Majalisa Ta Mika wa Tinubu Bukatar Janye Aiwatar da Sabuwar Dokar Haraji a 2026

Majalisa Ta Mika wa Tinubu Bukatar Janye Aiwatar da Sabuwar Dokar Haraji a 2026

  • Majalisar Wakilan Najeriya ta bukaci Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu da ya dakatar da batun fara aiwatar da dokar haraji a watan Janairu na shekarar 2026
  • An nemi a dakatar da aiwatar dokokin ne bayan surutu ya yi yawa game da zargin cewa akwai bambanci tsakanin wacce Majalisa da gyara da wacce aka sa wa hannu
  • Tuni majalisa ta kafa kwamiti da zai bibiyi lamarin, domin gano yadda aka samu matsala a dokokin harajin da ake cece-kuce a kansu a 'yan kwanakin nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT AbujaMajalisar Wakilai ta bukaci a dakatar da aiwatar da sababbin dokokin gyaran haraji na Najeriya, sakamakon zargin cewa an sauya nau’ukan dokokin da aka wallafa.

Wannan na zuwa ne bayan Majalisar Tarayya ta amince da dokokin tare mika wa Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya sanya mata hannu, amma daga baya aka ce an hango matsala

Kara karanta wannan

Gwamnati ta fadi ainihin dajin da bama baman Amurka suka sauka a Najeriya

Majalisar Wakilai ta nemi Tinubu ya jingine fara aiwatar da dokar haraji
Zauren Majalisar Wakilan Najeriya, Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Abbas Tajudeen/Bayo Onanuga
Source: Facebook

Jaridar Aminiya ta wallafa cewa wannan zargi ya tayar da kura a cikin Majalisa da wajen ta, inda mutane ke tambayar inganci da gaskiyar tsarin zartar da dokoki da wallafa su a hukumance.

Majalisa na son a dakatar da dokar haraji

The Guardian ta wallafa cewa Majalisar Wakilai ta kaddamar da kwamitin bincike mai karfi domin gano ko an yi wa dokokin gyaran haraji sauyi ba bisa ka’ida ba bayan an zartar da su.

Shugaban marasa rinjaye a Majalisar Wakilai, Hon. Kingsley Chinda, ta cikin wata sanarwa da ya fitar ya bayyana cewa wannan lamari babbar matsala ce a kundin tsarin mulki.

Majalisar wakilai ta ce a jira a kammala duba dokar harajin da aka wallafa
Wasu daga cikin 'yan majalisar wakilai a zauren majalisa Hoto: House of Representatives
Source: Facebook

A sanarwar da aka fitar a ranar Litinin, Hon. Kingsley Chinda ya jaddada cewa wannan lamari ya wuce batun siyasa, kuma akwai bukatar a yi masa duba na tsanaki.

Ya yi gargadin cewa duk wani yunƙuri na sauya dokokin da Majalisa ta zartar, hari ne kai tsaye ga dimokuradiyya.

Kara karanta wannan

Sanata Ndume na neman dawo da hannun agogo baya game da sababbin dokokin haraji

Majalisa ta girgiza kan dokar haraji

Hon. Kingsley Chindace ya bayyana cewa zargin ya girgiza ’yancin kai da sahihancin Majalisar Tarayya, yana mai tabbatar wa ’yan Najeriya cewa marasa rinjaye a majalisa za su goyi bayan a yi cikakken bincike.

Hon. Chindace ya jaddada cewa bisa tsarin doka, Majalisar Tarayya kaɗai ke rike da sahihan nau’ikan dokokin da aka zartar a Tarayya.

Saboda haka, ’yan majalisar sun bukaci ’yan Najeriya su yi watsi da duk wani kwafin dokokin haraji da ke yawo wanda ba ya dauke da sa hannun Sakatare na Majalisar Tarayya da Shugaban kasa.

Sun kara da gargadi cewa duk wani yunkuri na tilasta wa jama’a dokoki na bogi ko wadanda aka sauya, hari ne ga nauyin da kundin tsarin mulki ya dora wa Majalisa.

Hon. Kingsley Chinda ya bukaci gwamnatin tarayya ta dakatar da aiwatar da dokokin harajin har sai an kammala bincike tare da tabbatar da ingantattun dokokin da za a aiwatar.

Kara karanta wannan

'An kusa gama gyara lantarkin Najeriya,' Ministan makamashi ya yi albishir

Majalisa ta fadi matsayarta kan sayen kuri'a

A baya, mun wallafa cewa Majalisar wakilai ta yi watsi da wani kudiri domin tsaftace harkokin zaɓe a Najeriya, inda ta ƙi amincewa da sashen haramta ba wa wakilan jam’iyya kuɗi a zaben fitar da gwani.

Rahoton gyaran dokar ya ƙunshi wani sashe da ke cewa duk wanda ya ba wakili kuɗi ko wata alfarma domin canza sakamakon zaɓen fitar da gwani ko babban taron jam’iyya, ya aikata laifin da ya kamata a hukunta shi.

Sai dai bayan Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu, ya nemi a kaɗa ƙuri’a kan wannan sashe, dukkannin ’yan majalisar suka ƙi amincewa da shi, wanda ke nufin an watsar da batun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng