Abba Gida Gida Ya Ba wa Gwamnonin Arewa Mafita game da Matsalar Tsaro

Abba Gida Gida Ya Ba wa Gwamnonin Arewa Mafita game da Matsalar Tsaro

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya shawarci takwarorinsa a kan kafa rundunar hadin gwiwar tsaron iyakokin Arewa maso Yamma
  • Ya bayyana cewa hakan zai taimaka wajen yakar ayyukan ’yan daba da sauran laifuffuka da ake yi ta iyakokin jihohin da ke shiyyar
  • Gwamnan ya jaddada cewa babu wata hukuma guda ɗaya da za ta iya tsare jihar shi kaɗai, kuma hadin kai da aiki tare ne mabuɗin nasara

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa gwamnati na shirin kafa rundunar hadin gwiwar tsaron iyakokin Arewa maso Yamma.

Ya ce za a dauki matakin ne domin magance matsalolin ’yan daba da sauran laifuffuka da ke ketare iyakokin jihohi tare da jawo wa jama'a tashe-tashen hankula.

Kara karanta wannan

"Na cancanci zama shugaban Najeriya," Gwamna ya yi magana kan yin takara a 2027

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da gwamnonin Arewa sun gana game da tsaro
Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf Hoto: Ibrahim Adam
Source: Facebook

Wannan sanarwa ta fito ne daga jawabin gwamnan, wanda Darekta Janar kan yada labarai, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a shafin Facebook a ranar Talata.

Abin da gwamnonin Arewa ke yi kan tsaro

Gwamna Abba ya yi wannan jawabi ne yayin bikin kammala horas da jami’ai 2,000 na rundunar tsaron jihohi a filin wasa na Sani Abacha, Kano.

Ya ce gwamnati na tattaunawa da gwamnonin jihohin makwabta kan dabarun aiki tare, musayar bayanai da gudanar da sintiri don tabbatar da cewa ’yan daba ba su da mafaka a yankin.

Abba Kabir Yusuf ya ce:

“Ina so in sanar da cewa gwamnati na tattaunawa da jihohin da abin ya shafa don tsara dabarun aiki tare, gudanar da sintiri da musayar bayanai domin magance barazanar da ke ketare iyakokin jihohi."

Gwamnan Kano na neman hadin kan jihohi

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kara da cewa wannan shiri ya dace da hangen nesa na Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Yamma, karkashin jagorancin Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umar Radda.

Kara karanta wannan

2027: Kawu Sumaila ya fadi zabinsa daga cikin masu son takarar gwamna a Kano

Gwamnan ya bukaci sarakuna da al’ummomi su goyi bayan sabuwar rundunar tsaron jiha da aka samar, sannan ya nemi hadin kan ‘yan sanda, DSS, NSCDC, sojoji, Hisbah da KAROTA domin tabbatar da tsaro.

Abba ya ce samar da runduna ta musamman ya zo daidai da kudirin gwamnonin yankin
Gwamna Dikko Radda, Shugaban kungiyar gwamnonin Arewa maso Yamma Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda
Source: Facebook

Gwamna Abba ya umarci jami’an da aka yaye da su gudanar da ayyukansu bisa gaskiya, su girmama doka, sannan su yi aiki kafada da kafada da sauran hukumomin tsaro.

A yayin bikin, ya kaddamar da motoci sama da 400 da za su taimaka wajen aiki a cikin sauri da inganci a fadin kananan hukumomin Kano 44.

Gwamna ya share hawayen Kansilolin Kano

A baya, mun wallafa cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya kammala biyan dukkannin bashin alawus da na tsofaffin kansiloli da suka taru har na tsawon shekaru 10 ba a biya su ba.

Wannan biyan bashin ya hada da Naira biliyan 8.26 ga kansiloli 1,371 da suka yi aiki tsakanin shekarun 2021 zuwa 2024, yayin da aka biya tsofaffin kansiloli daga 2014 zuwa 2020 a watan Mayu da Agusta 2025.

Gwamna Abba ya bayyana cewa wannan mataki ba wai kawai rufe wani shafi na bashi bane, har ma yana bude sabon babi, tare da tabbatar da cewa kansiloli masu aiki yanzu sun riga sun samu 50% na hakkinsu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng