‘Yan Ta’adda daga Ketare na ’Shirin’ Kawo Hari Jihohin Arewa 4 a Najeriya

‘Yan Ta’adda daga Ketare na ’Shirin’ Kawo Hari Jihohin Arewa 4 a Najeriya

  • Majiyoyin sojoji sun tabbatar da cewa an samu nasara bayan hare-haren Amurka a Arewa maso Yamma bayan haɗin gwiwa da sojojin Najeriya
  • Bayanai sun nuna cewa ’yan ta’adda daga Mali da Burkina Faso sun kutsa Najeriya, suna shirin kai hare-hare a jihohin Arewa hudu
  • Hakan ya sanya fargaba a zukatan al'ummar yankin dama kasa baki daya yayin da Arewacin Najeriya ke fama da matsalolin tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Majiyoyin manyan sojojin Najeriya sun tabbatar kai hare-haren da sojojin ruwan Amurka suka kai kan ’yan ta’adda a jihar Sokoto.

An gudanar da aikin ne tsakanin sojojin Amurka tare da haɗin gwiwar sojojin Najeriya domin ci gaba da kakkabe yan ta'adda.

Ana fargabar yan ta'adda za su kawo hari Najeriya daga ketare
Hafsan sojoji, Laftanar-janar Waidi Shaibu da dakarun soji. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Wata majiya ta shaida wa Vanguard cewa an gudanar da aikin ne da hadin guiwa sojojin kasashen guda biyu a Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

Sharudan da Tinubu ya bayar kafin harin Amurka kan 'yan ta'adda a Sokoto

Majiyar ta ce:

“Aiki ne na haɗin gwiwa da sojojin Amurka. Mu ne muka ba da bayanan wuraren hari, su kuma suka kai farmakin. A yanzu haka muna aikin tsabtace yankin.”

Fargabar kawo hari Najeriya daga ketare

Rahotanni sun nuna cewa kafin kai harin, bayanan sirri sun tabbatar da taruwar ’yan ta’adda da ’yan bindiga masu yawa daga yankunan Mali da Burkina Faso, suna shigowa Najeriya ta hanyoyin daban-daban.

An ce ƙungiyoyin sun yi shirin kai hare-hare a jihohin Sokoto, Zamfara, Niger da Katsina, domin tayar da zaune-tsaye a lokacin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara, cewar TheNigeriaLawyer.

Ƙungiyoyin ISIS da aka kai wa hari sun haɗa da Lakurawa da Jenni, waɗanda bayanan sirri suka nuna suna tara mayaƙa daga Mali da Burkina Faso domin kai hare-hare a Najeriya.

Ana jita-jitar kawo hari wasu jihohin Arewa daga ketare
Ministan tsaro a Najeriya, Christopher Musa. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Dabarun da aka bi wurin farmakar yan ta'adda

Bayanan da Pentagon ta fitar sun nuna cewa an harba aƙalla makami mai linzami na Tomahawk daga jirgin ruwan yaƙin Amurka a tekun duniya kusa da Ghana, a matsayin wani ɓangare na aikin.

Kara karanta wannan

Rawar da sojojin Najeriya suka taka yayin harin Amurka a Sokoto

Haka kuma, an yi amfani da jiragen leƙen asiri marasa matuƙa (drones) masu nisan zango domin gano wuraren da rage yiwuwar cutar da fararen hula.

Da aka tambayi batun yiwuwar asarar rayukan fararen hula, majiyoyin soji sun ce an tsara aikin cikin tsanaki, inda aka kai hari ne kawai kan ’yan ta’adda da wuraren ajiyar kayan aikinsu.

A cewar su, an tanadi ingantattun hanyoyin sa ido domin tabbatar da cewa babu wanda ba shi da laifi da aka shafa a harin.

Yadda Tinubu ya ba Amurka izinin kai hari

An ji cewa Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya tabbatar da cewa Shugaba Bola Tinubu ya amince da hare-haren Amrurka a Sokoto.

Ambasada Tuggar ya ce Najeriya ce ta bayar da bayanan sirri ga Amurka, kuma an yi aikin ne tare, ba tare da take yancin ƙasar ba.

Gwamnatin tarayya ta jaddada cewa hare-haren ba su da alaƙa da addini, illa yaki da ta’addanci da kare rayuka da dukiyoyi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.