Jami'an DSS Sun Cafke 'Yan Ta'addan ISWAP da Suka Tsallaka Kudancin Najeriya

Jami'an DSS Sun Cafke 'Yan Ta'addan ISWAP da Suka Tsallaka Kudancin Najeriya

  • Dubun wasu 'yan ta'addan kungiyar ISWAP ta cika bayan da suka fada hannun jami'an hukumar DSS a jihar Legas
  • Jami'an na hukumar DSS sun cafke 'yan ta'addan ne bayan sun baro yankin Arewa maso Gabas da suka dade suna ta'addanci
  • Bayan cafke mutanen da ake zargi, jami'an na hukumar DSS sun tsare su domin ci gaba da tatsar bayanai daga wajensu

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Legas - Jami’an tsaro sun kama mutane biyu da ake zargin ’yan ta'addan kungiyar Islamic State West Africa Province (ISWAP) ne a jihar Legas.

Jami'an tsaron na hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun cafke 'yan ta'addan ne a ranar Lahadi, 21 ga watan Disamban 2025.

Jami'an DSS sun kama 'yan ta'addan ISWAP
Jami'an hukumar DSS a bakin aiki Hoto: @OfficialDSSNG
Source: Facebook

Jaridar Premium Times ta ce waɗanda ake zargin, Modu Gana da Ibrahim Dugge, sun shiga hannun jami’an hukumar DSS.

Kara karanta wannan

'Dan Majalisa, Bello El Rufai ya lale miliyoyi domin taimakon karatun mutane a Kaduna

'Yan ta'addan ISWAP sun shiga hannun DSS

Wata majiya ta tsaro mai masaniya kai tsaye kan kamun ta bayyana cewa an kama Modu Gana da Ibrahim Dugge ne a cikin birnin Apapa, na jihar Legas.

"An kama su da misalin karfe 8:45 na safe a ranar Lahadi, 21 ga watan Disamban 2025."

- Wata majiya

Majiyar ta kara da cewa an tsare wadanda ake zargin domin yi musu tambayoyi.

Jaridar ta gano cewa kamen ya biyo bayan bayanan sirri da suka nuna cewa waɗanda ake zargin sun tsere daga yankin Arewa maso Gabas da rikicin ’yan ta’adda ya lalata, zuwa jihar Legas.

Me jami'an hukumar DSS suka ce kan kamun?

Da aka tuntubi wani jami’i daga sashen yaɗa labarai na hukumar DSS, ya ce ba a sanar da su batun kamen ba.

Tun bayan sake wajen aiki ga tsohon kakakin DSS, Peter Afunanya, hukumar ta ɗauki tsarin sirri a hulɗa da kafafen yaɗa labarai, inda ta ce hakan zai taimaka mata wajen gudanar da ayyukan leken asiri yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

A karshe, Gwamnatin Tarayya ta bayyana kungiyoyi da take kallo a matsayin 'yan Ta'adda a Najeriya

Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, ba a san takamaiman manufar zuwan waɗanda ake zargin Legas ba.

Haka kuma, babu wata alama da ke nuna cewa suna shirin kai hari a Legas, cibiyar kasuwanci ta Najeriya. Sai dai masana sun ce ISWAP na kokarin faɗaɗa ayyukanta zuwa wajen yankin Arewa maso Gabas.

DSS ta yi caraf da 'yan ta'addan ISWAP a Legas
Taswirar jihar Legas, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Yakin Najeriya da ’yan ta’adda

Ta'addancin Boko Haram ya shafe fiye da shekaru 15 yana gudana. Bayan rarrabuwa gida biyu da ta haifar da ɓangarori biyu a shekarun 2012 da 2016, rikicin ya wuce jihohin Borno, Adamawa da Yobe, waɗanda suka fi shan wahala.

Yayin da ’yan ta’addan suka kashe dubban ’yan Najeriya tare da tilasta miliyoyin mutane barin muhallansu, jami’an tsaro sun kuma kara zafafa hare-hare a kansu.

A watan Mayu, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa an kashe ’yan Boko Haram da ISWAP 13,543, yayin da 124,408 suka mika wuya cikin shekaru biyu na mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

DSS ta gayyaci Datti Baba-Ahmed

Kara karanta wannan

Buhari, Dahiru Bauchi da mutanen da Tinubu ya mayar da sunayen jami'o'i zuwa sunan su

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar tsaron farin kaya (DSS), ta aika da goron gayyata zuwa ga Yusuf Datti Baba-Ahmed.

DSS ta gayyaci tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar LP a zaben 2023 ne saboda wasu kalamai da ya yi.

Hukumar DSS ta gayyace shi ne bisa zargin cewa yana ci gaba da bayyana ra’ayoyi da ake kallon suna tunzura jama'a kan gwamnatin Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng