Kwankwaso Ya Mika Bukata ga Yan Sanda kan Zaman Aminu Ado Bayero a Fadar Nassarawa

Kwankwaso Ya Mika Bukata ga Yan Sanda kan Zaman Aminu Ado Bayero a Fadar Nassarawa

  • 'Dan takarar Shugaban Kasa a zaben 2023, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bukaci a janye jami’an tsaro daga fadar Nasarawa a jihar Kano
  • Ya jaddada cewa Khalifa Muhammadu Sanusi II ne halastaccen Sarkin Kano saboda haka babu dalilin girke 'yan sanda a gidan Sarki na Nassarawa
  • Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne a yayin da Gwamnan Kano mai ci, Abba Kabir Yusuf ya goyi bayan kafa ’yan sandan jihohi da tsaron al’umma

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma jagora a jam'iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya kara magana game da rikicin masarauyar Kano.

Kwankwaso, wanda tsohon dan takarar Shugaban Kasa ne ya yi kira ga Kwamishinan ’Yan Sandan Kano da ya janye jami’an tsaro da aka jibge a Fadar Nasarawa inda Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ke zaune.

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida ya ba wa gwamnonin Arewa mafita game da matsalar tsaro

Kwankwaso ya nemi a janye yan sandan da ke tsaron Aminu Ado Bayero
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso Hoto: Ibrahim Adam
Source: Facebook

Jawabin Kwankwaso na kunshe a cikin wata sanarwa da Darektan yada labaran gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kiran Kwankwaso game da Aminu Ado Bayero

Kwankwaso ya nemi a janye jami'an Sarkin yayin da yake jawabi a bikin kaddamar da rundunar tsaro mallakin jiha da aka gudanar a Kano ranar Talata, 23 ga watan Disamba, 2025.

Ya sake jaddada matsayinsa na cewa Muhammadu Sanusi II shi ne kadai halastaccen Sarkin Kano, ya ce samun sarakuna ko masarautu masu cin karo da juna na iya barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

A kalaman Kwankwaso:

“Halastaccen Sarkin Kano shi ne Muhammadu Sanusi II. Shi ne sarkin Kano na gaskiya."

Rikicin masarautar Kano ya samo asali ne tun a watan Maris na shekarar 2020, lokacin da tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya tube Sarkin Kano na wancan lokaci, Muhammadu Sanusi II.

Ya bayyana cewa an dauki matakin bisa zargin rashin biyayya da rikicin siyasa. Daga bisani Ganduje ya raba masarautar Kano zuwa gida hudu, tare da nada Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya ja tawaga, ana kaddamar da sabuwar hukumar tsaro a Kano

Sai dai Gwamna Abba Kabir Yusuf ya soke wannan mataki, ya rusa sababbin masarautun, ya cire Aminu Ado Bayero, sannan ya maido da Sanusi II kan karagar mulki.

Gwamnan Kano ya kaddamar da rundunar tsaro

A nasa bangaren, Gwamna Abba Yusuf ya bayyana cikakken goyon bayansa ga kiran Shugaba Bola Ahmed Tinubu na kafa ’yan sandan jihohi, yana mai cewa hakan muhimmin mataki ne wajen magance matsalolin tsaro a Najeriya.

Ya ce zaman lafiya mai dorewa ba zai samu ba sai an hada ingantaccen tsaro da samar da damammakin tattalin arziki, yana jaddada cewa matasa marasa aikin yi sun fi fuskantar fadawa harkokin laifi.

Gwamnan Kano ya goyi bayan samar da yan sandan jihohi
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Ibrahim Adam
Source: Facebook

A cewar Gwamnan:

“Mun kammala horas da matasa sama da 2,000 a yau, mun cire su daga tituna mun saka su cikin aikin hidimar jama’a. Ba wai kawai suna kare al’ummominsu ba ne, suna gina sana’o’i, suna samun abin dogaro da kai, kuma suna zama abin koyi."

APC na neman Kwankwaso - Jam'iyyar NNPP

A baya, kun ji cewa Shugaban NNPP a Jihar Kano, Dr Hashimu Sulaiman Dungurawa, ya bayyana cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na da tasiri sosai a fagen siyasar Kano da Najeriya baki daya.

Kara karanta wannan

Tsagin NNPP na son jawo matsala bayan babban taron su Kwankwaso a Abuja

Ya ce jam’iyyar APC ba ta da karfin siyasa da zai ba ta damar samun nasara a zaben shekarar 2027, saboda haka Kwankwaso na da muhimmanci wajen samu ko jawo wa jam'iyyar rashin nasara.

Dungurawa ya fadi haka ne yayin taron manema labarai a hedikwatar NNPP, inda ya ce APC ta Kano da ta tarayya sun samu rashin jagoranci, wanda hakan ya sa suke neman taimako daga Kwankwaso.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng