Gwamna Aliyu Ya Kaddamar da Sababbin Dabaru na Kawo Karshen Ƴan Bindiga a Sokoto

Gwamna Aliyu Ya Kaddamar da Sababbin Dabaru na Kawo Karshen Ƴan Bindiga a Sokoto

  • Gwamna Ahmad Aliyu ya sanar da sababbin hanyoyin yaki da 'yan bindiga domin maido da zaman lafiya a yankunan karkara na Sokoto
  • Ya bukaci mazauna jihar su ci gaba da taimaka wa hukumomin tsaro da sahihan bayanan sirri domin gano maboyar masu aikata laifuffuka
  • Gwamnatin jihar ta sake jaddada kudurin tallafa wa jami'an tsaro da kayan aiki a kananan hukumomi 13 da hare-hare suka fi shafa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sokoto - Gwamnan Sokoto, Ahmad Aliyu, ya ƙaddamar da sababbin tsare-tsare domin ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ‘yan bindiga, yana mai cewa gwamnatinsa ta kuduri aniyar ganin an kawar da matsalar gaba ɗaya.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake buɗe taron majalisar zartarwa ta jiha karo na 17, wanda aka bayyana a matsayin zaman majalisa na ƙarshe na shekarar 2025, a Sokoto.

Kara karanta wannan

Tsohon sanata ya samu mukami da shugaban jam'iyyar APC ya nada hadimai 15

Gwamna Ahmed Aliyu ya kawo dabarun yaki da 'yan bindiga a Sokoto
Gwamna Ahmed Aliyu a taron majalisar zartarwar jihar Sokoto. Hoto: @Ahmedaliyuskt
Source: Facebook

Sokoto: An kaddabar da dabarun yaki da 'yan bindiga

‘Yan bindiga sun dade suna haddasa rashin tsaro a yankunan karkarar jihar Sokoto, inda ake fuskantar hare-haren ta’addanci, a cewar rahoton Punch.

Rahoton ya ce 'yan ta'addar sun raba jama’a da muhallansu, suna satar shanu, garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa, da kuma jawo durƙushewar harkokin tattalin arziki.

Gwamna Ahmed Aliyu ya ce sababbin matakan, da ke cike gibin ƙoƙarin tsaro da ake yi a halin yanzu, an tsara su ne domin ƙarfafa tattara bayanan sirri da inganta haɗin gwiwa da hukumomin tsaro.

A cewarsa, tun bayan hawansa mulki, gwamnatinsa ke ci gaba da tallafa wa hukumomin tsaro da kayan aiki da sauran muhimman abubuwa domin ƙara musu ƙarfi wajen aiwatar da ayyukansu a dukkan kananan hukumomi 13 da matsalar ‘yan bindiga ta shafa.

Gwamna ya nemi taimakon al'ummar Sokoto

Gwamna Ahmed Aliyu ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da marawa ƙoƙarin gwamnati baya tare da haɗa kai da jami’an tsaro ta hanyar bayar da sahihan bayanai cikin lokaci.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An gano mutanen da 'yan bindiga ke amfani da su wajen karbar kudi a Najeriya

Ya ce:

“Mu a matsayinmu na gwamnati, a shirye muke mu yi duk abin da ya dace domin ganin ‘yan bindiga sun zama tarihi a jihar Sokoto, amma ba za mu iya yin hakan mu kaɗai ba."

Gwamnan ya yaba wa mambobin Majalisar Zartarwa ta Jiha bisa jajircewarsu, yana mai danganta nasarorin da gwamnatinsa ta samu zuwa yanzu da goyon bayansu da haɗin kai.

Gwamna Ahmad ya roki taimakon al'ummar Sokoto don yaki da 'yan bindiga
Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya na magana da manema labarai. Hoto: @Ahmedaliyuskt
Source: Twitter

An yi sababbin nade nade a gwamnatin Sokoto

Haka kuma, ya gode wa al’ummar jihar bisa addu’o’insu da haɗin kai, tare da tabbatar musu da ƙarin amfanin dimokuraɗiyya, in ji rahoton Tribune.

Gwamna Ahmed Aliyu ya yi amfani da damar wajen taya sabon shugaban ma’aikata, Abdulkadir Ahmed Mohamed, da babban mataimaki na musamman kan harkokin majalisa, Bande Rika, murna.

Ya bukaci sababbin jami'an gwamnatin da su ba da gudunmawa mai ma’ana wajen cimma burin Ajandar Smart Innovative na gwamnatinsa don ci gaban jihar Sokoto.

'Yan bindiga sun buga ta'asa a Sokoto

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida ya ba wa gwamnonin Arewa mafita game da matsalar tsaro

A wani labari, mun ruwaito cewa, ’yan bindiga dauke da makamai sun kai hari kauyen Kurawa da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.

Wasu majiyoyi sun ce 'yan bindigan sun kashe mutum biyu tare da yin garkuwa da mutane 15, ciki har da wasu mata huɗu masu shayarwa da jariransu.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, ɗan majalisar da ke wakiltar yankin, Hon. Sa’idu Ibrahim, ya ce mutum 15 ne maharan suka tafi da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com