Kasar Amurka Ta Yanke Matsaya game da Maganar Turo Dakarun Sojoji Najeriya

Kasar Amurka Ta Yanke Matsaya game da Maganar Turo Dakarun Sojoji Najeriya

  • ’Yan majalisar dokokin Amurka sun bayyana cewa sanya Najeriya a CPC ba shiri ba ne na turo sojoji, mataki ne na matsin diflomasiyya domin kawo gyare-gyare
  • Sun ce matakin ya samo asali ne daga yawaitar tashin hankali da ke shafar al’ummomi masu addinai daban-daban, musamman a yankin Arewa ta Tsakiya
  • Majalisar ta jaddada cewa Amurka na son kara hadin gwiwa da Najeriya ta hanyoyin jin-kai da karfafa hukumomi, ba ta fannin soja ba kamar yadda ake fada a baya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa ba ta da shirin tura sojojinta zuwa Najeriya, duk da sanya kasar a CPC kan batun ’yancin addini da tsaro.

’Yan majalisar dokokin Amurka daga jam’iyyun Republican da Democrat ne suka bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Abuja, bayan wata ziyara da suka kai domin duba halin tsaro da batun ’yancin addini a Najeriya.

Kara karanta wannan

'Shirya komai aka yi': An 'gano' yadda rashin tsaro ya fara a Najeriya

Bola Ahmed Tinubu, Donald J Trump
Shugaba Bola Tinubu da Donald Trump na Amurka. Hoto: Bayo Onanuga|The White House
Source: Getty Images

Arise News ta wallafa cewa sun ce manufar CPC ita ce karfafa gyare-gyare da daukar matakai ta hanyar tattaunawa da hadin gwiwa, ba amfani da karfin soja ba.

Dalilin Amurka na sanya Najeriya cikin CPC

Shugaban tawagar, dan majalisa Bill Huizenga, ya ce Najeriya na bukatar taimako wajen magance matsalolin tsaro, amma hakan ba ya nufin shigowar sojojin Amurka.

Ya bayyana cewa CPC hanya ce ta matsa lamba domin a dauki matakai na gyara, yana mai jaddada cewa tashin hankali da ake samu ya shafi Musulmi da Kiristoci baki daya.

A cewarsa, kare rayuka da dukiyoyin ’yan kasa na kowane addini nauyi ne da ya rataya a wuyan gwamnatin Najeriya.

Bambancin matsalolin tsaron Najeriya

’Yan majalisar sun bambanta matsalolin ta’addanci a Arewa maso Gabas, wadanda ake alakanta da Boko Haram da makamantansu, da rikice-rikicen da ke da alaka da addini ko kabilanci a wasu yankuna.

Kara karanta wannan

Za a fara alkunut, malamai sun yi wa Amurka martani kan Shari'a da Hisbah

Sahara Reporters ta rahoto sun ce kowanne yanki na da halin da yake ciki, don haka dabarar da ta dace da Borno ba lallai ta yi aiki a Plateau ko Benue ba.

Wannan bambanci, a cewarsu, na bukatar tsare-tsare daban-daban da suka dace da yanayin kowane yanki na Najeriya.

Tasirin jefa Najeriya a cikin CPC

Tawagar ta ce sanya Najeriya cikin CPC ya riga ya haifar da tattaunawa tsakanin jami'an gwamnatin kasar, lamarin da suka bayyana a matsayin abu mai kyau.

Sun jaddada cewa matakin ba kokarin kawo nakasu ba ne ga Najeriya, illa kira ne na daukar mataki, yin gyare-gyare da kuma inganta kariyar ’yancin addini.

Tawagar Amurka a Najeriya
Wasu 'yan majalisar Amurka tare da Nuhu Ribadu. Hoto: Riley Moore
Source: Twitter

Sun kara da cewa matsayin CPC ba na dindindin ba ne, kuma ana iya duba shi idan aka samu ci gaba mai ma'ana a kasar.

Kasar Amurka ta janye jakadanta a Najeriya

A wani labari, kun ji cewa gwamnatin Amurka ta sanar da janye jakadanta a Najeriya, Richard Mills a wani sauyi da ta yi.

Shugaba Donald Trump ne ya dauki matakin yayin da ya ke sauye-sauyen diflomasiyya a kasashe da dama na duniya.

Baya ga Najeriya, Donald Trump ya janye jakadun Amurka a kasashen Afrika 15, wasu kasashen Turai da yankin Asia.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng