Malamin Musulunci, Sheikh Guruntum Ya Yi Nasiha a Kayar da Masu Mulki a 2027
- Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum ya ce ‘yan siyasa sun riga sun fara shirye-shiryen zaben 2027, inda ya bukaci jama’a su maida hankali a ranar kada kuri’a
- Malamin ya bayyana cewa zanga-zanga ba za ta tilasta wa masu sauka daga mukamansu ba, yana mai cewa hanya mafi dacewa ita ce kayar da su a zabe
- Ya kuma gargadi jama’a kan karbar kudi daga ‘yan siyasa, yana mai cewa kudin yaudara ne da ke lalata makomar zabe ba wata fa'ida da za a samu daga hakan ba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum ya yi kira ga al’umma da su shirya tun daga yanzu domin zaben 2027, yana mai cewa lokaci ya yi da za a daina dogaro da surutai ko matakan wucin-gadi wajen fuskantar ‘yan siyasa.
A cewarsa, babban makamin da jama’a suke da shi shi ne kuri’a, kuma idan aka yi amfani da ita yadda ya kamata, za ta iya kawar da azzalumai daga madafun iko.

Source: Facebook
Malamin ya bayyana hakan ne a wani bidiyo da ya wallafa a Facebook, inda ya ce a halin da ake ciki ‘yan siyasa sun fara shirya dabarunsu, yayin da mutane da dama ke jiran ranar zabe kawai domin daukar mataki.
Kiran Ahmad Guruntum kan zabe a Najeriya
Sheikh Guruntum ya yi karin haske kan batun zanga-zanga, inda ya ce zanga-zanga ba za ta tilasta wa ‘yan siyasa sauka daga kujerunsu ba.
Ya ce ko dan majalisar jiha ba sauki ba ne a cire shi daga kujerarsa saboda zanga-zanga, balle a zo maganar gwamna ko manyan shugabanni.
A saboda haka, ya ce bai dace a mayar da hankali kan zanga-zanga a matsayin hanya ta sauya shugabanci ba a kasar nan.
Malamin ya jaddada cewa hanya mafi muhimmanci ita ce kada a bar azzalmi ya sake cin zabe. Ya ce idan aka kayar da shi a akwatin zabe, wannan shi ne sauke shi na gaskiya kuma bisa doka.
Darasi kan rikicin Natasha da Akpabio
Sheikh Guruntum ya yi ishara da misalan da suka faru a majalisa, ya ce sau da yawa ana iya ganin yadda ake hukunta dan siyasa idan ya taba manyan mutane masu karfi.
Malamin da ke zaune a garin Bauci ya kara da cewa amma idan 'dan majalisa ya cutar da mazabarsa ko jama’arsa, babu abin da zai same shi.
A cewarsa, wannan darasi ne da ya kamata jama’a su fahimta, domin yana nuna cewa idan dan siyasa ya taba manyan ana iya lababtar da shi, amma ana iya kyale shi idan ya taba mutanensa.

Source: Facebook
Duk da bai kama sunan kowa ba, saboda haka, ya bukaci al’umma da su dauki zabe a matsayin lokaci mafi muhimmanci na yanke hukunci kan makomar 'yan siyasa.
Nasiha kan karbar kudi daga ‘yan siyasa
Dangane da batun karbar kudi, Sheikh Guruntum ya ce ‘yan siyasa suna shirin zaben 2027 ne ta hanyar tara kudi domin raba wa jama’a. Ya ce wannan dabara ce da aka saba amfani da ita domin yaudarar masu zabe.
Ya jaddada cewa bai kamata a karbi kudi da sunan za a zabi wani da ya cancanta ba. A cewarsa, babu wata hujja da za ta sa a karbi kudi daga dan siyasa mara cancanta.
Malamin ya bukaci jama’a da su yi watsi da duk wanda bai cancanta ba, ba tare da la’akari da abin da zai bayar ba a lokacin zabe
Majalisa ta gyara dokokin zabe a Najeriya
A wani labarin, mun kawo muku cewa majalisar dokokin Najeriya ta amince da wasu gyararraki a harkokin zaben kasar nan.
'Yan majalisar sun nuna amincewa da a yi daurin shekaru ga jami'an INEC da aka samu da laifi wajen magudin zabe.
Baya ga haka, majalisar dokoki ta yi gyara game da shari'ar da ta shafi jam'iyyu da cancantar 'yan takara a gyaran da ta yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


