Yadda Tonon Sililin Dangote Ya Ci Kujerun Shugabannin Hukumomi 2 a Najeriya
- Alhaji Aliko Dangote, ya tona badakalar cin hanci da rashawa da ya alakanta da hukumomin NMDPRA abin da ya tayar da kura a Najeriya
- Dangote ya zargi shugaban NMDPRA, Farouk Ahmed, da biyan dala miliyan biyar kudin makarantar ’ya’yansa a Switzerland, inda ya bukaci a gurfanar da shi kotu
- Bayan zargin, Farouk Ahmed da Gbenga Komolafe sun ajiye mukamansu, yayin da Shugaba Tinubu ya tura sunayen sababbin shugabannin majalisa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Attajiri a Nahiyar Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya yi zargin cin hanci da rashawa da ya tayar da hankula a Najeriya.
Aliko Dangote ya tona wata badakala da ya ke zargin an aikata a wasu hukumomi guda biyu da ke da alaka da ma'aikatun mai.

Source: Getty Images
Rahoton Punch ya ce zargin Dangote ya yi sanadin rasa kujerun shugabannin hukumomin NMDPRA da NUPRC.
Aliko Dangote ya zargi shugaban NMDPRA Farouk Ahmed da biyan $5m kudin makarantar sakandaren ‘ya’yansa hudu a Switzerland.
Wadanda ake magana kan su, sun hada da shugaban NMDPRA, Farouk Ahmed da kuma na NUPRC, Gbenga Komolafe.
Zargin da Dangote ke yi wa Farouk Ahmed
Attajirin ya bukaci a gurfanar da Farouk Ahmed a gaban kotun da'ar ma'aikata domin ya bayyana yadda ya samu wadannan makudan kudade.
Domin kara karfafa zarginsa, Dangote ya fadi wani muhimmin mataki da zai dauka idan Alhaji Farouk ya musanta biyan wadannan kudade.
Legit Hausa ta duba masu mukamai guda biyu da suka ajiye aikinsu bayan tonon asiri da Dangote ya yi na zargin cin hanci.
1. Farouk Ahmed - tsohon shugaban NMDPRA
Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Kasa (NMDPRA), Farouk Ahmed ya yi murabus daga mukaminsa ranar Laraba, 17 ga watan Disamba, 2025.
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga shi ya tabbatar da murabus din Farouk Ahmed a shafin X.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa sa'o'i kafin murabus dinsa, tsohon shugaban NMDPRA ya ziyarci Bola Tinubu a fadar shugaban kasa da ke babban birnin tarayya, Abuja.

Source: Facebook
2. Gbenga Komolafe - tsohon shugaban NUPRC
Har ila yau, shugaban hukumar NUPRC, wacce ita ma ta shafi kula da harkokin man fetur, Gbenga Komolafe ya yi murabus daga mukaminsa.
Ba tare da bata lokaci ba, Shugaba Tinubu ya bukaci Majalisar Dattawa ta amince da nadin sababbin shugabannin hukumomin guda biyu.
Tinubu ya tura sunayen wadanda za su ci gaba da jagorancin na Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Tsakani da Kasa (NMDPRA) da kuma Hukumar Kula da Harkokin Hako Man Fetur ta Kasa (NUPRC).
Hadimin shugaban kasar ya ce Tinubu ya tura sunayen mutane biyu, Oritsemeyiwa Eyesan a matsayin shugaban NUPRC, da kuma Saidu Mohammed a matsayin shugaban NMDPRA zuwa Majalisar Dattawa domin tantance su.

Source: Facebook
Farouk Ahmed: Abin da yan Najeriya ke cewa
Wannan zarge-zarge da Dangote ya yi, ya tayar da kura a Najeriya inda wasu ke ganin kudin da ake magana sun yi yawa matuka.
'Yan Najeriya da dama sun nuna damuwa kan lamarin har ma wasu daga cikin manyan yan siyasa a kasar.
Mafi yawan wadanda suka yi magana sun caccaki tsohon shugaban NMDPRA yayin da wasu ke ganin an yi haka ne domin raba Farouk da kujerarsa.
Bukatar Oshimhole game da Farouk Ahmed
Sanata Adams Oshiomhole ya bayyana damuwa game da Farouk Ahmed inda ya bukaci daukar mummunan mataki kansa.
Tsohon gwamnan ya ce ya yi murnar murabus din shugabannin NMDPRA da NUPRC daga mukamansu.
Oshiomhole ya ce ya ji dadi ne saboda haka ya zama dole domin ceto tattalin arzikin Najeriya daga rugujewa.
Daga bisani, Oshiomhole ya bukaci a rataye Farouk saboda irin haka ne yake kassara tattalin arzikin Najeriya har kasa.
Sanata David Jimkuta ya goyi bayan sanatan yayin tantance sababbin shugabannin hukumomin da Bola Tinubu ya tura.
NMDPRA: An maka Tinubu a kotu
Mun ba ku labari a baya cewa wata kungiya ta shigar da kara a kotu kan zargin rashin gaskiya da ake yi wa tsohon Shugaban hukumar NMDPRA, Farouk Ahmed.
Karar ta biyo bayan zargin da Aliko Dangote na cewa Farouk Ahmed na aikata almundahana da cin mutuncin kujerarsa.
Kungiyar na neman a yi bincike, a dakatar, tare da gurfanar da tsohon Shugaban NMDPRA a gaban kotu domin gaskiya ta yi halinta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



