Amurka: An Jero Yankunan Arewa da Ake So Trump Ya kai Hari a Wata Wasika

Amurka: An Jero Yankunan Arewa da Ake So Trump Ya kai Hari a Wata Wasika

  • Shugaban Mzough U Tiv ya yaba wa Donald Trump kan fara hare-haren sama a yankin Arewa maso Yamma, yana mai cewa Benue ma na bukatar hakan
  • Sarkin ya bayyana cewa tsawon shekaru ana kashe manoma da lalata kauyuka a Benue, lamarin da ya tilasta wa dubban mutane barin muhallansu
  • Ya nemi a ci gaba da hare-haren tare da faɗaɗa su zuwa Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya domin dakile abin da ya kira kisan kiyashi a yankunan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Benue – Shugaban kungiyar Mzough U Tiv, Iorbee Ihagh, ya roƙi Shugaban Amurka Donald Trump da ya faɗaɗa hare-haren saman da aka fara a Arewa maso Yamma zuwa jihar Benue, domin kawo ƙarshen kashe-kashe.

Cif Ihagh ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a Makurdi, inda ya nuna farin cikinsa kan matakin da gwamnatin Amurka ta ɗauka.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Sokoto ta fito da bayanai kan harin da Amurka ta kai jihar

Shugaban Amurka da wasu jiragen kasar
Shugaba Donald Trump da wasu jiragen yaki. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Leadership ta wallafa cewa ya ce tsawon lokaci ana fama da hare-haren da suka shafi manoma da masu ibada a jihar, kuma hakan ya jefa yankin cikin wani hali na bala’i da rashin tsaro.

Cif Ihagh, wanda ya ce ya fito daga karamar hukumar Kwande, ya bayyana cewa sama da shekaru 16 al’ummarsu ke rayuwa cikin gudun hijira sakamakon hare-haren da ya alakanta da ‘yan bindiga.

Yankunan Arewa da ake so Trump ya kai hari

Cif Ihagh ya ce ya rubuta wasiƙa zuwa ga Shugaba Trump domin gode masa bisa matakin da ya ɗauka, tare da roƙon a turo dakarun Amurka zuwa Benue.

A cewarsa, an soke taron ibadar daren Kirsimeti a Makurdi sakamakon wata wasiƙar barazana da aka ce ‘yan bindiga suka aiko, inda aka takaita lokutan ibada zuwa tsakanin ƙarfe 4:30 na yamma zuwa 6:00 na yamma.

Taswirar jihar Benue
Taswirar jihar Benue a Arewa. Hoto: Legit
Source: Original

Daily Post ta rahoto ya roƙi a ci gaba da hare-haren cikin tsari mai ƙarfi tare da faɗaɗa su zuwa Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya, yana mai cewa Jihar Benue ta sha wahala sosai.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya aika sako ga Tinubu bayan harin Amurka a Sakkwato

Bincike ya nuna cewa jihohin Arewa ta Tsakiya sun hada da Benue, Kogi, Kwara, Nasarawa, Niger da Plateau sai kuma birnin tarayya Abuja.

A daya bangaren, yankin Arewa Maso Gabas kuma ya hada da jihohin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe. Yankin da ya yi fama da rikicin Boko Haram tsawon shekaru.

Amurka ta kawo hari Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Amurka ta bayyana cewa ta kai hari Arewacin Najeriya a daren Kirsimeti na 25 da Disambann 2025.

Shugaban Amurka, Donald Trump ne ya bayyana haka, inda ya yi ikirarin cewa sun kashe 'yan ta'adda da dama a farmakin da suka kai cikin dare.

Wannan ne karon farko da Amurka ta kai hari Najeriya tun bayan da aka fara maganar zargin kashe Kiristoci a kasar a kwanakin baya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng