Yadda Gwamnatin Tarayya Ke Sauke Shafukan Sada Zumuntan ’Yan Ta’adda

Yadda Gwamnatin Tarayya Ke Sauke Shafukan Sada Zumuntan ’Yan Ta’adda

  • Gwamnatin Tarayya ta ce tana aiki tare da manyan kamfanonin kafafen sada zumunta domin gano yan ta'adda
  • Hakan na daga cikin kokarin rufe asusun ’yan ta’adda da masu laifi da ke amfani da su wajen yaɗa ayyukansu
  • Shugaban hukumar yaki da ta'addanci, Janar Adamu Laka, ya bayyana kokarin da suke yi kan haka

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana cewa hukumomin tsaro suna aiki domin kakkabe yan ta'adda.

Gwamnatin ta ce tana aiki kafada da kafada da manyan kamfanonin kafafen sada zumunta domin gano tare da goge asusun da ’yan ta’adda.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya ja tawaga, ana kaddamar da sabuwar hukumar tsaro a Kano

Ana goge shafukan sada zumunta na yan ta'adda a Najeriya
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Ana shafe shafukan sada zumuntan 'yan ta'adda

Darakta Janar na Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta Ƙasa (NCTC), Manjo Janar-Adamu Laka shi ya bayyana haka a Abuja, cewar Punch.

Laka ya ce ’yan ta’adda sun dade suna amfani da dandali irin su TikTok, Facebook, Instagram, Snapchat da X wajen sanar da hare-harensu.

A cewarsa, hukumomin tsaro sun yi taruka da dama da shugabannin kafafen sada zumuntar domin magance wallafe-wallafe da asusun da ke barazana ga tsaron ƙasa.

Kara karanta wannan

Bayanai na kara fitowa a kan yadda gwamnati ta ceto daliban Neja

Laka ya ce:

“Batun amfani da kafafen sada zumunta da kungiyoyin ’yan ta’adda ke yi, da kun san yawan asusun da muka rufe. Mun yi taruka da dama da wadannan kamfanoni kamar TikTok, Instagram, Snapchat, Facebook da X.
“Su kasuwanci suke yi, suna son kara yawan masu bibiyarsu, amma muna shiga mu bayyana musu illar wasu wallafe-wallafe ga tsaron kasa, sannan mu tabbatar an goge su.
“Akwai lokacin da ’yan bindiga ke shiga TikTok suna nuna ganimar da suka kwace. Mun rufe wadannan asusu, ba ku ganin haka yanzu."
Gwamnatin Tinubu na kokarin kakkabe yan ta'adda
Ministan tsaro, Christopher Musa da Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

'Dabarun da 'yan ta'adda ke yi'

Laka ya kara da cewa dabarun ’yan ta’adda na ci gaba da sauyawa, ciki har da amfani da sunaye na bogi da asusun da ba a tantance su ba, cewar Daily Post.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi aika aika bayan kai wani harin ta'addanci a Zamfara

Janar Laka ya kuma bayyana cewa biyan kudin fansa na daga cikin manyan hanyoyin daukar nauyin ta’addanci, inda ake amfani da masu POS wajen tura kuɗaɗe.

“Za ka ga an canja wurin tura kuɗi, idan ka bincika asusun, sai ka gano na mai POS ne. Masu garkuwa da mutane suna ba da lambar POS, a tura kuɗin, sannan su je su karɓa.”

Shugaban yaki da ta’addancin ya ce hukumomin tsaro sun ƙara ƙaimi wajen bin diddigin kudin fansa, kama masu hannu a ciki da kuma rusa hanyoyin daukar nauyin ta’addanci.

Kungiyoyi da za a ayyana yan ta'adda

Kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da sabon tsari na yaƙi da ta’addanci a Najeriya baki daya.

Tinubu zai ayyana ’yan bindiga, masu garkuwa, masu karɓar kuɗin fansa da masu taimaka musu a matsayin ’yan ta’adda.

Shugaban ya ce manufar ita ce kare zaman lafiyar ƙasa, rage fargabar jama’a da tabbatar da sakamako mai gamsarwa daga kuɗaɗen tsaro.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.