"Ba Gwamnoni ne Kadai Barayi a Najeriya ba:" Dikko Radda Ya Dauki Zafi

"Ba Gwamnoni ne Kadai Barayi a Najeriya ba:" Dikko Radda Ya Dauki Zafi

  • Gwamna Dikko Umaru Radda ya kalubalanci masu kiran gwamnoni barayi, inda ya ce wasu ba su da nagartar yin magana kan batun
  • Ya ce ba gwamnoni kaɗai ne ke satar kuɗi ba, akwai sauran shugabanni da suka aikata hakan kuma kujerunsa ba su kai na gwamna ba
  • Game da batun tsaro, ya ce dole ne jihohin Arewa su hada kai wajen dawo da tsaro da kawo ƙarshen ta’addancin da ya addabe su

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina – Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya dauki zafi a kan masu kiran gwamnonin Najeriya da barayi.

Ya bayyana cewa ba gwamnoni ke kawai barayi ba, an samu mutanen da suka riƙe kujerun da ba su kai na gwamna ba da tafka mummunan sata.

Kara karanta wannan

Babbar magana: An fara neman a tsige Bola Tinubu daga kujerar shugaban kasa

Gwamnan Katsina ya ce ba gwamnoni ne kadai barayi ba
Gwamnan jihar Katsina, Umaru Dikko Radda Hoto: Dr. Umaru Dikko Radda
Source: Facebook

Dikko Radda ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da RFI da aka wallafa a shafin Facebook, inda ya ce akwai barayi da dama a madafun iko daban-daban.

Gwamna Dikko Radda ya dauki zafi

Gwamna Dikko Umaru Radda ya ce wasu daga cikin mutanen da ke zargin gwamnoni ba su da nagarta da za su bude bakin fada masu haka.

Ya ce:

"Gwamnoni ne kaɗai barayi a Najeriya? Barayi nawa aka kama aka ga kudin da ba a tunani ko rabin kujerar Gwamna ba su kai ba? Magana ce ta nagarta mutane."
"Ba daidai ba ne mutane su rika kudin goro suna kiran mutane da kowane irin sunaye. Wani ma ba abinda nagartar da zai kira ka da sunaye. Shugabancin nan duka amana ce. Idan baka amsa gaban mutane ba za ka amsa a gaban Allah."
"Abin da ke da amfani a gwamnati shi ne a tabbatar da cewa kuɗin alumma suna kai wa gare su."

Kara karanta wannan

2027: Kawu Sumaila ya fadi zabinsa daga cikin masu son takarar gwamna a Kano

Dikko Radda ya magantu game da tsaro

Game da batun tsaro, Dikko Radda ya ce akwai bukatar a yi aiki a matsayin tsintsiya madaurinki ɗaya matukar ana son dawo da zaman lafiya.

Gwamnan Katsina ya magantu game da tsaro a Najeriya
Umaru Dikko Radda, Gwamnan Jihar Katsina Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda
Source: Facebook

Ya ce:

"A shawarwari da muka yi da gwamnoni, ya zama wajibi gare mu mu dauki tsari guda daya wanda zai kawo wa yankin mu tsaro daidai gwargwado."
"Mun fahimci cewa idan muka yi maganin tsaro a Katsina, ba mu tare bangaren Zamfara ba da mu ke iyaka da su, aikinmu ba zai yi nasara ba."
"In Zamfara ta yi Katsina ba ta yi ba, aikin ba zai yi nasara yadda ake so ba, sai dai ya rage."

Ya bayyana cewa dole ne sai jihohin Arewa kamar Kano, Katsina, Kaduna, Zamfara, Kebbi, Sokoto da Zamfara sun yi aiki tare idan da gaske za a kawo karshen matsalar ta'addanci.

Gwamnan Katsina ya yabi sulhu da 'yan ta'adda

A baya, mun wallafa cewa Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya yi magana kan batun sulhun da wasu al'ummomi daban-daban a jiharsa suka kulla da 'yan bindiga domin samun sauki hare-hare.

Kara karanta wannan

Abin da Abba, Kwankwaso suka shaidawa zababbun shugabannin jam'iyyar NNPP

Gwamna Radda ya yabawa al’ummomin da suke fama da matsalar tsaro saboda kulla yarjejeniyar zaman lafiya da ‘yan bindiga a yankunansu, inda su ke dauki hakan a matsayin mafitarsu.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyararsa a kananan hukumomin Batsari da Danmusa, a ci gaba da zagayen da yake yi a fadin jihar. Ya ce yarjejeniyar da aka kulla sun fara haifar da da mai ido.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng