'Yan Sanda Sun Fitar da Bayanai kan Harin Bam a Masallacin Maiduguri

'Yan Sanda Sun Fitar da Bayanai kan Harin Bam a Masallacin Maiduguri

  • An shiga jimami a jihar Borno bayan wani dan kunar bakin wake ya tayar da bam ana tsaka da Sallah a wani masallaci da ke birnin Maiduguri
  • Rundunar 'yan sandan jihar Borno ta bayyana matakan da ta auka bayan aukuwar lamarin da yammacin ranar Laraba, 24 ga watan Disamban 2025
  • Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan, DSP Nahum Daso, ya bayyana cewa mutane biyar sun mutu nan take sakamakon fashewar bam din

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Rundunar ’yan sanda a jihar Borno ta yi magana kan harin bam da wani dan kunar bakin wake ya kai a birnin Maiduguri.

Rundunar 'yan sandan ta tabbatar da mutuwar mutane biyar tare da jikkatar wasu 35 sakamakon fashewar bam da ta auku a ranar Laraba, 24 ga watan Disamban 2025 a wani masallaci da ke Maiduguri.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Bam ya tashi da mutane a masallaci ana sallar Magarib a Maiduguri

Bam ya tarwatse a jihar Borno
Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun Hoto: @PoliceNG
Source: Facebook

Bam ya fashe a masallacin Maiduguri

Jaridar Vanguard ta ce jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sanda ta jihar Borno, DSP Nahum Daso, ya tabbatar da hakan yayin wata hira da manema labarai a Maiduguri.

Lamarin ya faru ne sakamakon harin bam da ake zargin dan kunar bakin wake ne ya kai a yankin Gamborun na birnin Maiduguri.

Me 'yan sanda suka ce kan fashewar bam?

A cewar mai magana da yawun 'yan sandan, wanda ake zargin dan kunar bakin waken ne, ya tayar da abin fashewar ne da misalin karfe 6:15 na yamma yayin da ake sallar jam’i a yankin Gamborun.

Ya ce mutane biyar sun mutu nan take, yayin da mutane 35 suka jikkata, inda wasu daga cikinsu suka samu munanan raunuka.

DSP Nahum Daso ya kara da cewa an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri (UMTH) domin samun kulawa cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Tanka makare da fetur ta tarwatse a tsakiyar gidan mai a Bauchi

'Yan sanda sun dauki matakai

Ya bayyana cewa jami’an sashin lalata bama-bamai (EOD) tare da sauran hukumomin tsaro sun isa wajen da lamarin ya faru domin tsare yankin, gudanar da bincike, da tabbatar da cewa babu wata bam na biyu da aka dasa.

Dan kunar bakin wake ya tayar da bam a Maiduguri
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Hakazalika, ya ce an kebe yankin gaba ɗaya, yayin da hukumomin tsaro suka fara bincike kan musabbabin harin.

Sai dai kakakin rundunar ya yi kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu su kuma kasance masu taka-tsantsan, tare da gaggauta sanar da jami’an tsaro mafi kusa idan suka ga wani mutum, motsi ko abu da ke da alamun shakku.

Bam ya kashe sojoji a Borno

A wani labarin kuma, kun ji cewa an rasa rayukan sojoji a jihar Borno bayan wani dan kunar bakin wake ya tayar da bam a yankin Pulka.

Ana dai zargin dan kunar bakin waken na daga cikin ‘yan kungiyar Boko Haram, kuma ya fito ne daga maboyarsu da ke tsaunukan Mandara, kusa da iyakar Najeriya da Kamaru.

Bayanan da aka samu sun nuna cewa dan ta’addan ya yi basaja da zama matafiyi, inda ya karaso kusa da sojojin da ke bakin aiki kafin ya tayar da bam din da ke jikinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng