Sarki Ya Haramta Halartar Wurin Ibada saboda Rashin Tsaro a Kogi

Sarki Ya Haramta Halartar Wurin Ibada saboda Rashin Tsaro a Kogi

  • Babban Sarki a Kogi ya kawo mafita kan matsalolin tsaro da ke faruwa a jihar wanda ya yi sanadin asarar rayuka
  • Sarkin Kabba, Oba Solomon Owoniyi tare da CAN a Kabba/Bunu, sun dakatar da dukkan ayyukan coci sakamakon barazanar tsaro
  • CAN ta bukaci coci su bi umarnin domin kare rayuka, tare da ci gaba da addu’o’i, tana mai cewa za a sanar da su idan tsaro ya inganta

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kabba, Kogi - Sarkin Kabba kuma Shugaban Majalisar Gargajiya ta Kabba/Bunu, Oba Solomon Owoniyi ya ba da umarni kan zuwa coci a yankin.

Wannan umarni ya biyo bayan hadin guiwa da CAN inda suka bayar da umarnin dakatar da ayyukan coci gaba ɗaya.

Sarki, CAN sun hana zuwa coci a Kogi
Taswirar jihar Kogi da ke cikin jihohi masu fama da matsalar tsaro. Hoto: Legit.
Source: Original

Kogi: An hana zuwa coci saboda matsalar tsaro

Wata sanarwa daga Shugaban CAN a Kabba/Bunu, Rabaran Kayode Osatuyie, ta ce an cimma matsayar ne bayan taro a fadar Sarki, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Akpabio ya goyi bayan kashe 'yan bindiga masu garkuwa da mutane

An dauki wannan mataki ne bayan samun rahotannin tsaro, ciki har da hare-haren da aka kai coci da gano tarin makamai daga maboyar ‘yan ta’adda.

Sanarwar ta bayyana cewa Sarkin ya ba da umarnin rufe dukkan coci-coci bayan rahoton ingantaccen tsaro kan barazanar hare-haren ‘yan bindiga.

Rabaran Osatuyie ya ce an dauki matakin ne bayan tuntubar shugabannin CAN na jihar, inda aka bukaci coci su yi biyayya domin kare lafiyar jama’a.

Ya kara da cewa ya zama wajibi a ci gaba da addu’o’i domin zaman lafiya a Kabba/Bunu, yana mai cewa za a sanar da coci idan an samu saukin tsaro.

An hana zuwa coci a wani yankin Kogi
Gwamna Usman Ododo na jihar Kogi. Hoto: Alhaji Ahmed Usman Ododo.
Source: Facebook

Gargadin gwamnatin Kogi ga wuraren ibada a jihar

A baya, gwamnatin Kogi ta sanar da gano manyan makamai da alburusai yayin wani hadin gwiwar jami’an tsaro a sassan jihar.

Hakan ya biyo bayan fama da hare-haren yan bindiga da jihar ke yi wanda ya ke jawo asarar rayukan a'umma da dama da kuma dukiyoyin mutane.

Gwamnatin ta kuma gargadi wuraren ibada, musamman na bayan gari, da su guji gudanar da ibada a wuraren da ke fama da matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

Kungiyar CAN ta yi magana da babbar murya ga Tinubu yayin da ake shirin Kirsimeti

A watan da ya gabata, an kai hari cocin Cherubim da Seraphim, yayin da aka kashe masu ibada biyu a cocin ECWA da ke Kiri, cewar rahoton Punch.

Rahotanni sun ce a sabon harin da aka kai a karshen makon jiya, ‘yan bindiga sun afka cocin yayin ibada, inda suka kashe mutane tare da sace kusan masu ibada 20.

Kogi: Ciyaman ya sanya dokar hana fita

An ji cewa Shugaban Karamar Hukumar a Kogi ya kawo hanyoyin dakile matsalolin tsaro da ke damun al'ummarsa a yankin.

Hon. Edibo Peter Mark na karamar hukumar Omala ya kafa dokar hana fita daga ƙarfe 7:00 na dare zuwa 6:00 na safe domin dakile matsalolin tsaro.

Wannan mataki na da nasaba da matsalolin tsaro da ake fuskanta a yankin musamman sace-sacen al'umma wanda ya jawo asarar rayuka da dukiyoyi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.