An Kama Kasurgumin 'Dan Bindiga Mai Nuna Miliyoyin Kudi a Intanet

An Kama Kasurgumin 'Dan Bindiga Mai Nuna Miliyoyin Kudi a Intanet

  • Rundunar ’yan sandan Najeriya ta sanar da cafke wasu manyan jagororin garkuwa da mutane a Jihar Kwara, bayan nasarar wani aikin aka gudanar
  • Daya daga cikin waɗanda aka kama shi ne mutumin da ya yi fice a kafafen sada zumunta, inda aka gan shi a bidiyo yana ta nuna makamai da tarin kuɗi
  • Jami’an tsaro sun kuma ƙwato babur, kuɗin fansa da bindiga kirar AK-47, abin da ya ƙara bayyana hanyoyin da ƙungiyar ke bi wajen aikata laifuffuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kwara – Rundunar ’yan sandan Najeriya ta sanar da cafke wasu shahararrun ’yan fashi da masu garkuwa da mutane guda biyu da ake zargi suna da hannu a manyan laifuffuka a jihohin Katsina, Zamfara, Neja da Kwara.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta fadi ainihin dajin da bama baman Amurka suka sauka a Najeriya

A cewar rundunar, an kama mutanen ne a wani aikin sirri da aka gudanar a yankin Komen–Masallaci da ke Karamar Hukumar Kaiama a Jihar Kwara, bayan dogon bincike kan ayyukan wata ƙungiya mai haɗari.

Dan bindiga Siddi da aka aka kama a Kwara
Dan bindiga mai bidiyo a intanet da aka kama a Kwara. Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Sanarwar ta fito ne a sakon da kakakin rundunar, CSP Benjamin Hundeyin, ya wallafa a X, inda ya bayyana cewa an aiwatar da aikin ne a ranar 19, Disamba, 2025.

An cafke dan bindiga mai bidiyo a intanet

Sanarwar ta ce jami’an FID–IRT sun gudanar da aikin ne tare da haɗin gwiwar jami’an rundunar ’yan sandan Jihar Kwara, inda suka yi nasarar kama mutanen biyu.

An bayyana sunayen waɗanda aka kama da Abubakar Usman, mai laƙabi da Siddi, mai shekaru 26, da kuma Shehu Mohammadu, mai laƙabi da Gide, mai shekaru 30.

Rahoton TVC ya nuna cewa dukkaninsu an kama su ne a ƙauyen Komen–Masallaci, Kaiama, a lokacin samamen da aka yi.

Rundunar ta ce binciken farko ya nuna cewa mutanen biyu manyan mambobi ne a wata ƙungiyar fashi da garkuwa da mutane da ke addabar al’umma a jihohi da dama na Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

An baza 'yan sanda ta ko ina a Maiduguri bayan harin bam a masallaci

Bidiyon da ya jawo hankalin jama’a

A cikin bayaninta, rundunar ta tunatar da cewa ɗaya daga cikin waɗanda aka kama, Abubakar Usman, shi ne mutumin da aka gani kwanan nan a wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, inda yake ta nuna bindigogi da tarin kuɗi.

Wannan bidiyo, a cewar rundunar, ya taimaka wajen ƙarfafa bincike kan hanyoyin samun kuɗin ƙungiyar da kuma inda suke ɓoye.

Abubuwan da 'yan sanda suka ƙwato

Rundunar ta bayyana cewa yayin farmakin, jami’an tsaro sun ƙwato muhimman kayayyaki da suka haɗa da babur kirar Honda Ace 125, mai launin ja, wanda kimarta ta wuce Naira miliyan 1.

An ce bincike ya nuna cewa an sayi babur ɗin ne da kuɗin fansa da aka karɓa daga hannun waɗanda aka sace. Haka kuma, an ƙwato kuɗi N500,000 a hannusu, waɗanda aka ce saura ne daga kuɗin fansa.

Baya ga haka, jami’an sun ƙwato bindiga kirar AK-47 guda ɗaya tare da wata jaka da ke ɗauke da harsasai 20 da suke aiki da su.

Kara karanta wannan

Gwamna Aliyu ya kaddamar da sababbin dabaru na kawo karshen ƴan bindiga a Sokoto

Sufeton 'yan sandan Najeriya
Shugaban 'yan sanda na kasa a wani taro. Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

An baza 'yan sanda a Maiduguri

A wani labarin, mun kawo muku cewa an kara yawan jami'an tsaro a Maiduguri bayan harin kunar bakin wake da aka kai wani masallaci.

Rahotanni sun bayyana cewa an kara dakarun 'yan sanda 1,000 domin tabbatar da tsaro a bukukuwan karshen shekara da ake yi.

Rundunar 'yan sanda ta ce za ta tabbatar da komai ya tafi lafiya yayin da ta bukaci jama'a da su rika sakin bayanan 'yan ta'adda domin kama su.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng