Tinubu Ya Yi Albishir ga ’Yan Najeriya game da Karbo Wasu Jiragen Yaki daga Amurka
- Shugaba Bola Tinubu ya bayyana shirin gwamnatinsa wurin tabbatar yaki da ta'addanci domin wanzar da zaman lafiya
- Tinubu ya ce Najeriya ta sayi jiragen yaƙi huɗu masu saukar ungulu daga Amurka, waɗanda za su iso ƙasar nan nan gaba kaɗan
- Shugaban ya ce matsalar tsaro ta kai matakin damuwa a duniya, lamarin da ya jawo haɗin gwiwa da ƙasar Amurka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Lagos - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da shirin kawo wasu jiragen yaki daga Amurka domin yaki da ta'addanci.
Tinubu ya bayyana cewa jiragen yaƙi masu saukar ungulu huɗu da gwamnatin tarayya ta sayo daga ƙasar Amurka za su iso Najeriya nan gaba kaɗan.

Source: Twitter
Tinubu ya koka kan karuwar matsalar tsaro
Ya bayyana hakan ne yayin ganawa da kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN a Lagos yayin da ta kai masa ziyara, cewar Channels TV.
Shugaban ya fadi haka ne a daidai lokacin da ƙasar ke fama da ƙalubalen rashin tsaro da ta’addanci, wanda ke ci gaba da bazuwa a sassa daban-daban na Najeriya.
Tinubu ya ce matsalar tsaro ta kai wani matsayi na damuwa a idon duniya, lamarin da ya sa aka samu buƙatar shigar gwamnatin Amurka cikin yaƙin da ake yi da ’yan ta’adda a Arewa maso Yammacin ƙasar.
Ya ce wannan haɗin gwiwa ne ya haifar da kai hare-haren sama cikin tsanaki kan wuraren ’yan ta’adda a wasu yankuna a jihar Sokoto da Kwara.

Source: Facebook
Albishir da Tinubu ya yi ga 'yan Najeriya
Yayin ganawa da tawagar Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ƙarƙashin jagorancin Shugabanta, Rabaran Daniel Okoh, Tinubu ya ce gwamnatinsa ta riga ta ba da umarnin sayen jiragen yaƙin daga Amurka.
Ya ƙara da cewa duk da jinkirin isowarsu, gwamnati ta nemi taimako daga ƙasar Turkiyya domin ƙara ƙarfafa tsaron ƙasar, cewar Tribune.
Shugaban ya amince cewa jinkirin kayan aikin sojoji na iya shafar yadda jama’a ke kallon ƙudirin gwamnatinsa na magance matsalar tsaro.
Tabbacin da Tinubu ya ba 'yan Najeriya
Tinubu ya kuma tabbatar da cewa za a kafa ’yan sandan al’umma da na jihohi da zarar Majalisar Tarayya ta kammala dokokin da suka dace.
Ya ce kayan aikin sojoji suna da tsada kuma ba sa samuwa kai tsaye, amma duk da haka gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen dawo da zaman lafiya da bunƙasar tattalin arziki a ƙasar.
Gwamnatin Sokoto ta magantu kan harin Amurka
Kun ji cewa gwamnatin Sokoto ta tabbatar da harin da aka kai a wasu sassan ƙananan hukumomi a jihar da Amurka ta yi.
Hadimin gwamna Ahmed Aliyu ya ce harin ya shafi yankin Jabo, kuma gwamnati ta ce babu fararen hula da suka mutu ko suka jikkata.
Gwamnatin Sokoto ta yi kira ga jama’a da su ci gaba da ba da bayanan sirri domin samar da tsaro mai ɗorewa a jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

