Dalilin Donald Trump na Jinkirta Kai Hari a Najeriya zuwa Ranar Kirsimeti

Dalilin Donald Trump na Jinkirta Kai Hari a Najeriya zuwa Ranar Kirsimeti

  • Shugaban Amurka Donald Trump ya magantu bayan kai harin sojojinsa kan wasu 'yan ta'adda a jihar Sokoto da ke Najeriya
  • Trump ya ce ya sauya ranar kai harin soji kan ’yan ISIS a Najeriya zuwa ranar Kirsimeti domin wani dalili na musamman.
  • Masu lura da al’amura sun ce harin na iya kasancewa wata dabara don faranta ran Kiristocin masu ra’ayin mazan jiya a Amurka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Rahotanni sun nuna cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ne ya sauya ranar kai harin sojin Amurka kan ’yan ta'adda a Najeriya zuwa ranar Kirsimeti.

Shugaba Trump ya ce shi ya hana kai hari mako daya kafin wannan lokaci saboda farantawa wasu Kiristoci rai a duniya.

Trump ya fadi dalilin kai hari Najeriya ranar Kirsimeti
Shugaban Amurka, Donald Trump. Hoto: @RealDonaldTrump.
Source: Getty Images

A wata hira da kafar yada labarai ta Amurka, Politico, wadda aka fitar ranar Juma’a, Trump ya ce an shirya kai harin tun ranar Laraba amma ya dage shi.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta fadi ainihin dajin da bama baman Amurka suka sauka a Najeriya

Harin da Donald Trump ya kawo Najeriya

Trump ya bayyana a ranar Alhamis 25 ga watan Disambar 2025 cewa an kai hare-haren masu ƙarfi kan ’yan bindigar ISIS da yake suna kashe Kiristoci.

Ya ce hare-haren sun kasance “masu muni da ƙarfi,” inda aka kai farmaki kan ’yan ta’addan da ke kai munanan hare-hare, musamman kan Kiristoci, a wasu sassan Najeriya.

Majiyoyi sun ce harin ya shafi kauyen Jabo da ke karamar hukumar Tambuwal a Sokoto da kuma yankin Offa da ke jihar Kwara.

Trump ya ce ya kawo hari Najeriya a matsayin kyautar Kirsimeti
Shugaba Donald Trump na kasar Amurka. Hoto: Donald J Trump.
Source: Getty Images

Dalilin dage harin zuwa ranar Kirsimeti

Rahoton ya ce Trump ya bayar da umarnin dage harin na kwana guda “saboda wasu dalilai,” yana mai cewa ya so ya sanya harin a ranar Kirsimeti.

Trump ya ce:

“Na ce a’a, mu ba su kyautar Kirsimeti. Ba su yi tsammanin hakan ba, amma mun buge su ƙwarai. An lalata kowane sansani.”

A halin yanzu, ana nuna damuwa sosai a tsakanin Kiristocin masu ra’ayin mazan jiya a Amurka kan zargin ana tsananta wa Kiristoci a Najeriya, cewar The Guardian.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda daga ketare na 'shirin' kawo hari jihohin Arewa 4 a Najeriya

Hangen da masu sharhi ke yi kan lamarin

Masu sharhi kan harkokin siyasa sun ce sabon harin da Amurka ta kai na iya nuna ƙoƙarin Trump na neman ƙarin goyon baya daga mabiyansa na addinin Kirista.

Sun ce batun kare Kiristoci a ƙasashen waje na daga cikin muhimman abubuwan da ke jan hankalin magoya bayan Trump a Amurka da ketare gaba daya.

Tambuwal ya magantu kan harin Amurka a Sokoto

Mun ba ku labarin cewa Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya yi tsokaci kan hare-haren sama da Amurka ta kawo a mazabar da yake wakilta a jihar Sokoto.

Aminu Waziri Tambuwal ya jaddada muhimmancin kare rayukan fararen hula tare da kira ga jama'a su bayar da hadin kai domin ganin an kawo karshen matsalolin tsaro a kasar.

Tsohon gwamnan ya kuma bukaci jama'a da su kwantar da hankulansu yayin da hukumomin da suka dace ke ci gaba da ayyukansu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.