Tsaro ne kan Gaba da Shugaba Tinubu Ya Gabatar da Kasafin Kudin 2026 a Majalisa
- Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kasafin kudin 2026 a zaman hadin gwiwa na Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai yau Juma'a
- Shugaban kasar ya yi bayani dalla-dalla kan yadda Najeriya za ta kashe sama da Naira tiriliyan 58 a shekara mai zuwa watau 2026
- Bangaren tsaro shi ne ya fi samun kaso mafi tsoka a kasafin kudin, wanda aka ware sama da Naira tiriliyan 15 don biyan basussuka
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Kamar yadda aka tsara, Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2026 ga Majalisar Tarayya a Abuja.
Bola Tinubu ya gabatar da kasafin 2026, wanda ake sa ran zai lakuma Naira tiriliyan 58.18 a gaban zaman hadin guiwa tsakanin Majalisar Dattawa da ta Wakilai yau Juma'a.

Source: Twitter
Fadar shugaban kasa ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da mai taimakawa Tinubu kan harkokin soshiyal midiya, Dada Olusegun ya wallafa a shafin X.
Najeriya za ta kashe N58.18trn a 2026
Shugaban kasar ya bayyana cewa an ware Naira tiriliyan 26.08 domin gudanar da ayyukan ci gaba, yayin da aka ware Naira tiriliyan 15.25 a matsayin kudin tafiyar da gwamnati na yau da kullum
Mai girma Bola Tinubu ya ce an kuma sa farashin man fetur a Dala $64.85 kan kowace ganga, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
Tinubu ya ce gwamnati na sa ran samun jimillar kuɗaɗen shiga Naira tiriliyan 34.33 a shekarar 2025, sannan ta tsara kashe kuɗaɗen da suka kai Naira tiriliyan 58.18.
Daga cikin wadannan kudade, Shugaba Tinubu ya ce an ware Naira tiriliyan 15.52 domin biyan wasu daga cikin basussukan da ake bin Najeriya.
"Za a samu gibin ₦23.85trn a kasafin kudin 2026, wanda ke wakiltar kashi 4.28 cikin 100 na karfin tattalin arziki watau GDP," in ji shi.
An gina kasafin ne bisa hasashen samar da gangar man fetur miliyan 1.84 a kowane rana, da kuma musayar kuɗi ₦1,400 kan kowace Dala ɗaya a shekarar 2026.
Tsaro ya samu kaso mafi tsoka a kasafin
A bangaren rabon kuɗaɗen kasafin, tsaro da kare ƙasa ya samu mafi girman kaso na Naira tiriliyan 5.41, yayin da bangaren gina ababen more rayuwa ya samu Naira tiriliyan 3.56.
Sai kuma bangaren harkokin Ilimi da ya ya samu Naira tiriliyan 3.52, da kuma bangaren lafiya, wanda ya samu kason Naira tiriliyan 2.48.
An sanya wa kasafin kuɗin taken “Budget of Consolidation, Renewed Resilience and Shared Prosperity," watau kasafin kara karfafawa, juriya da ci gaban tattalin arziki na bai daya.

Source: Facebook
Wasu kalaman Tinubu a gaban Majalisa
Da yake jawabi ga ‘yan majalisa, Shugaba Tinubu ya jaddada cewa kasafin ba wai kawai jerin lambobin lissafi ba ne, bayanai ne na abubuwan da kasar za ta ba muhimmanci.

Kara karanta wannan
Gwamna Fubara ya fadi biliyoyin da ya tarar a asusun Rivers bayan cire dokar ta baci
Tinubu ya ce:
“Wannqn kasafin kuɗi bayani ne na abubuwan da ƙasa ta fi bai wa muhimmanci. Muna ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da daidaiton tsara dukiyar kasa, gaskiya wajen bashi, da kuma tabbatar da cewa duk kuɗin da ake kashewa yana da amfani ga al’umma.”
Tinubu ya sha alwashin samar da tsaro
A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya jaddada cewa dole ne a tabbatar da kafa 'yan sandan jihohi domin magance matsalar tsaro a Najeriya.
Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne a yayin taron jam’iyyar APC karo na 14 da aka gudanar a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Ya ce kafa irin wannan tsari zai taimaka matuƙa wajen rage matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar, tare da bai wa jihohi damar ɗaukar nauyin kare al’ummominsu
Asali: Legit.ng

