Gwamna Ya Tausaya wa Malaman Musulunci, Ya Shirya Kara Masu Albashi a 2026
- Gwamna Dauda Lawal ya waiwaiyi 'dan albashin da ake bai wa malaman addinin Musulunci da limaman Juma'a a jihar Zamfara
- Mai girma gwamnan ya tabbatar da cewa ya karbi shawarwarin kwamitin da ya kafa domin duba albashin malaman, kuma zai fara aiwatarwa a 2026
- Ya bukaci malamai da sauran shugabannin addini su hada kai da gwamnati, kuma su maida hankali wajen shiryar da al'umma zuwa tafarkin zama lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara, Nigeria - Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana shirin kara alawus din da ake biyan Imaman masallatan Juma’a da malamai 11,300 duk wata a fadin jihar.
Gwamna Lawal ya shirya kara wa malamai kudin ne domin inganta walwalarsu kuma ana sa ran sabon tsarin zai fara aiki daga watan Janairu, 2026.

Source: Twitter
Daily Trust ta rahoto cewa ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga shugabannin addini yayin wata ganawa da su a fadar gwamnatinsa da ke Gusau.
Gwamna ya waiwayi malamai a Zamfara
Gwamnan ya bayyana cewa, a halin yanzu, gwamnatinsa na kashe Naira miliyan 81.8 a kowane wata wajen biyan albashi ga malamai, Imaman masallatan Juma’a, da masu tsabtace masallatai.
“Rahoton kwamitin da muka kafa ya bada shawara game da albashinku, kuma ina tabbatar muku cewa daga Janairu 2026, za a aiwatar da hakan domin jin dadinku,” in ji Lawal.
Gwamnan Zamfara ya kuma yi bayani kan wasu tallafi da gwamnatinsa ta samu, ciki har da tallafin Dala miliyan 3 daga Tarayyar Turai (EU), tare da wasu shirye-shirye da suka shafi inganta shugabanci da jin dadin jama’a a jihar.
Dauda Lawal ya damu da batun tsaro
Da yake nuna damuwa kan matsalolin tsaro da ke ci gaba da ta'azzara a Zamfara, Lawal ya yi kira ga shugabannin addini da su ƙara yawan addu’o’i.
Gwamnan ya nemi limamai da su dage da addu’ar nan ta musamman da ake kira Al-Qunut a cikin sallolin farilla guda biyar, domin neman taimakon Allah.
Ya bukaci jama'a su ci gaba da addu’o’i don gano da kawar da wadanda ake zargin suna tada fitina da ta’addanci, na fili da na boye a jihar Zamfara, kamar yadda TVC News ta rahoto.

Source: Facebook
Gwamnan ya kara bayyana damuwa matuka game da wasu abubuwan da suka faru, wadanda ya kira da “abin baƙin ciki,” duk da cewa ba su dace a fallasa ga jama’a ba.
Ya jaddada cewa ba zai kuskura ya jingina wa kowa laifi don neman riba ta siyasa ba, yana mai nuna kudurinsa na ci gaba da kwatanta gaskiya a mulki.
Har ila yau, ya yi kira ga malaman addini da su yi amfani da tasirin su, iliminsu, da fasahar su wajen shiryar da al’umma zuwa dabi'u nagari da zaman lafiya.
Gwamna Dauda ya samu lambar yabo
A wani rahoton, kun ji cewa an karrama Gwamna Dauda Lawal da lambar yabo bisa yadda ya gyara harkokin shugabanci da tunkarar matsalar tsaro a Zamfara.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya mika lambar yabo ta Nigeria Excellence Awards in Public Service (NEAPS ) 2025 ga Gwamna Dauda Lawal.
Daga cikin manyan nasarorin da aka ce gwamnan ya samu akwai gyara tsarin aikin gwamnati da jin dadin ma’aikata da biyan fiye da N15bn na bashin fansho ga tsofaffin ma'aikata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

