Gwamnati Ta Fadi Ainihin Dajin da Bama Baman Amurka Suka Sauka a Najeriya

Gwamnati Ta Fadi Ainihin Dajin da Bama Baman Amurka Suka Sauka a Najeriya

  • Gwamnatin tarayya ta ce hare-haren hadin gwiwa da Amurka sun kai ga manyan sansanonin 'yan kungiyar IS a dajin Bauni da ke Tangaza
  • Ministan yada labarai na kasa, Mohammed Idirs ya bayyana cewa an yi aikin ne bayan cikakken sahalewar shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
  • Mohammed Idris ya ce burbudin makaman da aka harba ne suka faɗa yankunan Jabo da Offa kuma babu fararen hula da suka rasa rai a sanadiyyar hakan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fito ta fayyace ainihin wuraren da aka kai hare-haren hadin gwiwa da Amurka a yaki da ta’addanci, bayan da aka samu ce-ce-ku-ce da rade-radi kan sahihancin aikin da tasirinsa.

Wasu masu suka sun yi zargin cewa harin bai cimma nasara ba, inda suka ce wuraren fararen hula ne aka kai wa farmaki, ba tare da wani gagarumin natija a kan ‘yan ta’adda ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Sokoto ta fito da bayanai kan harin da Amurka ta kai jihar

Wajen da makaman Amurka suka sauka a Najeriya
Wajen da makaman Amurka suka sauka a Sokoto da Ministan yada labarai. Hoto: Mohammed Idris|Zagazola Makama
Source: Facebook

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa a X cewa bayanan da ke yawo ba su dace da gaskiyar abin da ya faru ba, yana mai jaddada cewa an kai hari ne kan manyan maboyar ‘yan kungiyar IS.

Inda Amurka ta kai hari a Najeriya

A cewar sanarwar, gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar gwamnatin Amurka sun gudanar da kyawawan hare-haren da aka tsara daidai kan manyan sansanonin ‘yan kungiyar IS guda biyu da ke cikin dajin Bauni, a yankin Tangaza na Jihar Sokoto.

Ministan ya ce bayanan sirri sun tabbatar da cewa wadannan wurare na zama cibiyoyin taruwa da shirya ayyukan ta’addanci, inda ‘yan IS daga yankin Sahel ke shigowa Najeriya tare da hadin gwiwar masu goyon bayansu na cikin gida.

Ya bayyana cewa daga wadannan maboyar ne ake tsara manyan hare-haren ta’addanci da ake shirin kai wa cikin Najeriya, lamarin da ya sa aka dauki matakin kai hare-haren cikin tsari da kwarewa.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda daga ketare na 'shirin' kawo hari jihohin Arewa 4 a Najeriya

Lokacin da Amurka ta kai hari Najeriya

Sanarwar ta ce an aiwatar da hare-haren ne tsakanin karfe 12:12 zuwa 01:30 na dare a ranar Juma’a, 26, Disamba, 2025, bayan samun cikakken sahalewar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

An kara da cewa aikin ya gudana ne karkashin tsauraran tsare-tsaren umarni da kulawa, tare da cikakken goyon bayan rundunar sojin Najeriya, karkashin sa ido na Ministocin tsaro da na harkokin waje da kuma Babban hafsan tsaro.

Ministan yada labarai, Mohammed Idris
Ministan yada labarai na wani jawabi. Hoto: Mohammed Idris
Source: Twitter

Ministan ya ce an kaddamar da hare-haren ne daga dandamalin ruwa da ke Tekun Guinea, bayan dogon shiri, tattara bayanan sirri da bincike na musamman kan wuraren da aka nufa.

Burbudin makamai sun faɗa Jabo da Offa

Daily Trust ta wallafa cewa a cewar sanarwar, an yi amfani da jiragen yaki marasa matuka na MQ-9 Reaper, inda aka harba makamai masu bin tsarin GPS guda 16, wanda ya yi sanadin lalata sansanonin ‘yan IS da aka nufa.

Sai dai yayin aiwatar da aikin, wasu burbudin makamai da aka yi amfani da su sun faɗa garin Jabo da ke Karamar Hukumar Tambuwal a Sokoto, da kuma Offa a Jihar Kwara, kusa da wani otal.

Kara karanta wannan

Abin da gwamnatin Najeriya ta ce game da harin Amurka a Sakkwato

Gwamnatin Sokoto ta yi bayani kan harin Amurka

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin jihar Sokoto ta yi bayani game da harin da Amurka ta kai wani yanki na karamar hukumar Tambuwal.

Rahotanni sun bayyana cewa mai magana da yawun gwamna Ahmed Aliyu ya bayyana cewa harin bai kashe fararen hula a kauyen ba.

A bayanin da gwamnatin jihar ta yi, ta yi kira ga jama'a da su rika ba jami'an tsaro bayanan sirri domin samun damar dakile 'yan ta'adda.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng