Garkuwa da Mutane: Sojojin Najeriya Sun Gwabza Kazamin Dada 'Yan Bindiga a Kano
- Dakarun soji sun ceto Rabiu Alhaji Halilu tare da fatattakar 'yan bindiga bayan wani kazamin artabu a iyakar jihohin Kano da Katsina
- Rundunar sojojin ta Brigade 3 Kano ta bayyana cewa an kai samamen ne bayan samun sahihan bayanan sirri na motsin 'yan bindiga
- Hakazalika, dakarun Operation Hadin Kai ta kashe 'yan ta'adda 438 tare da kwace na'urorin sadarwa na Starlink guda 300
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Dakarun hadin gwiwa na JTF da ke Faruruwa sun ceto wani mutum da aka sace bayan nasarar wani sumame na tsaro da suka kai a kan iyakar Kano–Katsina da safiyar Lahadi.
Rundunar sojojin Najeriya ta Brigade 3 Kano ta bayyana cewa an kai samamen ne bayan samun sahihan bayanan sirri na motsin 'yan bindiga a yankunan Daurawa da ke Kira zuwa Kano.

Source: Twitter
Sojoji sun fafata da 'yan bindiga a Kano
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar sojin Najeriya ta Brigade ta 3, Kano, Manjo Zubair Babatunde, ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN).
A cewarsa, dakarun da ke aiki daga Forward Operating Base (FOB) Yankwada sun gaggauta hada rundunar sintiri domin tare hanyar ‘yan bindigar a gefen iyakar Kano da Katsina.
“Da isarsu yankin Ungwan Dogo/Ungwan Tudu, dakarun sun yi artabu da ‘yan bindigar tare da fafatawa a wata mummunar musayar wuta.
“An rinjayi ‘yan bindigar tare da tilasta musu tserewa cikin rudani zuwa Karamar Hukumar Matazu ta jihar Katsina,” in ji shi.
Manjo Babatunde ya ce a yayin artabun, dakarun sun yi nasarar ceto wani da aka sace mai suna Rabiu Alhaji Halilu, mai shekaru 38.
'Yan bindiga sun tsere zuwa cikin Katsina
Ya bayyana cewa Halilu ya samu raunin harbin bindiga a ƙafarsa a lokacin da yake hannun ‘yan bindigar, inda aka gaggauta kai shi Cibiyar Lafiya ta JTF Faruruwa, inda a halin yanzu yake karɓar magani.
Abubuwan da aka kwato a wajen sun haɗa da babura uku da ‘yan bindigar suka bari yayin tserewarsu, da kuma adadin shanu da ba a bayyana yawansu ba, waɗanda ake zargin sun sato su ne.
Ya ƙara da cewa dakarun sun ƙara zafafa tsaro da sintiri a yankin domin hana sake aikata laifuka da tabbatar da dorewar tsaro a al’ummomin kan iyaka.
A wani labarin kuma, ci gaba da kai farmaki da dakarun hadin gwiwa na Arewa maso Gabas, Operation Hadin Kai (OPHK) ke yi na ci gaba da haifar da gagarumar nasara.

Source: Original
Ayyukan sojoji a Arewa maso Gabas
Rahotan da Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X, sun nuna cewa ba ƙasa da ‘yan ta’adda 438 na Boko Haram da ISWAP aka kashe cikin tsawon watanni bakwai.
Kwamandan rundunar ayyuka ta OPHK, Arewa maso Gabas Sashi na 1, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, ne ya bayyana hakan a ranar Asabar a Maiduguri, yayin liyafar Kirsimeti ta shekarar 2025 da aka shirya wa dakarun da ke fagen daga.
A cewarsa, a wannan lokaci an kwato makamai iri-iri guda 254, da kuma kusan na’urorin sadarwa na Starlink 300, waɗanda ‘yan ta’adda ke amfani da su wajen inganta umarni, kulawa da tattara bayanan sirri.
Ya ƙara da cewa dakarun sun kuma ceto fararen hula 366, ciki har da mata da yara, daga maboyar ‘yan ta’adda daban-daban a yankin Arewa Maso Gabas.
'Yan sanda sun fafata da 'yan bindiga
A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan sandan sun ceto Geoffrey Akume, wani mutumi da masu garkuwa da mutane suka sace a ranar Kirsimeti a Benue.
Kakakin rundunar, DSP Udeme Edet, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Alhamis, wadda aka bai wa manema labarai a Makurdi.
Ta bayyana cewa wanda aka ceto yana kan hanyarsa daga Gboko zuwa Makurdi lokacin da wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka tare shi a Tiortu.
Asali: Legit.ng


