"Babu Sassauci": Sojojin Sama Sun Kashe 'Yan Ta'adda Masu Yawa a Zamfara

"Babu Sassauci": Sojojin Sama Sun Kashe 'Yan Ta'adda Masu Yawa a Zamfara

  • Dakarun sojojin sama sun kaddamar da kai hare-hare a maboyar 'yan ta'adda da ke addabar mutane a jihar Zamfara
  • Sojojin saman sun samu nasarar kashe 'yan ta'adda da dama bayan sun farmake su a karamar hukumar Tsafe
  • Hakazalika, sojojin sun lalata sansanin jagoran 'yan bindiga, Kachalla Dogo Sule inda ake kera bama-bamai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - Rundunar sojojin sama ta Najeriya (NAF) karkashin bangaren sama na Operation Fansa Yamma, ta ragargaji 'yan ta'adda a jihar Zamfara.

Hare-haren wadanda aka kai a ranar 28 ga Disamba, 2025, sun yi sanadiyyar kashe ’yan ta’adda da dama tare da lalata cibiyar kera bama-bamai da sansanoninsu a jihar Zamfara.

Sojojin sama sun kai hari kan 'yan ta'adda a Zamfara
Jiragen yakin rundunar sojojin saman Najeriya Hoto: Sodiq Adelakun
Source: Getty Images

Jaridar Leadership ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sojojin sama, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya fitar a ranar Litinin, 29 ga watan Disamban 2025.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun ragargaza Boko Haram bayan Ndume ya nemi daukin Amurka

Sojojin sama sun ragargaji 'yan ta'adda

Sanarwar ta ce rundunar ta gudanar da hare-haren sama guda biyu masu tsananin tasiri a Dutsen Turba da kuma sansanin Kachalla Dogo Sule.

Dukkanin hare-haren an kai su ne a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara, inda aka kashe ’yan ta’adda masu yawa.

Air Commodore Ejodame ya ce bangaren sama na rundunar, bisa sahihan bayanan sirri daga tushe daban-daban, ya tura jiragen yakin NAF domin kai farmaki kan maboyar ’yan ta’adda a wuraren da aka gano.

A cewarsa, harin farko ya shafi Dutsen Turba, wanda aka tabbatar a matsayin maboyar ’yan bindiga, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar da hakan.

Ya kara da cewa bayanan leken asiri, sa ido da bincike sun nuna yawaitar motsin mutane da kuma wani gini mai rufin kwano da aka tantance a matsayin cibiyar ayyukan sansanin.

Ejodame ya ce bayan tabbatar da hakan, an kai harin cikin kwarewa da daidaito, wanda ya yi sanadiyyar samun nasara kai tsaye kan wurin.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun samu gagarumar nasara bayan gwabza fada da 'yan bindiga a jihar Kano

“Binciken da aka yi bayan harin ya tabbatar da lalacewar ginin gaba daya tare da kashe ’yan bindiga da dama."

- Air Commodore Ehimen Ejodame

Sojojin sama sun kashe 'yan ta'adda a Zamfara
Taswirar jihar Zamfara, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

An lalata wurin hada bama-bamai

A cewar kakakin sojojin, harin sama na biyu ya gudana ne a sansanin Kachalla Dogo Sule, wani fitaccen sansanin ’yan bindiga da aka gano a matsayin babbar cibiyar kera bama-bamai da shirya hare-hare.

Ya ce bayanan sirri sun danganta sansanin da shiryawa da aiwatar da hare-haren bama-bamai na baya-bayan nan a kan hanyar Dan Sadau–Magami.

“Harin da aka kai cikin kwarewa ya afka wa gine-gine da dama da ke a cikin sansanin, inda wuta mai tsanani ta tashi ta lalata wuraren tare da kashe ’yan bindiga masu yawa."

Air Commodore Ehimen Ejodame

Ya tabbatar da cewa wadannan hare-haren sama masu karfi sun raunana hanyoyin sadarwa da ayyukan ’yan bindiga a jihar Zamfara matuka, musamman karfinsu na kerawa da amfani da bama-bamai.

An dasa bama-bamai a Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu bama-bamai da aka dasa sun tashi da matafiya a jihar Zamfara ta tarayyar Najeriya.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Ƴan bindiga sun kashe bayin Allah, sun sace wasu mutane a Gombe

Bama-baman sun tashi ne a kan titin Dansadau-Magami inda suka yi sanadiyyar hallaka akalla matafiya guda tara.

Majiyoyi daga yankin sun yi zargin cewa 'yan bindiga ne suka dasa bama-baman a kan hanyar domin daukar fansa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng