Martanin Tambuwal da Sauran Manyan 'Yan Siyasa kan Harin Amurka a Najeriya
FCT, Abuja - Kasar Amurka ta kawo hari kan wuraren da ake zargin 'yan ta'addan ISIS na amfani da su a Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce ya bayar da umarnin kai hare-haren, yana mai bayyana su a matsayin masu karfi da kuma hadari ga ‘yan ta’adda.

Source: Twitter
Ma'aikatar yaki ta Amurka ta tabbatar da kawo hare-haren a wani sakon da ta wallafa a shafinta na X a daren ranar Juma'a, 26 ga watan Disamban 2025.
Amurka ta kawo hari a Najeriya
Hare-haren da Amurka ta kawo Najeriya sun gudana ne a wasu sassan jihar Sokoto, inda ake zargin ‘yan ta’adda na fakewa suna kai hare-hare kan fararen hula da jami’an tsaro.
Harin dai shi ne irinsa na farko da sojojin Amurka suka kawo Najeriya tun bayan da gwamnatin kasar ta fara zargin ana muzgunawa Kiristoci a kasar ta yankin Afrika ta Yamma.
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da hare-haren da aka kai inda ya ce an kai jerin hare-haren da aka tsara sosai.
Trump ya bayyana cewa ma’aikatar tsaron Amurka ce ta jagoranci hare-haren domin lalata karfin ‘yan ta’addan ISIS da ke yankin.
Najeriya ta sahela wa Amurka kawo hari
Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar, ya tabbatar da cewa an gudanar da aikin da sahalewar Najeriya gaba daya.
Ambasada Yusuf Tuggar ya jaddada cewa hare-haren ba su karya ikon kasar Najeriya ba, kuma ba su da nasaba da nuna wariya ta addini.
Me 'yan siyasan Najeriya suka ce kan harin Amurkan?
Biyo bayan hare-haren da Amurka ta kawo, manyan 'yan siyasa sun fito sun yi martani kan lamarin.
Wasu daga cikinsu sun bukaci jama'a su kwantar da hankulansu tare da nuna goyon baya ga duk wani shiri da hadin gwiwa da zai taimaka wajen kawar da matsalar rashin tsaro a Najeriya.
1. Shehu Sani
Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya nuna goyon baya ga harin idan har an kawo shi ne tare da hadin gwiwar hukumomin Najeriya.

Kara karanta wannan
Bayan Sakkwato, an jero jihohi 7 da ya kamata Amurka ta kawo hari a Arewacin Najeriya
A wani rubutu da ya yi a shafinsa na X, ya nuna damuwa kan yadda 'yan ta'adda suka dade sun addabar mutane a Najeriya.
“Idan har da gaske ne hare-haren soji da aka kai kan sansanonin ’yan ta’adda a Arewa maso Yammacin Najeriya aiki ne na hadin gwiwa da ‘hukumomin Najeriya’ kamar yadda rundunar US AFRICOM ta wallafa a shafinta na X da aka tantance, to wannan mataki abin a yaba ne."
"’Yan ta’adda sun zama kamar cutar daji a wannan yanki na kasarmu. Suna rayuwa ba imani. Labarin da ake yadawa cewa wadannan miyagun ’yan ta’adda suna kai hari ne kan mabiya addini guda daya kawai, karya ce tsagwaronta kuma mai yaudarar jama’a."
"Bugu da kari, hakikanin tsaro da zaman lafiyar kasarmu na hannunmu ne, ba na Amurka ko wata kasa ta waje ba. Za su iya kai hare-hare tare da mu ko su kadai, amma ba za su iya yaki a yakinmu har abada ba.”
- Shehu Sani
2. Festus Keyamo
Ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya nuna goyon bayansa kan harin da Amurka ta kawo.

Source: Facebook
Jagoran na APC a Delta ya bayyana a shafinsa na X cewa wanda yake da matsala, kuskure ne ya ki karbar tayin taimako, idan an yi niyyar taimaka masa.
“Idan gidanka yana ci da wuta, to wauta ce ka hana duk wanda ke da abin kashe wuta shigowa ya taimaka ya kashe wutar."
"Babu wata ma’ana ka fara tunanin sirrin gidanka a lokacin da wutar ke gab da cinye iyalanka.”
- Festus Keyamo
3. Aminu Waziri Tambuwal
Sanata mai wakiltar sokoto ta Kudu, Aminu Waziri Tambuwal, ya bukaci jama'a su kwantar da hankulansu kan hare-haren da Amurka ta kawo.
Tambuwal a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X ya muhimmancin kare lafiyar fararen hula, tare da yin kira ga hadin kan al’umma.
“Yana da matukar muhimmanci a kwantar wa jama’a da hankali cewa ayyukan yaki da ta’addanci ana nufin su ne kan ’yan ta’adda da masu aikata laifuka da ke barazana ga tsaronmu baki daya, ba kan fararen hula marasa laifi ba, wadanda su ma su ne ke fama da matsalar rashin tsaro."
"Kare rayukan fararen hula shi ne mafi muhimmanci kuma ginshiki a duk wani sahihin aikin tsaro.”
4. Ladan Salihu
Jigo a jam'iyyar ADC kuma tsohon shugaban gidan rediyo Najeriya Kaduna, Ladan Salihu, ya nuna goyon baya ga yunkurin hadin gwiwa don yaki da 'yan ta'adda.
Ladan Salihu ya bayyana a shafinsa na X cewa harin na Amurka ba a kai shi a inda ya dace ba.
“Ina goyon bayan duk wani yunkuri na hadin gwiwa wajen yaki da ’yan ta’adda. A shekarar 2025, Jabo ba ta fuskanci ta'addanci ko ayyukan ISWAP ko da sau daya ba. Haka nan babu rikicin manoma da makiyaya."
"Ina sa ran harin ya shafi Turji da sauran manyan jagororin ’yan ta’adda da aka sani a Arewa maso Gabas. Amma mutanen kauyen sun ba da rahoton ganin burbushin makamai masu linzami a kusa da wani babban rami."
"Ba a samu asarar rai ko rauni ba. Shin harin don daukar hankalin kafafen labarai aka yi shi ko kuwa don aika wani sako da ba a iya fahimta ba?"
"Dole ne hedikwatar tsaro ta kasa ta gudanar da bincike tare da gabatar wa ’yan Najeriya rahoton halin da ake ciki kan wannan aiki. Godiya ta tabbata ga Allah da makaman ba su fadi kan asibiti ko gidajen fararen hula na Jabo ba.”
- Ladan Salihu
5. Sanata Ali Ndume
Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume ya yaba kan matakin da Amurka ta dauka na kawo farmaki kan 'yan ta'adda a Najeriya.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta ce Sanata Ndume ya bukaci gwamnatin tarayya ta fadada hadin gwiwar soji da Amurka zuwa Arewa maso Gabas.
Sanata Ndume ya bayyana cewa idan aka fadada irin wannan hadin gwiwa zuwa Arewa maso Gabas, za a raunana ISWAP da Boko Haram sosai.
6. Bolaji Abdullahi
Jam’iyyar ADC ta bakin kakakinta na kasa, Bolaji Abdullahi ta bayyana hare-haren saman da Amurka ta kawo a matsayin shaidar gazawar shugabancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Bolaji ya ce harin ya nuna a fili rashin kwarewa da gazawar gwamnatin Shugaba Tinubj wajen tinkarar tabarbarewar matsalolin tsaro a Najeriya.
ADC ta yi gargadin cewa barin sojojin kasashen waje su rika kawo hari kai tsaye a cikin Najeriya abu ne da ba zai dore ba, kuma a nan gaba hakan na iya raunana muradun tsaro na kasar nan.
7. Omoyele Sowore
Dan gwagwarmaya kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore, ya soki gwamnatin tarayya kan hare-haren saman da Amurka ta kai kan ’yan ta’adda a Najeriya.
Omoyele Sowore ya bayyana cewa lamarin ya tona asirin abin da ya kira raunin shugabanci da rashin tasiri.
Tsohon dan takarar shugaban kasan ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X (tsohon Twitter) a ranar Juma’a, 26 ga watan Disamban 2025.
Sowore ya kalubalanci ikirarin da hukumomin Najeriya suka yi cewa suna sane da harin kuma an gudanar da shi ne tare da sahalewarsu.
Ya yi zargin cewa hare-haren sun faru ne ba tare da sahihiyar amincewa ko cikakkiyar yardar Najeriya ba.
Natijar harin Amurka a Najeriya
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan majalisa a Amurka, Riley Moore, ya yi tsokaci kan harin da kasarsa ta kawo Najeriya.
Riley Moore ya bayyana cewa hare-haren da Amurka ta kawo sun taimaka wajen hana kisan Kiristoci a lokacin Kirsimeti.
'Dan majalisar ya bayyana cewa a lokutan Kirsimeti biyu da suka gabata an kashe Kiristoci a Najeriya, amma a bana harin da Amurka ta kawo ya hana aukuwar hakan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng




