Musulmai Sun Yi Rashi: Shugaban Kotun Shari'ar Musulunci Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Musulmai Sun Yi Rashi: Shugaban Kotun Shari'ar Musulunci Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Gwamna Caleb Mutfwang ya yi alhinin rasuwar mukaddashin shugaban alkalan kotun shari'ar musulunci na jihar Filato, Mai shari’a Umar Ibrahim
  • Mutfwang ya jagoranci tawagar gwamnatin Filato sun je ta'aziyya gidan marigayin da ke karamar hukumar Jos ta Kudu
  • Mai girma gwamnan ya bayyana marigayi Malam Umar a matsayin mutum nagari, wanda rasuwarsa ta shafi dukkan musulmai

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Plateau, Nigeria - Rahotanni sun tabbatar da labarin cewa Mukaddashin Shugaban Alƙalan Kotun Shari'ar Musulunci na jihar Filato, Mai shari’a Umar Ibrahim ya rasu.

Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, ya bayyana rasuwar babban alkalin a matsayin babban rashi mai matuƙar zafi ga jihar da al’ummar Musulmi baki ɗaya.

Gwamna Caleb Mutfwang.
Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato yana jawabi a fadar gwamnati Hoto: Caleb Mutfwang
Source: Facebook

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan marigayin a gidansa da ke Bukuru, a Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ziyarar Tinubu: Gwamnatin Bauchi ta aika sako ga mutanen jihar

Gwamnan jihar Filato ya je ta'aziyya

A cewar wata sanarwa da Darakta na Yaɗa Labarai da Harkokin Jama’a ga Gwamna, Gyang Bere, ya fitar, Mutfwang ya bukaci iyalai da sauran musulmi su miƙa lamurra gaba ɗaya ga nufin Allah Maɗaukakin Sarki.

“Mun riga mun fara shirye-shiryen bikin murna da shagalin ritayarsa, amma Allah cikin hikimarsa ya tsara akasin haka.
"Wannan babban rashi ne mai raɗaɗi ga Jihar Filato da kuma al’ummar Musulmi gaba ɗaya,” in ji gwamnan.

Mutfwang ya yabi halayen marigayin

Ya bayyana marigayin a matsayin alkali mai tsoron Allah, nagarta da ladabi, wanda aikinsa ya kasance cike da adalci, gaskiya da sadaukarwa ga hidimar al’umma.

“Rayuwarsa ta kasance abin koyi wajen bin doka da gaskiya. Halayyarsa ta gari ta sa ya samu girmamawa da ƙauna, tare da taimaka wa rayuwar mutane da dama ta hanya mai kyau,” in ji Mutfwang.

Gwamna Mutfwang ya yi addu’ar Allah ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, ya kuma sanya shi cikin Aljannatul Firdaus.

Kara karanta wannan

An yi babban rashi: Tsohon Sanata a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya

Haka kuma ya yi kira ga al’ummar jihar da su rungumi ƙauna, gaskiya, yafiya da zaman lafiya, yana mai cewa waɗannan su ne tubalan gina al’umma nagari.

Gwamna Mutfwang.
Gwamna Caleb Mutfwanga na jihar Filato Hoto: Caleb Mutfwang
Source: Facebook

Iyalan alkalin sun gode wa gwamnan Filato

Da yake jawabi a madadin iyalan marigayin, Alhaji Ahmed Ibrahim ya gode wa gwamnan da tawagarsa bisa nuna tausayi da goyon baya a wannan lokaci na jimami.

“Duk da radadin wannan rashi yana da girma, muna samun kwanciyar hankali daga addu’o’i, kyawawan shaidu da ake fada game da marigayin, waɗanda ke nuna cewa ya rayu rayuwa mai amfani,” in ji shi.

Ya kuma gode wa Sarkin Wase, jami’an Kotun Shari’ar Musulunci, da sauran masu jaje bisa goyon bayan da suka nuna, tare da roƙon a ci gaba da yi wa iyalan marigayin addu’a, cewar Daily Post.

Malamin Izala a Gombe ya rasu

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar Izalah (JIBWIS) reshen Gombe ta sanar da rasuwar daya daga cikin shugabanninta na kungiyar a Kwamin Yamma.

Shugaban Jama'atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah a jihar Gombe, Alhaji Salisu Muhammad Gombe ya tura sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin.

Kumgiyar Izala ta bayyana alhini kan rashin jajirtaccen malamin Alhaji Abdullahi Barde wanda ya ba da gudunmawa sosai wajen yada addinin musulunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262