N58.47tn: Majalisa Ta Fara Tafka Muhawara kan Kasafin 2026 da Tinubu Ya Gabatar

N58.47tn: Majalisa Ta Fara Tafka Muhawara kan Kasafin 2026 da Tinubu Ya Gabatar

  • Kasafin kudin 2026 na Naira tiriliyan ₦58.47 da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar ya tsallake karatu na biyu a majalisar dattawa
  • Sanata Opeyemi Bamidele ya bayyana cewa kasafin zai mayar da hankali ne kan manyan ayyuka da rage dogaro ga basussukan waje
  • An tura kudurin zuwa kwamitin kasafi na majalisa don tantancewa, inda ake sa ran kammala duba shi a cikin watan Janairu, 2026

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A ranar Talata ne Majalisar Dattawa ta fara muhawara kan lissafin kasafin kuɗin shekarar 2026 a Shugaba Bola Tinubu ya gabatar mata.

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Opeyemi Bamidele, ya jagoranci tattaunawar kan wannan gagarumar shawara ta kashe kuɗi har Naira tiriliyan 58.47 a 2026.

Majalisar dattawa ta amince kasafin 2026 da Tinubu ya gabatar ya tsallake karatu na biyu
Shugaba Bola Tinubu ya na jawabi ga taron hadin gwiwar majalisar dokokin tarayya a Abuja. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Kasafin 2026: 'Yan majalisa sun fara muhawara

Yayin gabatar da ƙa'idojin lissafin, Bamidele ya bayyana wa majalisar cewa wannan doka ita ce matakin shari'a na aiwatar da kasafin kuɗin 2026, a cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Zargin badakalar N4.6bn: EFCC ta shirya fara shari'a da Kwamishinan kudi a Bauchi

Ya bayyana kasafin a matsayin ginshiƙin gudanar da gwamnati da tattalin arziki, yana mai jaddada cewa shi ne yake mayar da manufofin shugaban ƙasa zuwa ayyukan gwamnati na zahiri.

Game da yanayin tattalin arziki kuwa, shugaban masu rinjayen ya ce an tsara kasafin kudin 2026 ne a daidai lokacin da ake fuskantar sauye-sauyen tattalin arziki da nufin dawo da daidaito da kuma ƙarfafa asusun gwamnati.

Yadda aka tsara kasafin kudin 2026

Sanata Bamidele ya bayyana cewa Naira tiriliyan ₦58.472 da ake shirin kashewa sun ƙunshi:

  • Naira Tiriliyan 4.097 na kason da doka ta tanada
  • Naira Tiriliyan 15.909 na biyan bashi.
  • Naira Tiriliyan 15.252 na ayyukan yau da kullum
  • Naira Tiriliyan 23.214 na manyan ayyuka

A cewarsa, tsarin kasafin ya nuna fifikon da aka ba ayyukan ci gaba, inda aka ware mafi yawan kuɗin don sassa masu mahimmanci kamar sufuri, wutar lantarki, noma, ci gaban masana'antu, gidaje, da fasahar zamani.

Game da biyan bashi kuma, Bamidele ya ce an ware Naira tiriliyan 15.909 domin nuna wajibcin biyan basussuka, amma ya jaddada ƙoƙarin gwamnati na inganta hanyoyin samun kuɗin shiga don rage dogaro ga bashi nan gaba.

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida ya ba wa gwamnonin Arewa mafita game da matsalar tsaro

Majalisar dattawa za ta duba rahoton kwamitin kasafi a 2026 domin amincewa da shi.
Sanata Godswill Akpabio ya na jagorantar zaman majalisar dattawa a Abuja. Hoto: @NGRSenate
Source: Facebook

Kasafin 2026 ya tsallake karatu na 2

Majalisar Dattawa ta amince da kudirin kasafin kuɗin gwamnatin tarayya na ₦58.472tr na shekarar 2026 don tsallakawa zuwa karatu na biyu.

Shugaba Bola Tinubu ne ya gabatar da kasafin, wanda aka yi wa laƙabi da "kasafin karfafawa da samar da walwala", a ranar Juma'a, 19 ga Disamba, 2025.

Kamar yadda kafar yaɗa labarai ta NTA ta ruwaito, an tura kasafin zuwa ga kwamitin kasafi na majalisar dattawa don su duba shi, sannan su dawo da rahoto gaban majalisar nan da wata guda.

Yayin muhawarar, mambobin majalisar sun yaba wa kason da aka ware wa kowane sashe, suna masu bayyana shi a matsayin lissafi mai ma'ana.

Bangarorin da aka fi warewa kudi a kasafin 2026

A wani labari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya gabatar da kasafin 2026 na fiye da N58trn ga haɗin gwiwar Majalisar Ƙasa a ranar 19 ga Disamba, 2025.

Kara karanta wannan

Tinubu ya tura tawaga Morocco yayin da Najeriya za ta fafata da Tanzania a AFCON 2025

Kasafin kudin shekarar 2026 da Shugaban Kasa ya gabatar ya jaddada muhimman manyan bangarori huɗu: tsaro, ilimi, lafiya da ababen more rayuwa.

A cewar Shugaba Bola Tinubu, waɗannan fannoni hudu suna da alaƙa da juna, kuma su ne ginshiƙin hanyar Najeriya zuwa haɓakar tattalin arziƙi mai dorewa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com