Abin da Gwamnatin Najeriya Ta Ce game da Harin Amurka a Sakkwato

Abin da Gwamnatin Najeriya Ta Ce game da Harin Amurka a Sakkwato

  • Najeriya ta ce tana ci gaba da haɗa kai da kasar Amurka domin inganta tsaro da musayar bayanan sirri kan yaki da ta’addanci don kare rayuka
  • Wannan bayani ya biyo bayan hare-haren sama na musamman kan wuraren ‘yan ta’adda a Arewa maso Yammacin kasar da Amurka ta yi
  • Gwamnati ta ce kare rayukan fararen hula shi ne ginshikin duk wani matakin tsaro kuma ba za ta yi ƙasa a gwiwa game da haka ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Gwamnatin Najeriya tabbatar da cewa tana ci gaba da hadin gwiwa ta fuskar tsaro da musayar bayanan sirri da kasashen duniya, ciki har da Amurka, domin dakile barazanar ta’addanci.

Ma’aikatar Harkokin Waje ta Najeriya, ta yi bayani cewa hadin gwiwar ya kai ga kai wasu hare-haren sama kan wuraren ‘yan ta’adda a yankin arewa maso yammacin kasar.

Kara karanta wannan

Sojojin Amurka sun kawo hari Najeriya don 'kare rayukan kiristoci '

Najeriya ta ce ita ta sahale harin Amurka a kasar
Donald Trump Shugaban Amurka, Bola Tinubu Shugaban Najeriya Hoto: Donald J Trump/Bayo Onanuga
Source: Getty Images

Ma'aikatar ta tabbatar da cewa da yawunta sojojin Amurka suka kai harin jihar Sakkwato, kamar yadda gwamnatin Najeriya ta wallafa a shafin X.

Najeriya na aiki tare da kasar Amurka

A cewar ma’aikatar, hadin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da kasashe abokan hulda yana tafiya ne bisa ka’idojin kasa da kasa da yarjejeniyoyin bangarori biyu.

Hakan ya hada da musayar bayanan sirri, tsara dabarun tsaro tare, da bayar da tallafin da ya dace da dokokin kasa da kasa, tare da mutunta ikon kasa da kasa da martaba juna.

Gwamnati ta jaddada cewa wannan tsari yana nuna kudurin Najeriya na yin aiki tare da abokan hulda domin yakar barazanar ‘yan ta’adda, musamman a yankunan da ke fama da hare-haren masu tayar da kayar baya.

Gwamnati ta magantu kan kare rayuka

Ma’aikatar ta ce duk wani mataki da ake dauka a karkashin wannan hadin gwiwa yana la’akari da bukatar tabbatar da zaman lafiya a yankin da duniya baki daya, tare da kauce wa duk wani abu da zai karya dokokin kasa da kasa.

Kara karanta wannan

Gwamna Aliyu ya kaddamar da sababbin dabaru na kawo karshen ƴan bindiga a Sokoto

Najeriya ta sake nanata cewa dukkanin matakan yaki da ta’addanci suna karkashin ka’idar kare rayukan fararen hula.

Gwamnatin kasar ta kuma tabbatar da aikin hadin kan kasa, da kuma mutunta hakkin ‘yan kasa, ba tare da la’akari da addini ko kabila ba.

Shugaban Amurka ya ba da umarnin kawo hari Najeriya
Shugaban kasar Amurka Donald Trump Hoto: Donald J Trump
Source: Getty Images

Gwamnatin ta bayyana cewa duk wani nau’i na ta’addanci, ko da an nufa Kiristoci ne, Musulmi, ko wata al’umma, abin Allah-wadai ne kuma barazana ce ga kimar Najeriya. Har ila yau, gwamnatin tarayya ta ce tana aiki kafada da kafada da abokan hulda ta hanyoyin diflomasiyya da tsaro domin raunana kungiyoyin ‘yan ta’adda, katse hanyoyin samun kuɗinsu da kayan aiki. Ma’aikatar Harkokin Waje ta ce za ta ci gaba da tuntubar dukkanin abokan hulda da abin ya shafa, tare da sanar da ‘yan kasa halin da ake ciki ta hanyoyin hukuma da suka dace.

Amurka ta kawo hari a Arewacin Najeriya

A baya, mun wallafa cewa gwamnatin Amurka ta sanar da kaddamar da hare-haren sama kan wasu wuraren da ake zargin ‘yan ta’addar ISIS suna amfani da su a Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

ICPC ta jero ma'aikatun da aka fi tsammanin badakala a Najeriya a 2025

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce shi da kansa ya bayar da umarnin kai hare-haren, yana mai bayyana su a matsayin masu karfi da kuma barazana ga ‘yan ta’adda.

Rahotanni sun ce wannan shi ne karo na farko da sojojin Amurka suka kai irin wannan hari a Najeriya tun bayan da Donald Trump ya sake komawa kan karagar mulki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng