Daukar Ma'aikata: Gwamnatin Tarayya Ta Bullo da Wata Doka ga Masu Neman Aiki a Najeriya

Daukar Ma'aikata: Gwamnatin Tarayya Ta Bullo da Wata Doka ga Masu Neman Aiki a Najeriya

  • Gwamnatin tarayya ta wajabta gwajin miyagun kwayoyi kan duk wanda ke neman aikin domin tsaftace tsari da samar da ingantaccen aiki
  • Wannan mataki na zuwa ne yayin da ake kara samun yawaitar ta'amali da miyagun kwayoyi, musamman tsakanin matasan Najeriya
  • Ta umarci kowace ma'aikata da hukumomin gwamnati su hada kai da hukumar NDLEA domin fara aiwatar da dokar yayin daukar ma'aikata

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Gwamnatin tarayya ta sake kawo karin doka a tsarin daukar mutane aikin gwamnati a Najeriya.

Gwamnatin ta sanar da cewa daga yanzu, wajibi ne a yi wa duk wani mai neman aikin gwamnatin tarayya gwajin miyagun kwayoyi domin tabbatar da lafiyarsa.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnatin Najeriya Hoto: @OfficialABAT
Source: Twitter

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa hakan na kunshe ne a wata takardar sanarwa da ofishin sakataren gwamnatin tarayya (OSGF), Sanata George Akume ya fitar yau Litinin.

Kara karanta wannan

Babbar magana: An fara neman a tsige Bola Tinubu daga kujerar shugaban kasa

Takardar mai dauke da kwanan watan 22 ga watan Disamba, 2025, ta sanar da daukacin ma'aikatan gwamnati wannan sabon tsari da aka kawo na gwajin ta'amali da miyagun kwayoyi.

An wajabta gwajin kwaya wajen daukar aiki

A cewar gwamnati, an dauki wannan mataki ne domin kare ma’aikatan gwamnati daga barazanar da karuwar shan miyagun kwayoyi ke haifarwa.

A karkashin sabon tsari, gwamnati ta umarci manyan sakatarori na ma'aikatu da shugabannin hukumomi da su sanya gwajin miyagun kwayoyi cikin tsarin daukar sababbin ma’aikata.

Domin tabbatar da gaskiya da sahihanci, an kuma umurci Ma’aikatu, Hukumomi da Cibiyoyin Gwamnati (MDAs) da su yi aiki kafada da kafada da Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) wajen gudanar da gwaje-gwajen.

Dalilan wajabta gwajin miyagun kwayoyi

Gwamnatin Tinubu ta bayyana cewa an dauki wannan shawara ne sakamakon yawaitar shan miyagun kwayoyi, musamman a tsakanin matasa ‘yan Najeriya.

Ta kuma jaddada cewa wannan dabi'a ta shan miyagun kwayoyi na da mummunar illa ga lafiyar jama’a, ingancin aiki a wuraren aiki da kuma tsaron kasa, in ji tashar Channels.

Ta kara da cewa shan miyagun kwayoyi ba tare da kulawa ba yana rage kwarewa da nagartaccen aiki a gwamnati, tare da kara tsananta matsalolin tattalin arziki da zamantakewa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi aika aika bayan kai wani harin ta'addanci a Zamfara

George Akume.
Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume Hoto: @SGFAkume
Source: Facebook

Takardar, wadda Segun Imohiosen, Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na OSGF, ya sanya hannu, ta sake jaddada kudirin gwamnati na tsaftace bangaren ma'aikata.

Sanarwar ta bayyana cewa matakin zai taimaka wajen gina tsarin aikin gwamnati mai ladabi, koshin lafiya da inganci, wanda hakan zai taimaka wajen aiwatar da manufofin ci gaban kasa yadda ya kamata.

Gwamnati ta bada hutun kirismeti a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta ba da hutun kwanaki biyu domin bai wa 'yan Najeriya damar gudanar da bukukuwan kirismetin 2025.

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Alhamis, 25 ga Disamba, da Jumma’a, 26 ga Disamba, 2025 a matsayin ranakun hutu domin bikin kirisimeti.

Baya ga haka kuma, gwamnatin ta ayyana ranar Alhamis, 1 ga watan Janairu, 2026 a matsayin ranar hutun sabuwar shekara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262