Halin da Mazauna Kauyen Sokoto Ke ciki a Yanzu bayan Harin Amurka
- Kasar Amurka ta tabbatar da kai wani hari kan yan ta'adda a jihar Sokoto a daren jiya Alhamis 25 ga watan Disambar 2025
- Mazauna kauyen Jabo a Tambuwal a jihar Sokoto sun shiga tsananin fargaba bayan Amurka ta kai harin bama-bamai
- Wani ganau ya ce karar fashewar makaman ta girgiza gidaje, yayin da jami’an tsaro suka garzaya wurin da abin ya watse
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Jabo, Sokoto - Wasu mazauna garin Jabo a karamar hukumar Tambuwal ta jihar Sokoto sun magantu bayan harin Amurka.
Mazauna yankin sun shiga firgici a daren Alhamis 25 ga watan Disambar 2025 bayan bama-bamai sun fado yayin harin Amurka kan ’yan ta’adda.

Source: Getty Images
Amurka ta kai hari a kauyen Sokoto
Kasar Amurka ta kanta ta tabbatar da kai harin a Sokoto a kokarin kakkabe yan ta'adda wanda ma'aikatar yakin Amurka ta wallafa a X.
Lamarin ya faru da misalin karfe 9:30 na dare, inda karar fashewar ta girgiza gine-gine kafin bama-baman su fadi kasa, su tashi da wuta a wajen gari.
Wani ganau, Attahiru Madawaki Jabo, ya ce:
“Ina gida lokacin da muka ji ƙarar da ta fito daga wani wuri, wanda ya girgiza gidajenmu sosai.”
Majiyoyi sun ce sojojin da ke wani sansani kusa da wurin sun isa nan take, suka killace yankin, suka tattara sassan na’urar domin ci gaba da bincike.
Shugaban Amurka, Donald Trump ya tabbatar da harin, yana cewa an kashe ’yan ta’adda da dama, tare da alakanta lamarin da Ma’aikatar Yakin Amurka.

Source: Original
Yadda mazauna yankin Sokoto suka bar gidajensu
Rahoton Daily Trust ya ce makamin da ya fashe ya tilasta wa mazauna yankin barin gidajensu cikin firgici.
Lamarin, wanda ya tayar da hankula a yankin, ya faru ne da misalin karfe 9:30 na dare, kamar yadda shaidu suka bayyana.
Jihar Sokoto na daga cikin jihohin da ke yankin Arewa maso Yamma da ke fama da matsalolin tsaro da suka shafi garkuwa da mutane da kashe-kashe.
Wasu mazauna yankin sun shaida wa yan jaridu cewa na’urar ta kama da wuta ne bayan ta fado kasa.
A cewar majiyoyin yankin, sojojin da ke bakin wani shingen bincike a kusa da wurin sun garzaya wurin nan take, suka kewaye yankin.
Wasu daga cikin mazauna yankin sun ki komawa gidajensu saboda tsoron sake fashewar wata na’ura, cewar Punch.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga hukumomin gwamnati kan lamarin.
Martanin Najeriya bayan harin Amurka a Sokoto
Mun ba ku labarin cewa kasar Najeriya ta ce za ta ci gaba da haɗa kai da kasar Amurka domin kakkabe yan ta'adda da inganta tsaro.
Gwamnatin kasar ta tabbatar da cewa matakin zai hada da musayar bayanan sirri kan yaki da ta’addanci don kare rayukan al'ummar kasa.
Wannan bayani ya biyo bayan hare-haren sama na musamman kan wuraren ‘yan ta’adda a Arewa maso Yammacin kasar da Amurka ta yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


