Bayan Sakkwato, An Jero Jihohi 7 da Ya Kamata Amurka Ta Kawo Hari a Arewacin Najeriya
- Matsalar rashin tsaron Najeriya na ci gaba da jan hankali daga ciki da wajen kasar musamman bayan farmakin kasar Amurka
- Wani masani ya bukaci kasashen ketare da su taimaka su kawo dauki domin dakile hare-haren da 'yan ta'adda ke kai wa kan fararen hula a Najeriya
- Ya bayyana jihohi bakwai a matsayin waɗanda rikicin ya fi shafa, yana mai gargaɗin cewa matsalar rashin tsaro na neman wuce gona da iri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Masana da masu sharhi na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu bayan farmakin da sojojin Amurka suka fara kawo wa Najeriya da nufin dakile ayyukan ta'addanci.
Idan baku manta ba, kasar Amurka ta kai faramaki wasu yankuna a jihohin Saklwato da Kwara a makon da ya gabata ba da nufin kakkabe 'yan ta'adda.

Source: Getty Images
A wata sanarwa da kakakin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa a X, ya ce gwamnatin tarayya na da masaniya kan harin da Amurka ta kai Sakkwato da Kwara.
Wani masanin tsare-tsare da manufofin gwamnati a Najeriya, AbdulRasheed Hussain, ya lissafa jihohi bakwai da ya ce ya kamata su kasance a sahun gaba wajen kai hare-haren sama daga Amurka domin yakar ayyukan ta’addanci.
Da yake zantawa da Legit Hausa, Hussain ya nuna damuwa kan karuwar matsalar tsaro da kuma yawan kashe-kashen fararen hula da ake samu a sassa daban-daban na ƙasar nan.
Jihohi 7 da ake bukatar daukin Amurka
Hussain ya bayyana cewa:
“A gani na, bisa la’akari da rahotannin rasa rayuka, jihohi irin su Borno, Yobe, Kaduna, Zamfara, Neja, Filato da Benuwai na bukatar daukin sojojin (Amurka) cikin gaggawa.
"Waɗannan su ne wasu daga cikin jihohin da suka fi fuskantar tashin hankali a shekarar 2025, inda ake yawan samun mace-mace sakamakon hare-haren ’yan ta'adda.
"Wadannan yankuna su ne asalin girman matsalar rashin tsaro da ke ci gaba da lalata zaman lafiyar ƙasa tare da raguza yardar da jama'a suka yi da gwamnati.
Wane irin hali ake ciki a wadannan jihohi?
Masanin ya jaddada cewa waɗannan jihohi sun sha fuskantar hare-haren tashin hankali da kashe-kashen rayuka masu alaƙa da ta’addanci tun daga farko har karshen 2025.
Ya ce girman matsalar rashin tsaron da ke wadannan jihohi ya raunana amincewar jama’a da gwamnati tare da zama babbar barazana ga daidaito da zaman lafiyar ƙasa.

Source: Twitter
A cewarsa, akwai bukatar sojojin kasashen ketare kamar Amurka su kawo dauki wadannan jihohi bakwai domin dakile ayyukan ’yan ta’adda.
Bama-bamai 2 sun tarwatse a Zamfara
A wani labarin, kun ji cewa ana zargin 'yan bindiga da dasa bama-bamai a kan wani titi a jihar Zamfara wanda ya jawo asarar rayukan matafiya.
Akalla mutane tara ne suka mutu sakamakon jerin fashe-fashen bama-bamai da suka auku a kan hanyar Dansadau a jihar Zamfara.
Wani mazaunin Dansadau, Malam Nuhu Ibrahim Dansadau, ya ce fashewar farko da ta biyu sun hallaka mutane tara, yayin da ake ci gaba da tattara bayanan wadanda suka jikkata ko suka mutu.
Asali: Legit.ng

