Manyan Matakai 8 da Gwamnatin Tinubu Ta Dauka kuma Suka Ja Hankalin 'Yan Najeriya a 2025

Manyan Matakai 8 da Gwamnatin Tinubu Ta Dauka kuma Suka Ja Hankalin 'Yan Najeriya a 2025

Abuja, Nigeria - A shekarar 2025, gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta dauki matakai da dama da suka ja hankali kuma suka haddasa ce-ce-ku-ce.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kama daga ayyana dokar ta-baci da gyare-gyare a bangarori daban-daban kamar tsaro, wannan shekara cike take da matakai masu tsauri da kuma wadanda aka yi da nufin kawo ci gaba.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnatin Najeriya Hoto: @OfficialABAT
Source: Twitter

Jaridar Punch ta tattaro cewa wasu daga cikin shawarwarin da gwamnatin Tinubu ta yanke a 2025 sun haifar da ce-ce-ku-ce, wasu kuma sun kara wa mutane gwarin gwiwa.

Bisa haka ne muka tattaro muku manyan matakan da gwamnatin tarayya ta dauka a 2025, wadanda suka ja hankalin 'yan Najeriya. Ga su kamar haka:

1. Ayyana dokar ta-baci a jihar Ribas

A watan Maris, 2025, Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a Jihar Ribas, inda ya dakatar da gwamna, mataimakin gwamna da dukkan 'yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida.

Kara karanta wannan

Harin Amurka: Ndume ya roƙi Tinubu da Donald Trump game da yaƙi da ta'addanci

A sanarwar da fadar shugaban kasa ta wallafa shafinta na yanar gizo, ta ce matakin ya biyo bayan dogon rikicin siyasa a Ribas, wanda ya kai ga Gwamna Sim Fubara ya rusa majalisar dokokin jihar.

Masana sun danganta wani bangare na rikicin da sabanin da ya shiga tsakanin tsohon gwamnan Ribas kuma ministan Abuja, Nyesom Wike da Gwamna Siminalayi Fubara.

A ƙarƙashin dokar ta-ɓaci, shugaban kasa ya naɗa Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe (mai ritaya) a matsayin shugaban riko a jihar Ribas.

Shugaba Tinubu da Gwamna Fubara.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu tare da Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas Hoto: @SimFubara
Source: Facebook

Gwamnatin tarayya ta ce wannan mataki da aka dauka ya zama dole domin dawo da tsarin doka ada oda da kuma kare kadarorin mai masu mahimmanci.

Duk da cewa an ɗage dokar ta-ɓacin bayan watanni shida kuma aka sake dawo da zaɓaɓɓun jami'ai, lamarin ya ja hankalin mutane, inda wasu suka nuna shakku kan dalilin daukar wannan mataki.

2. Karin kudin fasfo a Najeriya

A watan Agusta, 2025, Hukumar Shige da Fice ta Najeriya (NIS) ta sanar da karin farashin kudin fasfo na shekara biyar daga N50,000 zuwa N100,000 da fasfo na shekara 10 daga N100,000 zuwa N200,000.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta fadi ainihin dajin da bama baman Amurka suka sauka a Najeriya

Hukumar NIS ta bayyana cewa ta yi wannan kari ne domin inganta harkokin yin fasfo din da kuma kawo karshen dogon jinkirin da ake samu, karin ya fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Satumba, 2025.

Olubunmi Tunji-Ojo
Ministan harkokin cikin gida na Najeriya, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo Hoto: @tunjiojo
Source: Facebook

Ministan harkokin cikin gida Olubunmi Tunji-Ojo ya ce hakan zai ba mutane damar samun fasfo cikin mako guda, wanda ake ganin ci gaba ne idan aka kwatanta da jinkirin da aka saba gani a baya, kamar yadda Bussiness Day ta kawo.

Duk da haka, 'yan Najeriya sun nuna takaicinsu yayin da suka bayyana matakin da na son rai kuma suka bukaci gwamnati da ta samar da keɓantaccen tallafi ga masu karamin karfi.

3. Sauya fasalin haraji

A watan Yunin 2025, shugaban kasa ya sanya hannu kan sababbin dokoki guda hudu na gyaran fasalin haraji a Najeriya

Waɗannan dokoki sun soke kuma sun gyara wasu tsofaffin dokokin haraji masu rudani da rikitarwa, sannan suka kafa sabuwar hukumar tattara kudaden shiga.

Gwamnatin tarayya ta ce ta dauki wannan matakin ne don gyara tsarin haraji, da rage sulalewar kudaden shiga da haramtacciyar hanya.

Vanguard ta ce wannan mataki dai ya haddasa rudani da ce-ce-ku-ce mai zafi tsakanin 'yan Najeriya musamman daga Arewa, sai dai duk da sukar da aka yi ta yi, gwamnati ta kafe kan bakarta.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima ya dauki zafi game da harin bam da aka kai masallacin Juma'a

Taiwo Oyedele.
Shugaban kwamitin sauya fasalin haraji na shugaban kasa, Taiwo Oyedele Hoto: @Taiwooyedele
Source: Twitter

Haka zalika, daga bisani an sake gano banbanci a dokokin haraji da Majalisa ta amince da su da wadanda gwamnatin tarayya ta fitar, lamarin da ya kara haifar ce-ce-ku-ce.

4. Ayyana dokar ta-baci kan tsaron kasa

A watan Nuwamba, yayin da matsalar tsaro ta tabarbarewa, gwamnati ta ayyana dokar ta baci a fannin tsaro a duk fadin kasar.

Shugaba Bola Tinubu ya bada umarnin daukar sababbin jami'an 'yan sanda 20,000 kuma ya ba da izinin tura dakarun gadin daji domin tunkarar kungiyoyin 'yan ta'adda da ke buya a jeji.

A rahoton Arise tv, shugaban kasar ya ce matakin ya zama dole don kare rayuka da kuma dakile ta'addanci kafin ya kara yaduwa, yana mai kira ga hukumomin tsaro da su kara tashi tsaye.

Wannan mataki ya nuna karuwar damuwa game da rashin tsaro a fadin kasar, wani babban batu da ke ci wa 'yan Najeriya tuwo a kwarya, kuma ya nuna za a shiga wani yanayin tsaro mai tsauri.

Kara karanta wannan

Atiku da NBA sun fadi hadarin da suka gani a dokar harajin Tinubu ta 2026

Shugaban kasa, Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a gidan gwamnatin Najeriya Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

5. Afuwa da sassauci ga masu laifi

A watan Oktoban 2025, Bola Tinubu ya yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi na jinƙai, ina ya yi wa mutane da dama afuwa tare da yiwa wasu sassauci a hukuncin da aka yanke masu.

A jimulla, shugaban kasa ya zakulo mutane 175 a karon farko, wanda ya hada da wadanda aka yafe wa gaba daya, canza hukunci, sassauci da wanke wasu daga laifi, cewar rahoton The Cable.

Wadanda aka yi wa afuwa sun hada da fursunonin da aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai, hukuncin kisa da wadanda da aka daure na tsawon lokaci bisa laififfuka daban-daban.

Wannan afuwa dai ta ja hankalin 'yan Najeriya, suka rika sukar matakin yafe wa wasu daga cikin mutanen, wanda a karshe gwamnarin tarayya ta sake nazari kan lamarin.

6. Batun afuwa ga Maryam Sanda

Kara karanta wannan

Babbar magana: An fara neman a tsige Bola Tinubu daga kujerar shugaban kasa

A watan Oktoban 2025, gwamnatin tarayya ta sanya sunan Maryam Sanda a cikin jerin wadanda za a yi wa afuwa.

An yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar ratayewa saboda kisan mijinta, Bilyaminu Bello, bayan wata sa-insa da ta shiga tsakaninsu a cikin gida a shekarar 2017.

