Dan Majalisar Amurka Ya Shiga Cocin Najeriya, Ya Yi Magana kan Kisan Kiristoci
- Amurka ta ce ba za ta tura sojoji zuwa Najeriya ba duk da sanya kasar cikin jerin kasashe masu damuwa ta musamman (CPC)
- ‘Yan majalisa Amurka sun ce an dauki matakin sanya Najeriya a jerin CPC domin matsin lamba ta diflomasiyya, ba don yaki ba
- Dan majalisar Amurka, Bill Huizenga ya ziyarci wata coci a Abuja, inda ya ba da tabbacin kawo karshen kisan da ake yi masu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Amurka ta ce ba ta da shirin tura sojoji zuwa Najeriya, duk da matakin da ta dauka na sanya kasar cikin jerin kasashe masu matsala (CPC) saboda rashin tsaro da ‘yancin addini.
Wasu ‘yan majalisar tarayyar Amurka, wadanda suka kai ziyara Najeriya domin tantance halin tsaro da ‘yancin addini, suka bayyana hakan a wani taron manema labarai da suka gudanar a Abuja.

Source: Getty Images
‘Yan majalisar Amurka sun yi karin haske
Tawagar 'yan majalisar ta kunshi Bill Huizenga, tare da Michael Baumgartner, Keith Self, da Jefferson Shreve, in ji rahoton Arise News.
Huizenga ya ce, “Najeriya na bukatar taimako, amma hakan ba yana nufin tura sojojin Amurka ba. Sanya Najeriya cikin jerin CPC hanya ce ta karfafa daukar mataki, ba shirin tura sojoji ba.”
‘Yan majalisar sun bayyana cewa sanya kasashe a jerin kasashe masu matsala ya samo asali ne daga yawaitar tashin hankali da ke shafar al’ummomi na kowane addini, musamman a yankin Middle Belt, inda suka ce ana ganin wasu hare-hare na da nasaba da dalilai na addini.
Wani daga cikin 'yan majalisar ya ce
“Abu ne da ba za a amince da shi ba cewa Musulmi ko Kirista na fuskantar irin wannan tashin hankali. Kare rayukan ‘yan kasa na kowane addini nauyi ne da ya rataya a wuyan gwamnatin Najeriya.”

Kara karanta wannan
An ware Musulmi a gefe da Najeriya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar $2bn da Amurka
Matsalolin tsaro a shiyyoyi daban daban
‘Yan majalisar sun bambanta matsalar ta’addanci a Arewa maso Gabas, wadda ke da alaka da Boko Haram da makamantansu, da rikice-rikicen kabilanci ko na addini a wasu yankuna kamar Filato da Benue.
“Akwai bambancin yanayi daga yanki zuwa yanki. Dabarar da za ta yi aiki a Borno ba lallai ta yi aiki a Filato ko Benue ba,” in ji wani dan majalisar.
Duk da kin tura sojoji, Amurka ta ce za ta kara mayar da hankali kan tallafin jin kai, hadin gwiwar diflomasiyya, da gina karfin hukumomi, in ji rahoton This Day.

Source: Twitter
Dan majalisar Amurka ya shiga coci a Abuja
Dan majalisar Amurka, mai wakiltar mazabar Michigan, Bill Huizenga, ya ziyarci Lighthouse CRC da ke Abuja, inda ya ce "na ziyarci 'yan uwana na addini."
Bill Huizenga ya rubuta a shafinsa na X cewa:
"Kiristoci a Najeriya na ci gaba da gudanar da addininsu duk da hare-haren da suke fuskanta, kama daga kisa da hana su sukunin gudanar da addini.
"Ni da wasu 'yan majalisa da muka kawo wannan ziyara na ci gaba da aiki don kawo karshen matsalar nan. Za mu ci gaba da tattaunawa da Amurkawa da gwamnatin Najeriya da ma shugabannin addini don kawo karshen kisan da ake yi wa Kiristoci da tsirarun Musulmi."
An fadawa Amurka abin da ba ta sani ba
A wani labari, mun ruwaito cewa, tsohon kakakin majalisar wakilai kuma tsohon gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya magantu kan matsalar tsaro.
Tambuwal ya shaidawa Amurka cewa ‘yan ta’adda ba sa girmamawa ko wakiltar kowane addini, yana mai cewa makiyan al’umma ne kawai da ke neman inda za su kai hari.
Ya bayyana halin tsaro a Najeriya a matsayin “mai matuƙar tayar da hankali,” inda ya gargadi shugabanni da kuma al’ummar duniya da su guji siyasantar da tsaron Najeriya.
Asali: Legit.ng

