Bidiyo: Yadda Aka Yi wa Ɗan Uwan Tsohon Gwamna Zindir, Aka Lakaɗa Masa Dukan Tsiya
- Wasu fusatattun matasa sun ci zarafin dan uwan tsohon gwamnan Edo sakamakon zargin yin kalaman batanci ga masarautar Benin
- A cikin wani bidiyo, an hango Pedro Obaseki a tube a kofar fadar Oba yayin da matasa suka ayyana shi a matsayin makiyin Mai martaba
- Tsohon gwamna, Godwin Obaseki ya yi Allah-wadai da harin, ya bukaci hukumomin tsaro su kamo wadanda suka daki dan uwan nasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Edo - Wasu da ake zargin 'yan daba ne sun ci zarafin dan uwa ga tsohon gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, kuma shugaban kamfanin Hosamudia Farm, Don Pedro Obaseki.
An rahoto cewa, fusatattun matasan sun yi wa Mista Don Pedro Obaseki tsirara, tare da lakada masa dukan tsiya a Benin, babban birnin jihar Edo a ranar Lahadi.

Source: Twitter
An yi wa dan uwan tsohon gwamna tsirara
Jaridar Vanguard ma ta rahoto cewa dan uwan tsohon gwamnan ya gamu da fushin 'yan dabar ne a lokacin da ya je buga kwallo a makarantar firamare ta Uwa.

Kara karanta wannan
Abin da gwamnoni 19 suka ce kan bam din da ya tashi a masallacin Juma'a a Maiduguri
Wannan farmaki ya biyo bayan zargin da ake yi masa na yin wasu kalaman batanci ga masarautar Benin yayin wani taron tattaunawa da tsohon gwamna ya gudanar tare da 'yan jihar mazauna kasashen Turai.
A cikin wani bidiyo da ya karade gari, an hango Pedro Obaseki a gaban kofar fadar sarki a kan gwiwowinsa, yayin da wadanda ke jan sa suke shaida wa masu gadin fada cewa sun kawo "Oghion Oba" (makiyin Oba) domin a hukunta shi kan laifuffukan da ya aikata.
Martanin fadar Benin kan dukan Pedro Obaseki
Jami'an fadar da suka tattauna da matasan a lokacin sun yi magana da yaren Bini, inda suka bayyana cewa Oba yana shirin zuwa cocin "Holy Arousa" a lokacin.
Saboda sarkin zai je cocin domin yin godiyar kammala bikin al'ada na Igue ne hadiman fadar suka gargadi matasan kan yin abin da zai kawo duk wani hargitsi.
Sun shaida wa matasan cewa duk wanda ya ce zai yi adawa da Oba, to su bar shi su ga yadda karshensa zai kasance, lamarin da ya sa aka kyale Obaseki a wulakance ba tare da kaya ko takalmi ba.
Tsohon gwamna ya fusata da dukan kaninsa

Source: Original
A nasa bangaren, tsohon gwamna Godwin Obaseki ya yi tir da wannan hari, inda ya bayyana shi a matsayin cin zarafin bil'adama da kuma watsi da dokokin kasa, in ji rahoton Leadership.
Obaseki ya yi kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da bincike mai zaman kansa domin kamo wadanda suka aikata wannan danyen aiki ga dan uwansa.
Ya yi gargaɗin cewa barin 'yan daba suna daukar doka a hannunsu da sunan manyan mutane zai iya jefa jihar cikin yanayin rashin doka da oda wanda ba zai haifar da ɗa mai ido ba.
Kalli bidiyon abin da ya faru da wani lauya, Frank Tietie ya wallafa a shafinsa na X a nan kasa.
Fusatattu sun yi wa matar sarki tsirara
A wani labari, mun ruwaito cewa, wasu fusatattun matasa, da har yanzu ba a gano ko su wanene ba, sun lakada wa Sarkin Ose, Oba Moses Bakare dukan tsiya.
Matasan ba su tsaya a iya kan sarkin ba, an rahoto cewa sun yi wa matar sarkin duka, kuma suka fara yi mata tsirara, tare da yiwa yarima Victor jina-jina.
Duk da cewa har yanzu ba a san musabbabin faruwar lamarin ba, amma dai wani mazaunin garin ya ce dama matasa suna kullace da Oba Moses Bakare.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