Matakin dai ya fusata jama’a, musamman bayan wasu daga cikin Iyalin marigayin sun fito sun yi Allah-wadai da yi wa Maryam afuwa.

Maryam Sanda.
Maryam Sanda da mijinta dan tsohon shugaban PDP, Bilyaminu Bello Hoto: @hapsat_paki
Source: Facebook

’Yan adawa da ƙungiyoyin farar hula ma sun bayyana ra’ayoyinsu kan lamarin, suna gargaɗin cewa yi wa wanda aka yanke masa hukuncin kisa afuwa na iya zama mummunan misali, tare da barazana ga imanin jama’a kan adalci.

Sakamakon fuskantar suka daga jama'a, fadar shugaban kasa ta sake duba jerin afuwar, inda a karshen watan Oktoban 2025, aka cire sunan Maryam Sanda daga jerin wadanda aka yiwa afuwa

Maimakon haka, shugaban kasa ya sassauta mata hukuncin kisa zuwa daurin shekaru 12, kamar yadda TVC News ta ruwaito.

7. Tinubu ya sauya manyan hafsoshin tsaro

A watan Oktoban 2025, Shugaba Tinubu ya yi garambawul a shugabancin sojojin Najeriya, inda ya cire tare da maye gurbin manyan hafsoshin sojojin kasar.

Kara karanta wannan

Kasar Amurka ta janye maganar turo dakarun sojoji Najeriya

A wannan gyaran, Tinubu ya naɗa Janar Olufemi Oluyede, wanda a lokacin shi ne Babban Hafsan Sojojin Kasa, a matsayin Babban Hafsan Tsaro, ya maye gurbin Christopher Musa.

Manjo Janar Waidi Shaibu ya zama Babban Hafsan Sojojin Kasa; yayin da Air Vice Marshal S.K. Aneke ya zama Babban Hafsan Sojojin Sama.

Shugaban kasa, Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu tare da wasu hasoshin tsaro a Aso Rock Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Tinubu ya kuma nada Rear Admiral Idi Abbas a matsayin Babban Hafsan Sojojin Ruwa, sai kuma E.A.P. Undiendeye, wanda shi kadai ya tsira dda mukaminsa na shugaban hukumar tattara bayanan sirri.

Duk da matakin ya haifar da muhawa kan zargin da ake cewa sojoji sun yi yunkurin juyin mulki, amma wasu na ganin canza hafsoshin tsaro ya nuna gwamnati dagaske take a kokarin dawo da zaman lafiya, in ji Premium Times.

8. Nada sababbin jakadun Najeriya

Bayan fiye da shekaru biyu, Shugaba Tinubu, a watan Nuwamba na 2025, ya gabatar da sunayen jakadun Najeriya ga Majalisar Dattawa don tabbatarwa, ciki har da Kayode Are, Aminu Dalhatu, da Ayodele Oke.

Wannan matakin ya kawo karshen dogon lokaci na rashin tabbas da fannin diflomasiyya, wanda ya sa ofisoshin jakadancin Najeriya suka koma hannun kwamitocin gwamnati.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta bude makarantu 47 da aka rufe a fadin Najeriya

Tun farko dai gwamnatin tarayya ta sha suka kan rashin nada jakadu, inda masana siyasa, kungiyoyi da jam'iyyun adawa suka soki jinkirin da Shugaba Tinubu, in ji rahoton Daily Trust.

Fadar shugaban kasa ta yi maganar dokar haraji

A wani rahoton, kun ji cewa fadar shugaban ƙasa ta shiga tsakani kan cece-kuce da aka yi game da dokokin haraji da za su fara aiki daga 1 ga watan Janairu, 2026.

Ta bukaci 'yan Najeriya su daina yada karerayi marasa tushe kan dokokin harajin da ake zargin an yi cushe a takardun da majalisar tarayya ta amince da su.

Fadar shugaban ta kuma jaddada cewa abin da ya bayyana a kafofin yada labarai ba daga kwamitin Majalisar wakilai yake ba, kuma ya kamata a bar su su gudanar da bincike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262