Gwamnatin Sokoto Ta Fito da Bayanai kan Harin da Amurka Ta kai Jihar

Gwamnatin Sokoto Ta Fito da Bayanai kan Harin da Amurka Ta kai Jihar

  • Gwamnatin Sokoto ta tabbatar da harin da aka kai a wasu sassan ƙananan hukumomi tare da haɗin gwiwar sojojin Amurka da na Najeriya
  • Hadimin gwamna Ahmed Aliyu ya ce harin ya shafi yankin Jabo, kuma gwamnati ta ce babu fararen hula da suka mutu ko suka jikkata
  • A sakon da ta fitar, gwamnatin Sokoto ta yi kira ga jama’a da su ci gaba da ba da bayanan sirri domin samar da tsaro mai ɗorewa a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto – Gwamnatin Jihar Sokoto ta tabbatar da kai wani hari a wasu sassan jihar, harin da Amurka ta ce an kai shi ne kan mayaƙan ƙungiyar IS.

Gwamnatin ta ce harin ya gudana ne a daren Alhamis, 25 ga Disamban 2025, inda ta bayyana cewa an yi aikin ne ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin sojojin Amurka da na Najeriya domin dakile barazanar tsaro a yankin.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda daga ketare na 'shirin' kawo hari jihohin Arewa 4 a Najeriya

Shugaban Amurka da gwamnan jihar Sokoto
Gwamna Ahmed Aliyu na Sokoto da Donald Trump. Hoto: Sokoto State Government|The White House
Source: Facebook

BBC Hausa ta wallafa cewa bayanin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan rawar da haɗin gwiwar ƙasashen waje ke takawa wajen yaki da matsalolin tsaro a Arewa maso Yammacin Najeriya.

Bayanin gwamnatin Sokoto kan harin Amurka

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Sokoto, Abubakar Bawa, ya fitar, ya bayyana cewa har yanzu ba a kammala tantance cikakken sakamakon harin ba.

A cewarsa:

“Ba za iya tantance haƙiƙanin sakamakon harin ba a cikin ƙanƙanin lokaci, saboda har yanzu muna jiran cikakken rahoton aiki na musamman.”

Sanarwar ta nuna cewa ana ci gaba da tattara bayanai daga hukumomin tsaro domin fahimtar abin da harin ya haifar, musamman dangane da wuraren da aka kai hari da kuma tasirin da ya yi.

Babu fararen hula da harin ya shafa

Gwamnatin jihar ta jaddada cewa harin da aka kai a yankin Jabo bai yi sanadin mutuwa ko jikkata fararen hula ba, lamarin da ta ce yana da matuƙar muhimmanci wajen kare rayukan al’umma.

Kara karanta wannan

Sharudan da Tinubu ya bayar kafin harin Amurka kan 'yan ta'adda a Sokoto

Legit ta rahoto cewa sanarwar ta bayyana cewa an yi duk wani tanadi na tsaro domin tabbatar da cewa ba a cutar da jama’a yayin aiwatar da aikin, tare da kula da dokoki da ƙa’idojin yaki da ta’addanci.

Wannan bayani ya zo ne bayan rade-radin da suka fara yawo a wasu sassan jihar game da yiwuwar samun asarar rayuka, abin da gwamnati ta musanta.

Matsayar gwamnati kan haɗin gwiwa

Gwamnatin Sokoto ta bayyana goyon bayanta ga duk wani aikin haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da wasu ƙasashe ko masu ruwa da tsaki, muddin manufarsa ita ce magance matsalolin tsaro da sauran laifuffuka a jihar.

A cewar sanarwar, irin wannan haɗin gwiwa na taimakawa wajen ƙarfafa jami’an tsaro da inganta dabarun da ake amfani da su wajen kare al’umma daga hare-hare.

Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu
Gwamnan jihar Sokoto yana wani jawabi. Hoto: Ahmed Aliyu
Source: Twitter

Gwamnatin jihar ta yi kira ga mazauna yankunan da harin ya shafa da su ci gaba da ba da haɗin kai ga gwamnatocin tarayya da jiha, musamman ta hanyar fitar da bayanan sirri ga jami’an tsaro.

A nemi fadada harin Amurka a Arewa

A wani labarin, mun kawo muku cewa wani shugaba a jihar Benue ya bukaci dakarun Amurka su fadada hare-hare a Najeriya.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya aika sako ga Tinubu bayan harin Amurka a Sakkwato

Hakan na zuwa ne bayan wani hari da sojojin Amurka suka kai Arewa maso Yamma bisa umarnin shugaba Donald Trump.

Basaraken ya bukaci kai farmaki jihar Benue da wasu yankunan Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Gabas a wasikar da ya turawa Trump.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng