Matatar Dangote Ta Kawo Tsarin da Zai Kara Sauke Farashin Fetur a Gidajen Mai aNajeriya
- Matatar Dangote ta kara daukar wasu matakai da nufin tabbatar da cewa yan Najeriya sun saya fetur a farashi mai rahusa
- Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan matatar ta zabtare sama da N100 a farashin kowace litar fetur ga 'yan kasuwa
- Matatar ta bukaci gidajen mai daga kowane bangare na kasar nan da su yi rijista da sabon tsarin da ta kawo domin samun sauki da garabasa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagoa, Nigeria - Kwanaki kadan bayan matatar Dangote ta zabtare farashin kowace litar man fetur, ta samar da hanyar da kowane gidan mai zai iya amfani da wannan rangwame.
A makon jiya ne matatar hamshakin dan kasuwa, Aliko Dangote da ke Legas ta sauke farashin man fetur daga N828 zuwa N699, inda ta zabtare N129 lokaci guda.

Source: Getty Images
Tsarin da matatar Dangote ta kawo
Amma a wata sanarwa da kamfanin Dangote Group ya wallafa a X jiya Alhamias, matatar ta yi tayin samar da fetur kan sabon farashi ga kowane gidan mai a kasar nan.
Matatar ta Dangote ta bayyana cewa za ta samar da fetur ga kowane gidan mai ko dan kasuwa da ya yi rijista a wannan tsari a kan farashin N699 kowane lita daya.
Ta gayyaci masu gidajen mai da masu zaman kansu su yi rajista domin cin gajiyar wannan tsari.
A cikin sanarwar, matatar Dangote ta ce:
"Muna kira ga masu gidajen mai da dillalan fetur! Ku yi rajistar gidajen manku yau domin cin gajiyar sabon farashin mu na ₦699 kan kowace lita.”
Matatar ta jaddada cewa tayin ba ya da iyakar da aka kayyade masa ko wani yanki, inda ta ce, “Wannan tayi ne ga dukkan masu gidajen mai da dillalan fetur a duk faɗin Najeriya.”
Dangote zai fara jigilar fetur kyauta
Haka kuma, matatar Dangote ta bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a ƙara tallafin jigilar kaya, inda ta shirya fara kai man kai-tsaye zuwa gidajen mai kyauta ba tare da kuɗin sufuri ba.
“Nan ba da jimawa ba za mu fara aikin kai man kai-tsaye zuwa gidajen mai a kyauta," in ji sanarwar.
Baya ga rage farashi, matatar ta kuma bayyana wasu ƙarin damarmaki da rangwame ga ‘yan kasuwa, domin tallafa musu wajen samun man da kuma rage musu nauye-nauye.
Daga cikin damarmakin da matatar ta shirya wa yan kasuwa akwai bashin kwanaki 10 tare da garanti daga banki da karancin adadin saye na lita 500,000 ga masu ciniki da yawa.

Source: Twitter
Matatar ta buƙaci duk masu sha’awar shiga shirin su tuntuɓe ta ta hanyoyin sadarwa na hukumance, inda ta bayar da lambobin waya da adireshin imel domin rajista da neman karin bayani.
IPMAN ta kulla yarjejeniya da matatar Dangote
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar dillalan man fetur ta IPMAN ta umarci mambobinta a fadin Najeriya da su fifita sayen mai daga matatar Dangote da ke jihar Legas.
IPMAN ta ce fara cinikayyar man fetur tsakanin matatar Dangote da mambobinta kai tsaye zai taimaka matuka wajen rage farashin fetur a Najeriya.
Kungiyar ta bayyana cewa ta riga ta yi yarjejeniya da matatar Dangote domin fara sayar da mai ga ’yan IPMAN kai tsaye, tare da jigilar kaya kyauta zuwa gidajen mai
Asali: Legit.ng


