Sakon Gwamnatin Amurka ga Najeriya bayan Harin Bam a Sokoto
- Gwamnatin Amurka ta bakin ministan tsaro ta yi magana kan kokarin Najeriya game da harin da aka kawo jihar Sokoto
- Ministan tsaron Amurka Pete Hegseth ya gode wa gwamnatin Najeriya bisa hadin kai yayin hare-haren sama da aka kai kan ’yan ta’adda
- Amurka ta ce harin ya biyo bayan gargadin Donald Trump kan kisan fararen hula, inda ta jaddada cewa ma’aikatar tsaro a shirye take koyaushe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Sokoto - Ministan tsaro a Amurka, Pete Hegseth, ya fadi rawar da Najeriya ta taka game da harin bam a jihar Sokoto.
Hegseth ya bayyana godiya ga gwamnatin Najeriya bisa goyon bayan da ta bayar yayin ragargazar sansanonin ’yan ta’adda a Sokoto.

Source: Facebook
Amurka ta godewa Najeriya bayan harin Sokoto
Legit Hausa ta samu wannan bayani ne daga shafin ministan na X da aka fi sani Twitter a yau Juma'a 26 ga watan Disambar 2025.
Hakan ya biyo bayan kaddamar da wani gagarumin hari da sojojin Amurka suka yi kan ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.
Hegseth ya bayyana hakan ne bayan ganawa da tawagar Najeriya a Amurka, bayan Shugaba Donald Trump ya sanya Najeriya cikin jerin kasashen da suke da matsala.
Ya ce:
“Shugaban kasa ya fayyace cewa dole ne a dakatar da kisan Kiristoci marasa laifi a Najeriya da sauran wurare.
“Ma'aikatar yaki a Amurka a koyaushe tana cikin shiri, don haka ISIS sun gano hakan a daren yau, a ranar Kirsimeti. Akwai sauran abubuwa masu zuwa…
Muna matuƙar godiya ga goyon baya da haɗin kai da gwamnatin Najeriya ta bayar.”
Hegseth ya kara da cewa ma’aikatar tsaron Amurka tana shirye koyaushe, yana mai cewa ISIS sun dandana karfin dakarunsu a daren Kirsimeti.

Source: Getty Images
Abin da gwamnatin Najeriya ta ce
A wata sanarwa da ta fitar, Ma’aikatar Harkokin Waje ta Najeriya ta ce hare-haren sama na daga cikin yunkurin dakile ta’addanci da tsattsauran ra’ayi.
Mai magana da yawun ma’aikatar, Kimiebi Ebienfa, ya ce an dauki matakin ne domin kare rayukan jama’a da tabbatar da tsaro.
Sanarwar ta ce hadin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka na kunshe da musayar bayanan sirri da tsare-tsare bisa mutunta dokokin kasa da kasa.
Gwamnatin tarayya ta jaddada cewa duk wani yaki da ta’addanci ana gudanar da shi ne domin kare fararen hula ba tare da la’akari da addini ko kabila ba.
Harin Amurka ya rikita 'yan Sokoto
Mun ba ku labarin irin halin da wasu mazauna yankin da Amurka ta kai harin bam a jihar Sokoto a jiya Alhamis 25 ga watan Disambar 2025 ke ciki.
Hakan na zuwa ne bayan Amurka ta tabbatar da kai wani hari kan yan ta'adda a karamar hukumar Tambuwal a jihar.
Mazauna kauyen Jabo a Tambuwal da ke jihar sun shiga tsananin fargaba bayan Amurka ta kai harin bama-bamai da ya tayar musu da hankali.
Asali: Legit.ng

