‘Babu Tausayi’: Tinubu Ya kuma Yin Albishir ga ’Yan Najeriya game da Ta’addanci
- Shugaba Bola Tinubu ya sha alwashin ci gaba da yaki da ta'addanci domin tabbatar da samun zaman lafiya
- Tinubu ya nuna cewa babu sassauci ga ’yan ta’adda, ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane a fadin kasar
- Shugaban ya ce gwamnati za ta tabbatar da daidaiton tattalin arziki da tsaro mai ɗorewa a Najeriya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2026 da ya ba tsaro muhimmanci.
Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta nuna tausayi ko sassauci ga ’yan ta’adda, ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane ba.

Source: Facebook
Alkawarin Bola Tinubu game da kawo karshen ta'addanci
Rahoton Punch ya ce Tinubu ya fadi haka ne a zaman majalisar hadin guiwa yayin gabatar da kasafin kudi.

Kara karanta wannan
Duk da samun jihohi 28, Shugaba Tinubu ya hango matsalar da ta tunkaro jam'iyyar APC
Tinubu ya ce za a tunkari laifuffukan tayar da hankali da tsattsauran mataki kan masu daukar nauyinsu a fadin ƙasar.
Ya ce gwamnati ta sake fasalin tsarin tsaron ƙasa gaba ɗaya domin magance matsalolin tsaro da ke addabar Najeriya.
A cewar Shugaban Ƙasa, an ware Naira tiriliyan 5.41 ga sashen tsaro da kare ƙasa, wanda shi ne mafi girman kaso a cikin kasafin.
Wannan shi ne karo na uku a jere da tsaro ke samun fifiko tun bayan fara gabatar da kasafin gwamnatinsa a shekarar 2023.
Tinubu ya ce ware kuɗin tsaro na nuna ƙudirin gwamnatinsa na gina ƙasa bisa tubalin tsaro.
Ya jaddada cewa duk kuɗin tsaro za su kasance bisa tsari da sakamako mai kyau, musamman wajen ƙarfafa sojoji da sauran hukumomin tsaro da kayan aiki na zamani.
Shugaban ya ce:
“Ba za mu nuna sassauci ba. Za mu yi amfani da sabon tsari kan masu aikata laifi. Za mu ɗauki mataki mai tsauri kan duk wanda ke aikata ko tallafa wa ta’addanci, ’yan bindiga, garkuwa da mutane da sauran manyan laifuka.”

Source: Facebook
Hanyoyin yaki da ta'addanci da aka kirkiro
Tinubu ya bayyana cewa gwamnati ta ƙirƙiri sabon tsarin yaƙi da ta’addanci, wanda ya dogara da haɗin gwiwar umarni, tattara bayanan sirri, kwanciyar hankalin al’umma da yaƙin da ’yan tawaye.
A karkashin sabon tsarin, duk wata ƙungiya mai ɗauke da makamai da ba ta ƙarƙashin ikon gwamnati za a ɗauke ta a matsayin ’yan ta’adda, cewar Vanguard.
Tinubu ya ce ’yan bindiga, ’yan daba, ƙungiyoyin asiri masu tayar da hankali, ƙungiyoyin da ke fakewa a dazuka, da kuma cibiyoyin laifi masu alaƙa da ƙasashen waje za su zama halastattun muradun hare-haren jami’an tsaro.
Kananan hukumomi: Tinubu ya yi wa gwamnoni barazana
Mun ba ku labarin cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi barazana ga gwamnoni game da 'yancin kananan hukumomi.
Bola Tinubu ya bukaci gwamnonin su aiwatar da hukuncin Kotun Koli wanda ya umarci a sakarwa kananan hukumomi mara.
Shugaban kasar ya fito kai tsaye ya gayawa gwamnonin matakin da zai dauka idan har ba su aiwatar da hakan ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng