya kacal.

Source: Getty Images
An samu katsewar wuta a wasu jihohin Najeriya
NISO ta bayyana cewa karfin rarraba wutar ya sauka daga megawatt 2,052.37 da misalin ƙarfe 2:00 na rana zuwa megawatt 139.92 kawai kafin ƙarfe 3:00 na rana, in ji rahoton Daily Trust.
Wannan rugujewar ta shafi dukkan sassan ƙasar, inda kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos) guda uku kacal daga cikin guda 11 suka iya samun wuta daga tushen wutar.
Kamfanin rarraba wutar lantarki na Ibadan (IBEDC) ne ya sami mafi yawan rabo da megawatt 80, yayin da kamfanin rarraba wuta na Abuja (AEDC) da na Benin suka samu megawatt 20, kowanne, wanda ya kai jimillar wutar da DisCos suka karɓa zuwa megawatt 120MW kacal.
Sauran kamfanonin rarraba wuta ba su samu wuta ko ta megawatt 1 ba, sakamakon lalacewar tushen wutar. Wadannan sun haɗa da Eko, Enugu, Ikeja, Jos, Kaduna, Kano, Port Harcourt da Yola.
Rashin tabbas kan lalacewar tushen wuta
Wannan lalacewar tushen wutar ya jefa birane da garuruwa da dama cikin duhu, lamarin da ya tilasta wa gidaje da kamfanoni dogaro da janareto da sauran hanyoyin samar da wuta, in ji rahoton Daily Nigerian.
Abin lura shi ne, wannan na faruwa ne kwana ɗaya bayan gwamnatin tarayya ta yi iƙirarin cewa ta gyara matsalar wutar bayan lalata bututun iskar gas na Lagos-Escravos da wasu suka yi.
Har yanzu, kamfanin kula da rarraba wutar lantarki na Najeriya (TCN) ko hukumar kula da wutar lantarki ta kasa (NERC) ba su yi bayani kan musabbabin matsalar ko lokacin da za a dawo da wutar ba.

Source: Getty Images
Yawaitar lalacewar tushen wutar lantarki
Najeriya na fama da yawan lalacewar tushen wuta a 'yan shekarun nan, wanda masana ke alaƙanta shi da tsufan kayan aiki, rashin isasshen iskar gas, da kuma raunin hanyoyin isar da wutar.
Wannan lamari na ci gaba da janyo damuwa ga 'yan ƙasar game da makomar wutar lantarki da kuma tasirinsa ga tattalin arzikin ƙasa.
Rashin tsayayyar wutar lantarki na ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da ke hana masana'antu haɓaka yadda ya kamata a ƙasar.
TCN ya taka nasara a samar da wuta
A wani labari, mun ruwaito cewa, kamfanin TCN ya sanar da cewa an kai megawatt 5,713.6 na samar da hasken lantarki ranar 2 ga Maris, 2025, wanda ya zarce matsayin baya.
Amma kamfanin kula da rarraba wutar lantarkin ya ce duk da haka, wannan ci gaba bai kai matsayin mafi girma da aka taba cimmawa ba na megawatt 5,801.60 a shekarar 2021.
Duk da haka, kamfanin ya bayyana cewa wannan sabon matsayi babbar nasara ce da aka cimma a sashen samar da hasken wuta a kwanakin nan da tushen wuta ke samun matsala.
Asali: Legit.ng


