Yadda Donald Trump Ya Jawo wa Najeriya Asarar Kusan Naira Tiriliyan 1

Yadda Donald Trump Ya Jawo wa Najeriya Asarar Kusan Naira Tiriliyan 1

  • Rahotannin NBS sun nuna faduwar darajar kayayyakin da Najeriya ta fitar zuwa Amurka a watanni tara na 2025, yayin da shigo da kaya daga can ya ninku fiye da sau biyu
  • Sabon tsarin harajin da gwamnatin Donald Trump ta aiwatar ya shafi kayayyakin da ba na man fetur ba, lamarin da ya rage bukata daga masu shigo da kaya a Amurka
  • Sauyin yanayin kasuwanci ya jawo gibin ciniki mai yawa, inda Amurka ta fice daga cikin manyan kasashen da Najeriya ke fitar da kaya zuwa gare su a tsakiyar 2025

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Najeriya ta fuskanci babbar asara a bangaren fitar da kaya zuwa Amurka bayan aiwatar da sabon tsarin haraji da gwamnatin Donald Trump ta bullo da shi.

Kara karanta wannan

Saukin da Dangote ya yi ya jawo 'yan kasuwa sun fara rage farashin fetur a Najeriya

Binciken cibiyar kididdiga ta kasa (NBS) ta nuna raguwar kudin da aka samu daga fitar da kaya a watanni tara na farkon 2025.

Bola Tinubu da Donald Trump
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya da Donald Trump na Amurka. Hoto: Bayo Onanuga|The White House
Source: Getty Images

Punch ta ce bayanan kasuwancin waje na NBS sun nuna cewa daga Janairu zuwa Satumba na 2025, darajar kayayyakin da Najeriya ta fitar zuwa Amurka ya ragu sosai idan aka kwatanta da makamancin lokacin na 2024.

Donald Trump ya jawo wa Najeriya asara

Nazarin alkaluman Q1 zuwa Q3 na 2024 da 2025 ya nuna cewa Najeriya ta fitar da kaya da darajarsu ta kai N3.65tn zuwa Amurka a watanni tara na 2025, kasa da N4.59tn da aka samu a 2024.

BBC Hausa ta rahoto cewa NBS ta ce wannan na nufin raguwar fitar da kayan Najeriya ya yi kasa da kashi 20.5 cikin 100, wato asarar kusan N940.98bn.

A gefe guda kuma, shigo da kaya daga Amurka ya tashi daga N3.01tn zuwa N6.80tn, karin da ya kai kashi 125.5 cikin 100.

A cewar NBS, wannan ya bar Najeriya da gibin ciniki da ya kai kusan N3.15tn, sabanin ribar ciniki ta N1.57tn da aka samu a 2024.

Kara karanta wannan

Rukunin 'yan Najeriya da takunkumin Trump na hana shiga Amurka zai shafa

Tasirin harajin Trump ga Najeriya

Raguwar ta zo ne a daidai lokacin da Amurka ta fara aiwatar da tsarin haraji, inda Shugaba Donald Trump ya rattaba hannu kan umarnin kara harajin Najeriya daga kashi 14 zuwa 15 cikin 100.

Legit Hausa ta rahoto cewa umarnin Trump da aka fitar a karshen watan Yuli, ya fara aiki ne a ranar 7, Agusta, 2025.

Yusuf Tuggar na Najeriya
Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar. Hoto: @YusufTuggar
Source: Twitter

Duk da man fetur bai shiga cikin harajin a wasu lokuta ba, ya fi shafan kayayyakin da ba na mai ba, lamarin da ya rage kwarin gwiwar masu shigo da kaya a Amurka.

Malaman Kano sun yi wa Amurka martani

A wani labarin, kun ji cewa malaman addinin Musulunci a Kano sun yi wa gwamnatin Amurka martani kan neman soke shari'a da Hisbah.

Wasu 'yan majalisar Amurka ne suka bukaci a soke shari'ar Musulunci a Najeriya da hukumar Hisbah a kwanakin baya.

Sai dai malaman sun ce shari'ar Musulunci da hukumar Hisbah lamari ne da ya shafi Musulmai kuma ba ja da baya a kansu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng