Bangarori 4 da Tinubu Zai Fi Kashewa Kudi a Kasafin 2026
Shugaban Kasa Bola Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2026 na Naira tiriliyan 58.18 a zaman haɗin gwiwa na Majalisar Ƙasa a ranar Juma’a, 19 ga watan Disamba, 2025.
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Kasafin kudin shekarar 2026 da Shugaban Kasa ya gabatar ya jaddada muhimman manyan bangarori huɗu: tsaro, ilimi, lafiya da ababen more rayuwa.
A cewar Bola Tinubu, waɗannan fannoni suna da alaƙa da juna, kuma su ne ginshiƙin hanyar Najeriya zuwa haɓakar tattalin arziƙi mai dorewa, kamar yadda aka wallafa a shafin X na Presidency Nigeria.

Source: Facebook
Legit ta tattaro wasu manyan bangarori da kasafin 2026 ya fi mayar da hankali a kansu, yayin da Tinubu ya bayyana muhimmancinsu ga ci gaban kasa.

Kara karanta wannan
Bola Tinubu ya kafa sabon tsarin tsaro, ya ayyana kungiyoyi 6 a matsayin 'yan ta'adda
Abubuwan da za a fi kashewa kudi a 2026
1. Tsaro
A kasafin kuɗin 2026, tsaro da bayar da kariya ga rayukan 'yan Najeriya sun samu mafi girman kaso, inda aka ware Naira tiriliyan 5.41 ga bangaren shi kadai.
Shugaba Tinubu ya jaddada cewa tsaro shi ne tubalin ci gaban tattalin arziƙi da haɗin kan al’umma. A cewarsa, gwamnatinsa ta fara sake fasalin tsarin tsaron ƙasa.
Shugaban Kasa ya ce a sabon tsarin da gwamnati ta bijiro da shi, ta mayar da hankali kan zamani, ayyukan da ke dogara da bayanan sirri, da amfani da fasahohin sa ido.

Source: Facebook
Ya bayyana cewa kasafin ya haɗa da kuɗin ƙarfafa ayyukan sojoji, inganta ma’aikata, da sayen na’urori da kayan aikin zamani domin tunkarar barazanar tsaro.
Babban ɓangare na wannan shiri shi ne aiwatar da sabon tsarin yaƙi da ta’addanci na ƙasa, wanda aka tsara domin magance ta’addanci, ‘yan fashi, garkuwa da mutane, da sauran laifuffuka.
Ya ce:
“Za mu zuba jari a tsaro tare da cikakken bin diddigin sakamakon kudin da aka zuba, domin dole ne kuɗin tsaro su haifar da sakamakon tsaro.”
A ƙarƙashin sabon tsarin, duk wata ƙungiya ko mutum mai ɗauke da makami da ke aiki ba tare da izinin gwamnati ba za a ɗauke shi a matsayin ɗan ta’adda.
Wannan ya haɗa da ‘yan fashi, mayaƙan ƙungiyoyi, ‘yan bindiga, ƙungiyoyin asiri masu, masu makamai a dazuka, da mayaƙan haya masu alaƙa da ƙasashen waje.
Haka kuma, duk wanda ke tallafa masu ta hanyar ba su kuɗi, ba su mafaka ko goyon baya, ciki har da ’yan siyasa, shugabannin al’umma, sarakunan gargajiya da shugabannin addini, za a ɗauke su a matsayin ’yan ta’adda.
2. Ilimi da lafiya
Baya ga tsaro, kasafin 2026 ya ba da muhimmanci sosai ga ci gaban ɗan Adam, inda Ilimi da lafiya suka samu N6tr a hade, wato N3.52tr ga ilimi, sai kuma N2.48tr ga lafiya.
A fannin ilimi, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta faɗaɗa samun ilimi a manyan makarantu ta hanyar Asusun Rancen Ilimi na Najeriya.
Ya bayyana cewa wannan shiri ya taimaka, ta hanyar tallafa wa ɗalibai fiye da 418,000 tare da haɗin gwiwar manyan makarantu 229 a faɗin ƙasar.

Source: Facebook
Ya ƙara da cewa kuɗin zai tallafa wa horon sana’o’i da bunƙasa ƙwarewa, ganin alaƙar ƙwarewa da samun aiki da kuma haɓakar ƙasa.
A fannin lafiya, wanda ya kai kusan kashi 6 cikin 100 na kasafin, da nufin kara yawan ababen more rayuwar lafiya, faɗaɗa samun kulawa a manyan asibitoci, da rage yawan cututtuka a ƙasar.
Shugaba Tinubu ya kuma bayyana wata tattaunawa ta baya-bayan nan da Gwamnatin Amurka, wacce ta samar da fiye da Dala miliyan 500 a matsayin tallafin kuɗi don ayyukan lafiya na musamman a Najeriya.
Ya tabbatar da cewa za a yi amfani da kuɗin da gaskiya domin inganta lafiyar jama’a da ƙarfafa haɗin gwiwa don ci gaba mai ɗorewa.
3. Abubuwan more rayuwa
Ci gaban ababen more rayuwa da haɓakar tattalin arziƙi sun zama ginshiƙi na uku a kasafin 2026, inda aka ware Naira tiriliyan 3.56.
A fannin noma, Shugaba Tinubu ya jaddada tabbatar da wadatar abinci da tsaron ƙasa. Daga cikin abubuwan da kasafin ya mayar da hankali a wannan bangare akwai kayan noma da injina.
Haka kuma an kara mayar da hankali a kan tsarin ban ruwa mai jure sauyin yanayi, da bunƙasa ajiya, sarrafawa da sauransu.

Source: Facebook
An tsara waɗannan matakai ne domin rage asara bayan girbi, ƙara kuɗin shiga na ƙananan manoma, da kara inganta masana’antar noma.
Ta hanyar ƙarfafa kasuwannin noma da sarkar ƙima, gwamnati na sa ran ƙarfafa juriya ta tattalin arziƙin Najeriya da rage dogaro da shigo da kaya daga waje.
Tinubu ya ce:
“Za mu ɗauki matakai masu ƙarfi don ƙarfafa kasuwannin noma. Samun wadatar abinci tsaron ƙasa ne."
Bola Tinubu ya gabatar da kasafin 2026
A bayan, mun wallafa cewa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2026 ga Majalisar Tarayya a Abuja a zaman haɗin gwiwa na Majalisar Dattawa da ta Wakilai.
Kasafin kuɗin 2026 ya kai Naira tiriliyan 58.18. Fadar Shugaban Ƙasa ta tabbatar da hakan ta hanyar wata sanarwa da mai taimaka wa Tinubu kan harkokin kafafen sada zumunta, Dada Olusegun ya fitar.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa an ware Naira tiriliyan 26.08 domin ayyukan ci gaba, yayin da aka tanadi Naira tiriliyan 15.25 don tafiyar da harkokin gwamnati na yau da kullum.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


