Fetur: Man da Najeriya Ta Dogara da Shi Ya ba Ta Kunya da Hasashen Kudin Shigan 2025
- Kudaden da Najeriya ke samu sun ragu har sun gaza hasashen da aka yi a kasafin kudin shekarar da muke bankwana da ita watau 2025
- A rahoton ofishin kula da harkokin kasafin kudi na tarayya, Najeriya ta gaza samun 63.49% na kudaden da ta yi tsammanin samu daga mai a farkon 2025
- Rahoton ya nuna cewa an samu ci gaba ta fannin adadin danyen man da ake hakowa, sai dai ana fama da kalubale da dama
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Gwamnatin Tarayya ta samu babban cikas a kudin da ta yi hasashen samu daga bangaren man feturin da ake hakowa a Najeriya a watanni shida na farko a 2025.
Rahoto ya nuna cewa Najeriya ta rasa sama da rabin kudin da ta yi hasashen samu duk da ɗan ƙarin da aka samu a yawan danyen man fetur da Najeriya ke samarwa.

Source: Getty Images
Jaridar Punch ta ruwaito cewa hakan na kunshe ne a cikin rahoton Budget Performance Report na zangon biyu (Q2) da Ofishin Kasafi na tarayya ya fitar.
Najeriya ta samu cikas a hasashen 2025
Rahoton ya nuna cewa daga watan Janairu zuwa Yuni 2025, an samu Naira tiriliyan 9.32 daga kudin man fetur, sabanin Naira tiriliyan 25.52 da aka yi hasashe a kasafin kudin 2025.
Wannan na nufin an rasa Naira tiriliyan 16.20, wato kashi 63.49 cikin 100 na abin da aka yi hasashe, lamarin da ya sake nuna raunin tsarin kudaden shiga na Najeriya da ya dogara sosai da man fetur.
A bangaren samarwa, matsakaicin danyen man da Najeriya ke hakowa a kowace rana ya kai ganga miliyan 1.68, wanda ya kasa cimma ganga miliyan 2.12 da aka sa a kasafin kudin 2025.
Wane ci gaba aka samu a bangaren mai?
Sai dai duk da haka, an samu ɗan ci gaba idan aka kwatanta da lokutan baya, domin man da ake hakowa ya haura na rubu'in farko na 2025 da kuma ta shekarar 2024 a irin wannan lokaci.
Ko da yake kudin da aka samu bai kai abin da aka tsara ba, rahoton ya nuna cewa an samu ci gaba idan aka kwatanta da shekarar 2024, inda kudin man fetur ya karu da Naira tiriliyan 2.78, wato kashi 42.59 cikin 100.
Wannan ya samo asali ne daga ƙarin adadin da ake hakowa da kuma ingantaccen taarun tattara haraji, kamar yadda Bussiness Day ta ruwaito.
Rahoton ya kuma bayyana cewa a zangon biyu na 2025 kadai, kudin da Najeriya ta samu daga bangaren mai ya kai Naira tiriliyan 4.77, amma har yanzu ya yi ƙasa da hasashen zangon da kusan kashi 62 cikin 100.
A bangaren kudaden da ba na mai ba, an samu ɗan ci gaba, wanda aka danganta da hauhawar farashi da ƙarin harkokin tattalin arziki.

Source: Getty Images
Matsalolin da bangaren mai ke fuskanta
Ofishin Kasafi ya jaddada cewa duk da sauye-sauyen da aka kawo ta hanyar Dokar Fetur ta PIA, bangaren man fetur na Najeriya na ci gaba da fuskantar manyan matsaloli.
Daga cikin matsalolin akwai satar mai, fasa bututun mai, rashin tsaro, ƙarancin zuba jari, da ƙarancin tace mai a cikin gida.
Wadannan kalubalen na ci gaba da barazana ga tattalin arziki da kuma kudaden shiga na gwamnati, lamarin da ke nuna bukatar bullo da sauye-sauye da za au shawo kan matsaloli.

Kara karanta wannan
Saukin da Dangote ya yi ya jawo 'yan kasuwa sun fara rage farashin fetur a Najeriya
Danyen mai ya yi warwas a kasuwar duniya
A wani rahoton, kun ji cewa farashin danyen mai a duniya ya fadi zuwa kasa da dala $60 kan kowace ganga karo na farko tun watan Fabrairun 2021.
Majiyoyi sun nuna cewa danyen man Brent, wanda shi ne ma’aunin farashin mai na duniya, ya fadi da 2.86% zuwa dala $58.83 kan kowace ganga.
Wannan faduwar farashi na da nasaba da damuwar yawaitar mai a kasuwa, tare da karuwar bukatar cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

