Za a Fara Alkunut, Malamai Sun Yi wa Amurka Martani kan Shari'a da Hisbah

Za a Fara Alkunut, Malamai Sun Yi wa Amurka Martani kan Shari'a da Hisbah

  • Kungiyar malamai da kungiyoyin Musulunci a Kano ta soki tsoma bakin gwamnatin Amurka kan batun Shari’a da ayyukan Hisbah a Najeriya
  • Malaman sun ce Shari’a da Hisbah hakki ne na Musulmi bisa doka da kundin tsarin mulkin Najeriya, kuma ba ja da baya a kansu kwata-kwata
  • Kungiyar ta yi gargadi da cewa matsin lamba daga kasashen waje na iya dagula zaman lafiya tsakanin mabiya addinai da ke zaune a Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Kungiyar Malamai a Kano ta yi kakkausar suka ga gwamnatin Amurka da majalisar dokokinta kan abin da ta kira tsoma baki cikin harkokin cikin gida na Najeriya.

Malaman sun yi magana ne game da Shari’a da ayyukan Hukumar Hisbah a wasu jihohin Arewa bayan Amurka ta caccake su.

Kara karanta wannan

Manyan Arewa sun ziyarci CAN da JNI domin hada kan Musulmi da Kirista

Shugaban Amurka, Donald Trump
Donald Trump da wasu jami'an Hisbah a Najeriya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tashar Arise News ta ce kungiyar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da Dr Sa’idu Ahmad Dukawa ya rattabawa hannu a madadinta.

A cewar sanarwar, yunkurin yana da nufin rage ‘yancin addini da kuma hana aiwatar da ka’idojin addini, ciki har da kira da ake zargin an yi na soke Shari’a da rusa Hukumar Hisbah.

Martanin Malamai kan Shari'a da Hisbah

Malaman Musulunci sun bayyana cewa irin wannan yunkuri ba kawai raina ‘yancin kai da martabar Najeriya ba ne, har ila yau yana iya zama barazana ga zaman lafiya da ke tsakanin Musulmi da Kiristoci a kasar.

Sanarwar ta ce wannan mataki na nuna rashin mutunta dimokuradiyya, tare da jaddada cewa al’ummar Najeriya na da ikon tsara rayuwarsu bisa dokoki da dabi’un da suka zaba.

The Sun ta rahoto kungiyar ta ce duk wani yunkuri daga kasashen waje na tilasta wa Najeriya soke dokokin da suka shafi addini na iya janyo sabani da rashin fahimtar juna a tsakanin al’umma.

Kara karanta wannan

Kasar Amurka ta fitar da sabon gargadi game da 'yan Najeriya

Matsayin Shari’a da Hisbah a Najeriya

Malaman sun yi watsi da duk wata kira da ke bukatar gwamnatin Najeriya ta soke Shari’a ko rusa Hukumar Hisbah, suna mai cewa wadannan tsare-tsare suna da tushe a cikin dokokin jihohi da majalisun dokoki suka amince da su.

A cewarsu, Shari’a hakki ne na Musulmi bisa kundin tsarin mulki da kuma koyarwar addini, kuma ana aiwatar da ita ne kawai a kan Musulmi a Kano da sauran sassan Najeriya da suka zabe ta.

Dakarun hukumar Hisbah a jihar Kano
Wasu 'yan Hisbah a bakin aiki a Kano. Hoto: Imrana Mohammed
Source: Facebook

Kungiyar ta jaddada cewa Hukumar Hisbah ta taka muhimmiyar rawa wajen inganta zaman lafiya, kare wuraren ibada ciki har da masallatai da coci-coci, da kuma taimakawa hukumomin tsaro a lokutan da ake fama da tashin hankali.

Barazanar Amurka: Za a fara alkunut a Najeriya

A karshe, kungiyar ta bukaci malaman Musulunci a fadin kasar nan da su fara alkunuti na musamman domin neman taimakon Allah kan matsalolin tsaro da dukkan barazanar da ke neman rusa zaman lafiyar kasa.

Kara karanta wannan

Barau ya bukaci a dauki matakin gaggawa game da harin 'yan bindiga a Kano

Haka kuma, ta yi kira ga Musulmi da su tuba, su rike kyawawan dabi’un Musulunci, tare da ci gaba da mara wa cibiyoyin addini da ke aiki bisa doka baya, domin samun zaman lafiya mai dorewa a Najeriya.

Za a fara duba watan Rajab a Najeriya

A wani labarin, mun kawo muku cewa mai alfarma Sarkin Musulmi ya fitar da sanarwar fara duba watan Rajab a Najeriya.

Sarkin Musulmi ya bayyana cewa a ranar Asabar, 20 ga Disamban 2025 za a fara duba watan bakwai na kalandar Musulunci.

Sanarwar ta bukaci duk wanda ya ga watan ya sanar da hakimi ko dagaci mafi kusa da shi domin hukumomi su samu labari.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng