Bayan Harin Amurka, Akpabio Ya Fadi Lokacin Kawo Karshen Matsalar Tsaro

Bayan Harin Amurka, Akpabio Ya Fadi Lokacin Kawo Karshen Matsalar Tsaro

  • Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya tabo batun matsalar rashin tsaron da ake fama da ita
  • Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa matsalar rashin tsaro ta kusa zama tarihi a Najeriy nan ba da jimawa ba
  • Tsohon gwamnan ya kuma bukaci 'yan Najetiya da su ci gaba da marawa gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Akwa Ibom - Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya yi magana kan matsalolin rashin tsaro.

Akpabio ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa za a kawar da ’yan bindiga da sauran matsalolin tsaro da ke addabar kasar nan, nan da shekarar 2026 da bayan haka.

Akpabio ya yi magama kan rashin tsaro
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da jami'a tsaro na sojoji Hoto: @SenateNGR, @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Jaridar The Nation ta ce ya yi wannan kiran ne a wajen wani taron addu’a da azumi da aka shirya domin girmama iyalan Akpabio.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya fadawa Tinubu tsarin da zai yi kan tsaro idan ya samu mulkin Najeriya

An shirya taron ne a Cocin Methodist ta Najeriya, Cathedral of Unity, Ukana Ikot Ntuen, da ke karamar hukumar Essien Udim a jihar Akwa Ibom.

Me Akpabio ya ce kan rashin tsaro?

A cikin wata sanarwa da mataimakinsa na musamman kan harkokin yada labarai, Anietie Ekong, ya fitar, an ambato shugaban majalisar dattawan yana cewa:

“Ina yi wa dukkan ’yan Najeriya fatan sabuwar shekara mai albarka da zaman lafiya. Ina so na tabbatar wa ’yan Najeriya cewa sabuwar shekarar za ta zo da sabon salo na zaman lafiya a kasarmu.”
"Saboda haihuwar Yesu Almasihu, za a fanshi ’yan Najeriya daga ta’addanci, ’yan bindiga da tayar da masu tayar da kayar baya a sabuwar shekara da ma bayan ta.”

- Godswill Akpabio

Akpabio ya yi kira ga 'yan Najeriya

Shugaban Majalisar Dattawan ya bukaci ’yan Najeriya, ba tare da la’akari da bambancin jam’iyyun siyasa ba, da su mara wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a yaki da ’yan bindiga da ’yan ta’adda.

Akpabio ya nuna kwarin gwiwar cewa sabuwar hadin gwiwa da kasashen waje za ta taimaka wajen murkushe matsalolin tsaro, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar da hakan.

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida ya ba wa gwamnonin Arewa mafita game da matsalar tsaro

Ya kuma jaddada muhimmiyar rawar da iyali ke takawa wajen samar da zaman lafiya da ci gaba, inda ya ce hadin kai shi ne ginshikin nasarar kowa.

Akpabio ya ce za a kawo karshen rashin tsaro
Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio Hoto: Godswill Obot Akpabio
Source: Facebook

A nata jawabin, matar shugaban majalisar dattawan, Ekaette Unoma Akpabio, ta karfafa gwiwar ’yan uwa da su rika tallafa wa juna ba tare da son kai ba, su ajiye son zuciya, su zauna cikin kauna da fahimtar juna.

Shi ma shugaban dangin Akpabio, Cif Ekan Akpabio, ya bukaci ’yan uwa da su ci gaba da mara wa Sanata Akpabio baya a matsayin jakada nagari na iyalan, karamar hukumar Essien Udim da kuma jihar Akwa Ibom.

Cif Akpabio ya kuma yi kira ga ’yan uwa da ke rike da mukaman siyasa da su kasance masu tunawa da asalinsu tare da fifita walwalar ’yan uwansu.

Shugaban majalisa ya gamu da hatsari

A wani labarin kuma, kun ji cewa tawagar ayarin motocin shugaban majalisar.dattawa, Godswill Akpabio, sun gamu da hatsari.

Hatsarin ya auku ne bayan wata tankar mai ta afkawa motoci lokacin da suke tafiya a jihar Oyo da ke Kudancin Najeriya.

Shugaban majalisar dattawan ya ce lamarin ya faru ne a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, bayan ayarinsa sun dauko shi daga filin jirgin saman Ibadan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng