NBS ta fitar da jerin basusukan da ake bin kowace jihar Najeriya yayin da ya kai N4.2tn
- Hukumar kididdiga ta kasa ta fitar da bayanan bashin da ake bin kowace jiha
- A cewar NBS, Legas ce jihar da ta fi kowacce bashi a kasar
- A halin yanzu, jihar Jigawa ce ke da mafi karancin bashi a kasa
Ana bin jihohin Najeriya ciki har da Babban Birnin Tarayya bashin N4.2tn a cewar Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS).
Da wannan sabon rahoto, Jihar Legas ce ke da kaso 12.15 na bashin har zuwa karshen 2020 yayin da jihar Jigawa ke da mafi karancin bashin a wannan rukuni da kashi 0.74 bisa dari.
KU KARANTA KUMA: 'Yan Najeriya sun kirkiri fasahar bin diddigin 'yan bindiga a duk inda suke
Ga jerin jihohin da bayanan bashin su na yanzu.
Abia - N89.12bn (2.13 per cent)
Adamawa - N98.9bn (2.36 per cent)
Akwa Ibom - N230.8bn
Anambra - N59.97bn
Bauchi - N102.8bn
Bayelsa - N144.13bn
Benue - N126.12bn
Borno - N89.05bn
Cross River - N163.16bn,
Delta - N248.45bn
Ebonyi - N44.21bn
Edo - N80.78bn
Ekiti - N84.97bn
Enugu - N68.09bn
Gombe - N84.72tn
Imo - N150.2bn
Jigawa - N30.97bn
Kaduna - N68.75bn
Kano - N116.93bn
Katsina - N48.03bn
Kebbi - N56.81bn
Kogi - N68.09bn
Kwara - N63.63bn
Lagos - N508.78bn
Nasarawa - N59.4bn
Niger - N66.77bn
Ogun - N153.49bn
Ondo - N74.66bn
Osun - N134.11bn
Oyo - N94.5bn
Plateau - N137.8bn
Rivers - N266.9bn
Sokoto - N42.36bn
Taraba - N106.04bn
Yobe - N54.87bn
Zamfara - N98.02bn
FCT - N69.5bn
KU KARANTA KUMA: Ina shirin mayar da rundunar sojin Najeriya mai matukar karfin iko, Attahiru
A wani labarin, babban jagoran jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bada shawarar yadda za ayi maganin fatara, a farfado da tattalin Najeriya.
Jaridar Daily Trust ta rahoto Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya na cewa ya kamata gwamnatin tarayya ta saki kudi da nufin yakar talauci da rashin aikin yi.
Bola Tinubu ya ce akwai bukatar shugabanni masu rike da madafan iko da ‘yan majalisa su hada-kai, a samu a ga yadda za a kawar da talaucin da ake fama da shi.
Asali: Legit.ng