Za a Fara Biyan Tsofaffin Ciyamomi da Kansiloli Alawus Mai Kauri a Jigawa
- Karamar Hukuma a Jihar Jigawa ta fara biyan alawus na wata-wata ga tsofaffin shugabanni da kansiloli
- Tsofaffin shugabannin karamar hukuma za su rika karbar ₦50,000 a wata, mataimaka ₦40,000 domin karfafa mulki
- Shugaban karamar hukumar ya ce shirin zai fara aiki nan take kuma zai taimaka wajen bunkasa ci gaban Kirikasamma
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Jigawa - Karamar Hukuma a Jihar Jigawa ta kaddamar da shirin biyan alawus na wata-wata ga tsofaffin shugabannin da suka mulke ta.
Karamar hukumar Kirikasamma ta ce alawus din za shafi mataimakan ciyamomi, sakatarori da kansilolin da suka rike mukaman a baya.

Source: Facebook
Ciyaman zai ba magabatansa alawus a Jigawa
Shugaban karamar hukumar, Maji Wakili Marma, ne ya bayyana hakan yayin wani taro da aka gudanar a hedkwatar karamar hukumar, cewar Punch.
Marma ya ce sauran tsofaffin masu mukaman siyasa ma za su samu alawus a wani yunkuri na karfafa hulda da hadin kai da su.
Ya ce an dauki matakin ne domin kara dankon zumunci da kuma karrama gudunmawar da tsofaffin jami’ai suka bayar a baya.
Yawan alawus na tsofaffin ciyamomi, kansiloli
A karkashin sabon tsarin, tsofaffin shugabannin karamar hukuma za su rika karbar ₦50,000 a kowane wata, mataimakansu ₦40,000.
Sai kuma sakatarori ₦30,000, yayin da tsofaffin kansiloli za su rika samun kimanin ₦25,000 a wata.
Marma ya bayyana cewa za a rika biyan kudaden akai-akai domin tabbatar da dorewa da daidaito a tsarin.
Ya kuma yaba wa tsofaffin jami’an bisa goyon baya da hadin kai da suke bai wa gwamnati wajen ci gaban karamar hukumar, yana mai cewa gogewarsu da shawarwarinsu na da matukar muhimmanci.

Source: Facebook
Dalilin ware alawus ga tsofaffin masu mukamai
A cewarsa, kimanin tsofaffin masu mukaman siyasa 100 ne ake sa ran za su ci gajiyar shirin, wanda ya bayyana a matsayin wata hanya ta nuna godiya bisa hidimarsu da jajircewarsu ga al’umma.

Kara karanta wannan
Duk da samun jihohi 28, Shugaba Tinubu ya hango matsalar da ta tunkaro jam'iyyar APC
Shugaban karamar hukumar ya ce:
“Mun dauki wannan mataki ne domin inganta alaka da tsofaffin shugabanninmu da kuma amfana da tarin kwarewarsu wajen tafiyar da al’amuran karamar hukumar.”
Ya kara da cewa shirin zai taimaka wajen karfafa hadin kai, zaman lafiya da cigaba a cikin al’umma, tare da rokon wadanda za su amfana da su ci gaba da ba da shawarwari.
Marma ya bayyana kwarin gwiwar cewa shirin zai kara inganta shugabanci a matakin karamar hukuma tare da bayar da gudunmawa ga cigaban al’umma.
Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa an bayyana cikakkun bayanan shirin ne a wani taro na musamman da aka gudanar a hedkwatar karamar hukumar.
Gwamnan Jigawa zai zuba jarin N3.5bn a Tsangaya
Mun ba ku labarin cewa Gwamnatin Jigawa ta dauki aniyar gyarawa da inganta makarantun haddar Alkur'ani da aka fi sani da Tsangaya.
Shugaban hukumar kula da makarantun Tsangya na Jigawa, Abubakar Maje ne ya tabbatar da haka yayin kare kasafin kudin 2026 a Majalisa.
Maje ya lissafa muhimman ayyukan da gwamnatin ta tsara yi da Naira biliyan 3.5 da aka ware wa ilimin Tsangaya a kasafin kudin shekarar 2026.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
