'Yan Arewa Mazauna Legas Sun Yi Kuka bayan Rushe Gidaje 5000 a Mile 12
- Wasu mutanen Arewa dake Legas sun nemi agaji bayan rushe gidaje sama da 5,000 a Mile 12 da gwamnatin jihar ta yi babu sanarwa
- Dubunnan iyalai sun rasa matsuguni, abinci da hanyoyin samun kudin shiga a lokacin da gwamnatin Babajide Sanwo-Olu ta masu rusau
- Shugaban Kungiyar Hausawa mazauna Legas, Abdullahi A.A Fulani ya bayyana wahalar da 'yan Arewa suka fada bayan rushe gidajensu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos – Shugaban Kungiyar al'ummar Arewacin Najeriya mazauna Jihar Legas, Alhaji Abdullahi A.A Fulani, ya ce jama'arsu na cikin tashin hankali.
Ya fito neman dauki daga gwamnatin tarayya, shugabannin Arewa da kuma masu hannu da shuni, bayan rushe-rushen da gwamnatin Jihar Legas ta gudanar.

Source: Facebook
Jaridar Aminiya ta wallafa cewa gwamnatin Legas ta yi rusau a unguwar Mile 12. A cewarsa, aikin ya shafi gidaje, masallatai da makarantu da dama mallakin Hausawa.
Hausawan Legas sun shiga wahala
A cewar Abdullahi A A Fulani, rasau da aka yi wa ƴan Arewa a Legas ya girgiza rayuwar mutanensu da ke zaune a yankin.
Ya bayyana cewa ba rushe gidaje kadai aka yi ba, har da rusa hanyoyin dogaro da kai da iyalai ke amfani da su wajen ciyar da kansu.
Ya ce:
"An katse mana rayuwa lokaci guda. Iyaye sun rasa sana’o’insu, yara kuma sun rasa wurin kwana da makaranta.”
Shugaban ya kuma roki kafafen yada labarai, lauyoyi da kungiyoyin kare hakkin dan Adam da su taimaka wajen ganin an ji muryar wadanda abin ya shafa.
'Yan Arewa a Legas sun nemi ɗauki

Kara karanta wannan
Zargin badakalar N4.6bn: EFCC ta shirya fara shari'a da Kwamishinan kudi a Bauchi
Abdullahi A.A Fulani ya ce a bi masu hakkinsu sannan a sama masu kayan jin don ya taimaka wajen rage radadin da jama’a ke ciki, tare da tabbatar da adalci da mutunta hakkin dan Adam.
A makon da ya gabata ne ruguje gine-ginen da gwamnatin jihar ta gudanar ya jefa dubban mazauna Mile 12 cikin kunci.

Source: Getty Images
Yawancin wadanda abin ya shafa ‘yan Arewa ne da suka shafe shekaru suna zaune a jihar Legas, inda aka rushe sama da gidaje 5,000.
Lamarin ya tilasta wa fiye da mutane 10,000 kwana a kan titi tare da kayansu, ba tare da matsuguni ba yayin da suka rasa inda za su saka ransu.
Ya kara da cewa mata da yara sun fi fuskantar wahala, musamman ganin barazanar rashin tsaro da yaduwar cututtuka iri-iri.
An yi wa 'yan Arewa rusau a Legas
A wani labarin, mun wallafa cewa dubunan ’yan kasuwa a jihar Legas sun shiga mawuyacin hali bayan da gwamnatin jihar ta rushe kasuwar Costain da ke birnin Lagos, lamarin da ya haddasa asarar dukiya.
Rahotanni sun nuna cewa rusau din ya gudana ne ranar Alhamis, 23 ga watan Oktoba, 2025, a yayin da jami’an gwamnati suka aiwatar da aikin da suka ce domin tsaftace muhalli da inganta tsari a yankin.
Shaidun gani da ido sun ce jami’an sun zo da manyan injinan tono tare da ’yan sanda, inda suka tarwatsa jama’a ta hanyar amfani da hayaki mai sa hawaye kafin su fara rushe shaguna da gine-gine.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

