Sulhu Ya Yi Rana: 'Yan Bindiga Sun Sako Mutanen da Suka Sace a Katsina
- An gudanar da zaman tattaunawa don yin sulhu da 'yan bindigan da ke kai hare-hare kan mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba a jihar Katsina
- Bayan cimma yarjejeniya kan sulhun, 'yan bindiga sun sako wasu mutane 10 da suka yi garkuwa da su a wani kauye na karamar hukumar Malumfashi
- Zaman sulhun dai ya hada da shugaban karamar hukuma, sarakunan gargajiya da wasu rikakkun jagororin 'yan bindiga da ke cikin daji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - 'Yan bindiga sun sako wasu mutanen da suka yi garkuwa da su a jihar Katsina.
'Yan bindigan sun sako mutane 10 da aka sace daga kauyen Danjanku da ke karamar hukumar Malumfashi, bayan cimma yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla tsakanin al’ummomin yankin da miyagun masu dauke mutane.

Source: Facebook
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
An yi tattaunawa da 'yan bindiga a Katsina
Rahotanni sun an gudanar da tattaunawar zaman lafiyar ne a ranar Juma'a 26 ga watan Disamban 2025 da misalin karfe 11:00 na safe.
An gudanar da zaman sulhun ne karkashin shirin Operation Safe Corridor, a kauyen Yantumaki da ke karamar hukumar Danmusa.
A cewar majiyoyi, taron ya hada shugaban karamar hukumar Malumfashi, sarakunan gargajiya da kuma shugabannin ’yan bindiga da suka hada da Munore, Wada Yellow da Yalmi.
Tattaunawar ta mayar da hankali ne kan dawo da zaman lafiya, dakatar da rikice-rikice, samar da tsarin mutunta juna da kuma tabbatar da ’yancin zirga-zirga a yankin.
An samu matsaya bayan zaman sulhu
Majiyoyin sun ce taron ya kare ne bayan dukkan bangarorin sun amince su mutunta sharuddan yarjejeniyar, lamarin da ya kai ga sakin mutanen 10 da aka sace tun da fari.
Hukumomi sun kara da cewa ana ci gaba da sanya ido a yankin domin tabbatar da dorewar zaman lafiya da kuma hana sake bullar matsalolin tsaro a yankin.

Source: Original
Karanta wasu labaran kan 'yan bindiga
- Gwamna Aliyu ya kaddamar da sababbin dabaru na kawo karshen ƴan bindiga a Sokoto
- Kwara: Babban Sarki da ƴan bindiga suka sace ya tsira bayan shafe kwana 25
- Sojoji sun cafke hatsabibin jagoran 'yan bindiga da yake addabar jihohin Arewa
- 'Yan bindiga sun yi aika aika bayan kai wani harin ta'addanci a Zamfara
'Yan bindiga sun farmaki jami'an NSCDC
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu da ake zargin 'yan ta'adda ne sun farmaki jami'an hukumar NSCDC a jihar Niger da ke yankin Arewa ta Tsakiya.
Hukumar NSCDC ta tabbatar da cewa 'yan ta'addan sun kai hari kan shingen binciken jami’anta a kan titin Wawa-Babanla na karamar hukumar Borgu a jihar Niger.
Maharan sun rika amfani da fitilun hannu wajen gano duk wanda ke motsi kafin su buɗe wuta, lamarin da ya tilasta jami’an tsaron yin dabarun kaucewa harbi tare da neman mafaka.
Asali: Legit.ng

