Sanata Barau Ya Yi Alhinin Rasuwar 'Yan Majalisar Dokoki 2 a Jihar Kano

Sanata Barau Ya Yi Alhinin Rasuwar 'Yan Majalisar Dokoki 2 a Jihar Kano

  • Sanata Barau I.Jibrin ya yi matukarjimami tate da mika sakon ta'aziyya bisa rasuwar yan majalisar dokokin jihar Kano guda biyu ranar Laraba
  • Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya ce wannan babban rashi ne ga al'ummar mazabun 'yan Majalisar da kuma gwamnatin Kano
  • Barau ya yi addu'ar Allah Ya gafarta masu kura-kuransu, Ya bai wa iyalansu hakuri da juriyar wannan babban rashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya bi sahun masu tura sakon ta'aziyya bisa rasuwar mambobi biyu na Majalisar dokokin jihar Kano.

Sanata Barau ya nuna matukar alhininsa kan rasuwar ‘yan Majalisar Dokokin Jihar Kano guda biyu cikin sa'a guda a ranar Laraba.

Sanata Barau I Jibrin.
Mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin Hoto: Barau I. Jibrin
Source: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa ‘yan majalisar da suka rasu sun haɗa da Aminu Sa’ad Ungogo, mai wakiltar ƙaramar hukumar Ungogo, da kuma Sarki Aliyu Daneji, wakilin Kano Municipal a Majalisar Dokokin Jihar Kano.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: 'Yan majalisar dokoki 2 sun mutu kusan lokaci guda a jihar Kano

Sanata Barau ya mika sakon ta'aziyya

A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Ismail Mudashir, ya fitar, Sanata Barau ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, jama'an mazabunsu da kuma gwamnatin Jihar Kano.

Barau ya ce,

“Cikin alhini nake miƙa ta’aziyyata ga iyalan ‘yan majalisa, al’ummar mazabunsu da kuma Gwamnatin Jihar Kano."

Barau Jibrin ya yiwa mamatan addu'a

Mataimakin shugaban Majalisar Dattawan ya kuma yi addu'ar Allah Ya gafarta wa mamatan, ya kuma sanya su a cikin gidan Aljannah.

“Ina roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta musu kura-kuransu, Ya sanya su cikin Aljannatul Firdaus, sannan Ya bai wa iyalansu da masoyansu haƙurin jure wannan babban rashi da ba za a iya misalta shi ba,” in ji sanarwar.

An ruwaito cewa an sanar da rasuwar Hon. Sarki Aliyu Daneji kasa da awa guda bayan mutuwar Aminu Hon Sa’ad Ungogo, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Kasafi na Majalisar Dokokin Jihar Kano.

Rasuwar yan majalisa 2 ta girgiza Kano

Kara karanta wannan

Sanata ya hango abin da zai wargaza APC duk da yawan sauya shekar 'yan adawa

Wannan lamari ya girgiza mutanen Kano musamman jama'ar mazabunnUngoggo da karamar hukumar birni da kewaye, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Wasu rahotanni sun nuna cewa Marigayi Hon.Ungogo, ɗan jam’iyyar NNPP, ya rasu ne bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.

Yan Majalisar Kano.
Yan Majalisar dokokin Kani guda biyu, Hon. Aminu Sa'ad Ungoggo da Sarki Aliyu Daneji Hoto: Kamal Karaye
Source: Twitter

Rahotanni sun nuna cewa ya halarci Majalisar Dokokin Jihar Kano a safiyar yau Laraba da ya rasu, inda ya shiga taron kwamitinsa, kafin daga bisani rai ya yi halinsa.

Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa wannan babban rashi ne, tare da rokon Allah Ya ba iyalan mamatan hakuri.

Tsohon wakilin Najeriya a UN ya rasu

A wani rahoton, kun ji cewa fitaccen ɗan diflomasiyyar Najeriya da ya wakilci kasar a Majalisar Dinkin Duniya (UN), Cif Christopher Mbanefo, ya rasu.

Marigayi Mbanefo, wanda ƙwararren akawu ne kuma masani a fannin ilimi, ya rasu yana da shekaru 95 a duniya.

An bayyana marigayi Mbanefo a matsayin mutum mai taimakon jama’a, musamman a fannin ilimi, inda ya kafa cibiyar Arthur Mbanefo Digital Research Center a Jami’ar Lagos.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262